Azumin bana: Halin matasa masu ‘yin caji’ a lokacin Sahur

Mata da maza sun bayyana yadda suke yin sahur, bude baki da ma azumin da taimakon kayan maye

Azumin bana: Halin matasa masu ‘yin caji’ a lokacin Sahur

(Hoto: redoakrecovery.com).

Matasa sun kirkiro da sabon salon shaye-shaye a yayin da al’ummar Musulmi suke yin azumin watan Ramadan a bana.

Wasu matasa mata da maza sun fede biri har wutsiya game da tsirfarsu ta yin sahur da bude-baki da kayan maye da kuma yadda suke kasancewa idan suka dauki azumi a bana.

‘Sai na sha kodin nake samun natsuwar yin azumi.’

Aminiya ta zanta da wata matashiya, wadda ta bukaci a sakaya sunanta kan yadda take ji a lokacin azumi, ganin cewa ya kamata ta daina shaye-shaye.

Budar bakin matashiyar ke da wuya, sai ta amsa da cewa ita dai tana ci gaba da shan kodin da hayaki (wato tabar wiwi).

Da wakilinmu ya sake tambayar ta, ko yaya take kasancewa a lokacin azumin, idan ta sha kodin, sai ta ce, “ba zan ji wuyar azumin ba gaskiya; amma sai dai matsalar ita ce zan yi ta neman hayaki (wato tabar wiwi) ce gaskiya.

“Ni duk azumin da na dauka ma, sai na sha kodin din nake samun natsuwa gaskiya. Da asuba, a lokacin sahur nake sha.”

Da aka tambaye ta ko za ta iya jurewa har ta kai azumin ba tare da ta sha komai ba, musamman ganin yadda ake cewa idan mutum ya saba ba ya iya dadewa bai sha ba, ga shi kuma ta ce dole za ta nemi hayaki, sai ta ce, “e mana, zan iya jurewa. Idan kuma na ji yanayi ya canja sosai, sai kawai in yi barci.”

‘Dalilin da ake sha lokacin sahur’

Shi kuma wani mai suna Tanko, cewa ya yi, “Ka ga ni ina shaye-shaye gaskiya, amma tun da aka fara azumi ban sha komai ba.

“Amma abin da ya sa wasu suke sha lokacin azumi, da shi suke yin sahur domin da rana su samu su yi barci kawai har faduwar rana. Ka ga kamar ‘bonus’ (garabasa) ke nan a wajensu.”

Da wakilinmu ya tambaye shi irin kayan mayen da suke sha domin su yi barci, sai ya ce, “idan ka sha maganin mura irinsu Kodin da Fakalin da Tutolin da Emzolin da sauransu.

“Idan mutum ya sha su suka yi yawa, kamar mutum ya sha kwalba daya, to dole zai yi ta barci da rana har zuwa yamma.

“Akwai kuma kwaya da ake sha kamar roci. Da mutum ya sha wadannan dole ya yi barci. Ka ga da mutum ya sha, dole zai ta yin barci har zuwa yamma. Ni ma ina sha amma gaskiya tun fara azumi, ni ban sha ba.”

Bude-bakin ’yan shaye-shaye

A game da yadda suke bude-baki, matashin cewa ya yi, “ai ka san kowa da irin nasa, wani da an kira Sallahi, taba yake fara sha, wani kuma da an kira wiwi yake fara sha. Ya riga ya murza ta tana ajiye kawai yana jira a kira Sallah.

“Wani kuma kayan kemis din ne, ya danganta ne da wanda mutum ya saba da shi.”

Shi ma wani da ya ki ya ambaci sunansa, cewa ya yi suna yin shaye-shayen ne domin ya taimaka musu wajen jan lokaci.

“Wasu da shi suke bude-baki, wasu kuma har sahur suke yi. Amma fa yawanci sai idan sun ci abinci tukuna sai a daura a kai, saboda yana taimakawa wajen rage radadin azumi domin barci yake sawa.

“Kafin a farka sai ka ga lokaci ya ja sosai. Ke nan ba za ka ji azumi ba,” inji shi.

Ya kuma kara da cewa, “Wasu kuma da an bude baki da shi za su fara, wasu kuma da asuba suke sha saboda ta riga ya bi musu jiki.

“Gaskiya yana taimakawa saboda abu ne da idan an sha barci ake yi, wanda za ka ga lokaci ya ja kafin ka tashi daga barcin,” inji shi.

“Nima mun taba a lokacin azumi a da, amma a yanzu na bari amma ina da masu sha da muke tare,” inji shi.

Dalilin da suke ji kamar ba su jin yunwa bayan shayeshaye – Dokta Auwal Salihu

 

“ba zan ji wuyar azumin ba gaskiya, amma sai dai matsalar ita ce zan ta neman hayaki (wato tabar wiwi) ce gaskiya. “Ni duk Azumin da na dauka ma, sai na sha kodin din nake samun natsuwa gaskiya. Da asuba a lokacin sahur nake sha.”

Aminiya ta tattaauna da Dokta Auwal Salihu, wanda kwararre ne a fannin kwakwalwa kuma malami ne a Asibitin Koyarwa na Malam Aminu Kano ta Jami’ar Bayero da ke Kano, inda ya ce, “Shayeshaye na da illoli duk da cewa illolin sun danganta ga irin abin da mutum yake sha.

“Idan muka duba, idan mutum ya fara shan kwayoyi akwai abin da ake cewa ‘addiction’ wato yadda kwayoyin za su sarke shi ya zama cewa dole kullum sai ya sha sannan zai ji daidai.

“Tun yana shan kwaya daya tana yi masa aiki, sai ya zama gobe sai ya kara zuwa biyu, a sannu a hankali zai rika karawa har ya kai wani abu.

“Wannan canjin zai iya rikita aikin kwakwalwarsa wani lokaci ya zamana yana yin wasu abubuwa da ba daidai ba.

“Baya ga haka kuma idan ya sha jiki ma yakan samu canji: Misali idan muka dauki giya tana lalata komai a jikin mutum.”

A cewarsa duk da cewar idan mutum ya sha Kodin ko wani abu da zai sa hankalinsa ya dauke daga tunanin abinci tsawon rana, wannan kai tsaye abu ne da zai shafi lafiyar kwakwalwa.

Dokta Salihu ya bayyana cewa babu wasu sinadarai wadanda za a iya cewa kai tsaye suna karfafa wa mutum ciki don saukaka azumi gare shi, sai dai akwai abubuwan da za su hana mutum ya san cewa yana jin yunwar.

“Kai tsaye ba za mu ce akwai wani sinadari ko wasu abubuwa da ke karfafa wa mutum ciki ya samun saukin azumi ko kuma ma a ce ba ya jin yunwa gaba daya ba, amma akwai abubuwa da ke hana mutum ya san cewa yana jin yunwar ma gaba daya.

“Idan kika dauki mutum da ke shan taba ko kofi, za ki ga cewar ya dauke masa hankali a kan batun jin yunwa.

“Zai zama cewar ba ya saurin jin yunwa kamar yadda sauran mutane da ba su shan wadannan abubuwa suke ji.

“Hakan shi ke sanya za ki ga duk masu wadancan shaye-shayen ba su yin kiba domin jikinsu ba ya samun abincin da ya kamata ya samu.

“Wannan shaye-sahyen ya dauke musu jin yunwa, akwai yunwar a jikinsu amma ba su jin ta, don haka ba su damu su ci abinci ba.”

Dokta Auwal Salihu ya yi kira ga matasa da su guje wa harkar shaye-shayen kwayoyi don samun dorewar lafiyarsu.

“Kirana ga matasa har kullum shi ne, su san cewa wadanann abubuwa da suke sha suna da illoli ga lafiyar kwakwalwarsu da ta jikinsu.

“Baya ga haka, yakan kasance mutum ya sa al’ummar da yake ciki ba sa kallon sa da kima, domin ganin sa ake kullum a [matsayin] shashasha wanda ba zai iya yin wani tunani ko wani abu mai kyau da zai amfani al’umma ba.

Abin da suke yi makaruhi ne – Malamai

Har ila yau Aminiya ta tattauna da malamai don sanin hukuncin azumin irin wadanan mutane da ke shan miyagun kwayoyi su yini suna barci don saukaka wa kwakwalwarsu azumi.

Shaikh Ibrahim Khalil ya bayyana cewa hakan makaruhi ne. “Kai tsaye ba za mu ce azuminsu bai yi ba, sai dai mu ce abin da suka aikata makaruhi ne domin an so mutum ya yi azumi a cikin hankalisa.

Amma sai ga shi sun yini suna barci don kada su ji yunwa ko kuma don gudun kada son shan kwayar ya taso musu ya kai su ga karya azumi.”

Shi ma Dokta Yahaya Tanko, fitaccen malamin Musulunci a Jihar Kano ya bayyana cewa: “Duk da cewa kai tsaye ba za mu iya cewa azumin bai karbu ba, amma idan mun duba, shi kallafa aikin ibada da Allah Ya yi a kan bawa, ana so ya yi shi ne a cikin hankalinsa.

“Duk mai barci ba ya cikin hankalinsa. Ba zai yiwu a ce mutum ya yi aikin ibada a yanayin barci ba. Zai iya zama babu ladan ibada ma gaba daya.

Matashi ya kashe mahaifiyarsa don yin tsafi a Kuros Riba

DSS ta ceto mutum 4 da aka sace a Sakkwato

2025: Wutar lantarkin Najeriya ta ɗauke gaba ɗaya

Kano: Kwamishinan da Abba ya tsige ya koma Jam’iyyarAPC