Yadda matar aure ta kashe dan kishiyarta da tafasasshen ruwa

An kama wata matar aure bisa zargin ta da kashe dan kishiyarta ta hanyar zuwa masa  tafasasshen ruwa a kaciyarsa a garin Dawakin Tofa da ke Jihar Kano.

’Yan sanda a Jihar Kano na zargin matar ta je ta dauki yaron ne a wurin kakarsa, ida ake kula da shi bayan an yi masa kaciya, kasancewar mahaifiyarsa da mahaifin sun rabu.

Bayanai sun nuna cewa duk da cewa kakar ta ki amincewa, amma sai da matar ta nace ta dauki yaron da cewa za ta kula da shi, bayan nan ne kuma sanya masa tafasasshen ruwa a gaban nasa, maimakon ruwan dumi.

Duk da raunin da tafasasshen ruwan ya yi  masa kuma, sai aka kai shi wurin mai maganin gargajiya maimakon asibiti, inda bayan kwana uku rai ya yi halinsa.

Kakakin rundunar ’yan sandan jihar, DSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya bayyana cewa matar tana tsare ana mata tambayoyi kafin a gurfanar da ita a gaban kuliya.