Yadda matar aure ta samu digiri mai daraja ta daya a fannin Lissafi daga Jami’ar ABU
Yadda na hada aure da karatun lissafi, kuma na kammala da digiri mai daraja ta daya
Wata matar aure Bahaushiya ta kafa tarihin zama mace ta farko a cikin shekara 60 da ta samu shaidar digiri mai daraja ta daya (First Class) a fannin ilimin Lissafi a Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya.
A hirarta da Aminiya, matar mai suna Zainab Bello Kofa ta bayyana sirrin wannan nasara da ta samu da kuma yadda ta hada rayuwar aure da karatun jami’a, kuma hakan bai hana ta kammala karatun da shaidar digiri mai daraja ta daya a fannin Lissafi ba.