Yadda matan Kannywood suke ƙarkon kifi a kan maza
Duk abin da mace take yana da kyau ta san cewa namiji zai fi ta daɗewa yana yi.
A ranar Talatar da gabata ce tsohuwar jarumar Kannywood, Mansurah Isah ta rubuta a shafinta na Facebook cewa, “A wannan yanayi, wataƙila in fito a sabon fim.
“Zan so a samu labari mai kyau, tsari mai kyau da aka kasafta miliyoyin kuɗi.
- Kashi 28.5 na Kanawa na fama da hawan jini — Kwamishinan Lafiya
- An ƙaddamar da gidan rediyon EFCC mai yaƙi da labaran ƙarya
“A shirye nake in fito a fim ɗin, amma wannan kira ne ga forodusoshi da suka shirya.”
Aminiya ba ta tabbatar ko da gaske take yi ba ko kawai raha ta yi domin jin amsoshin mutane, wanda kuwa ta samu sosai.
Aƙalla mutum 178 ne suka yi martani a shafinta na Facebook, inda aka yaɗa rubutun zuwa wasu wurare, bayan wanda ta yi a Instagram.
Wata mai suna Naja’atu Mahmud Ahmad ta mayar da martani cewa, “Don Allah ’yar uwa kada ki dawo cikin harkar fim, ki riƙe yaranki sai ya fi miki mutunci da daraja.
“Ai ke yanzu kin fi ƙarfin yin fim, girmanki ya wuce, don Allah ’yar uwa Mansura.”
Ita ma wata mai suna Fatima Sa’id ta bayyana a Facebook cewa, “Ko kin dawo ba za ki yi kasuwa ba, domin ita rayuwa komai lokaci ne, yanzu ba lokacinki ba ne.
“Yanzu ma shi kansa fim ɗin kasuwar yake yi? Ki tsaya wa harkokin kasuwancinki, ku daidaita da uban ’ya’yanki ko ki samu wani, ki yi aurenki, shi ne kawai mutuncinki, amma wallahi kina komawa fim yanzu baƙin jini za ki yi wajen masoyanki ciki kuwa har da ni.
“To idan ma a matsayin uwa za ki riƙa fitowa, domin ai kin wuce ’yan mata tsofai-tsofai da ke. Ki yi tunani dai gaskiya.”
Shi kuma wani mai suna M Inuwa MH cewa ya yi, “Muna kewarki kam, ya kamata ki dawo.
“Na tuno da Bil’adama da Jarumai da Guɗa da Haula da Babbar Riga da Daham da Jamila Ta Iya Ɗaura Zane.”
Idan ba a manta ba, a shekarar 2006 ce aka ɗaura auren Mansurah Isah da Sani Danja, sannan Allah Ya azurta su da ’ya’ya huɗu, mace ɗaya da maza uku kafin auren ya mutu.
Mansurah tana da Gidauniyar Today’s Life Foundation, inda a sanadiyar harkokin taimakon mabuƙata da take yi, ta samu kusanci da manyan mutane, ciki har da matar tsohon Gwamnan Jihar Kebbi, Dokta Zainab Shinkafi Bagudu.
Bayan mutuwar auren ta shirya wasu finafinai irin su Fanan, wanda a ciki har da Sani Danja da Yakubu Muhammed da ’yarsu.
Wannan lamarin ya dawo da batun da aka daɗe ana yi a tsakanin masu bibiyar harkokin Masana’antar Kannywood ta yadda matan jarumai suke ƙarkon kifi, idan aka kwatanta da maza.
Mansurah Isah ta yi zamani da Zainab Idris da Zainab Raga da su Maryam Jankunne da Maryam Hiyana da Safiya Musa da Hafsat Shehu da sauransu.
Sun zo sun samu mata irin su Fati Mohammed da Farida Jalal da Maijidda Abdulƙadir da sauransu.
Ko a zamanin, su Ali Nuhu da Sani Danja ne suke jan ragamar masana’antar, kafin su marigayi Ahmad S. Nuhu da Adam A. Zango su fara tashe.
A wata tattaunawa da ta yi da gidan rediyon Freedom a Kano, Mansurah ta ce, tun kafin ta fara fim ta fara ganin Sani Danja kuma yake burge ta sosai.
Wannan na nuna ta same shi yana burge ta, ta shigo, ta yi tashe sosai, ta yi aure, auren ya mutu, har take tunanin ko za ta dawo fim, amma su Sani da Ali suna ci gaba da taka rawa a masana’antar.
Masu bibiyar Masna’antar Kannywood da dama suna ganin har yanzu ba a yi jarumar da ta yi zarra kamar Fati Mohammed ba.
Amma ita ma, bayan ta yi shahara, ta yi aure, ta dawo ta ɗan taɓa wasu finafinan, ta sake dainawa ta koma gefe, amma wanda shi ne ubangidanta, Ali Nuhu yana ci gaba da taka rawa a masana’antar.
Shin haka abin yake a Nollywood?
Aminiya ta gano a Masana’antar Nollywood ta Kudu, akwai jarumai mata irin su Genevieve Nnaji, wadda yanzu shekararta 45, kuma har yanzu tana ci gaba da taka rawa a masan’antar, kuma tun 1987 take fim har zuwa yanzu.
Yanzu fim ɗin da ya fi tara kuɗi a Nijeriya shi ne fim ɗin Funke Akindele mai suna ‘A tribe called Judah’, wanda ya samar da sama da Naira biliyan 1, inda shi ne na farko da ya samu wannan nasara a ƙasar baki ɗaya, kuma yanzu shekararta 46, kuma tun a 1998 take fim.
Akwai darasi a rayuwar mata — Ɗanjuma Rasheed
Wani matashi mai bibiyar harkokin Masana’antar Kannywood, Ɗanjuma Rasheed ya bayyana lamarin da cewa rayuwar mace baki ɗayanta akwai darasi ba ma a masana’antar kaɗai ba.
Ya ce, komai na da lokaci, “Don haka duk abin da mace take yana da kyau ta san cewa namiji zai fi ta daɗewa yana yi.
“A ɓangaren fim kuma, kada ka manta har yanzu fim ɗin bai samu karɓuwa ba sosai a wajen Hausawa da Fulani.
“Ke nan dama ko ka ga mace tana fim, idan ma an amince mata a gida, to za ka ga yawancinsu ana matsa musu lamba a gida a kan su yi aure.
“Wasu suna fim ɗin, amma ko da iyayensu sun amince, za ka ga maƙwabta da wasu daga cikin dangi ba sa so.
“Don haka dole wannan matsalar ta sa duk tashen yarinya ta yi aure. Sannan yanayin ci-gabanmu daban da sauran masana’antun.
“Su a can, kasuwancinsu kullum ƙara haɓaka yake yi, wanda hakan ya sa idan ka iya, to akwai rawar da za ka iya takawa, musamman wandaya daɗe yana yi, dole za a ci gaba da sa shi.
“Amma a nan ai kasuwancin sai a hankali, dole jarumai mata su riƙa komawa gefe, suna bai wa sababbi waje, tunda yawanci ba su da kuɗin da za su ɗauki nauyin shirya finafinai, idan ma suna da kuɗin ai riba suke so, kuma an fi tunanin idan aka sa matasan za a fi samun riba,” in ji shi.