Yadda matasa suka yai tururuwa don samun amarya mai tukuici
daruruwan matasa a birnin Kano sun yi tururuwa zuwa gidan Rediyon Freedom don amsa kiran wata budurwa da ta yi alkawarin bayar da mota da gida ga duka saurayin da ta zaba ya aure ta. A ranar Talata ne budurwar mai shekara 22 mai suna Zainab Abdulmalik ta bayar da sanarwar neman miji a cikin […]
????????????????????????????????????

daruruwan matasa a birnin Kano sun yi tururuwa zuwa gidan Rediyon Freedom don amsa kiran wata budurwa da ta yi alkawarin bayar da mota da gida ga duka saurayin da ta zaba ya aure ta.
A ranar Talata ne budurwar mai shekara 22 mai suna Zainab Abdulmalik ta bayar da sanarwar neman miji a cikin shirin “IN DA RANKA” na gidan rediyon, inda ta ce duk wanda ya dace da aurenta za ta saya amsa mota da gida kuma ta ba shi kudi. Wannan tayi ya sa daruruwan matasan yin dafifi kowa na neman ya aure ta. Sai dai budurwa ta ce duk wanda za ta aura ya kasance dan shekara 17 zuwa 25 ne.
Matasan wadanda suka je daga ungwannin daban-daban da ke Kano da kewayenta, sun caba ado domin burge ta, inda da dama suka zauna zaman jiran budurwar, wasu da suka gaji suka tafi suka bar hotuna da lambar wayarsu a jiki don bayarwa ga budurwar
Lokacin da budurwar ta je gidan rediyon a shekaranjiya Laraba, matasan sun yi mata ca, sai da ’yan sanda suka shiga tsakani suka tafi da ita, hakan ya sa matasan bi ’yan sandan zuwa ofishinsu na Sharada da kuma Hukumar Hisba. Duk da cewa mafi yawan matasan da suka zo don neman aurenta sun yi ne saboda dukiyar da ta yi alkawari, wasu sun ce za su aure ta ne saboda Allah.
Ahmad Ibrahim Gama ya ce, yana ganin babu laifi don ya aure ta don dukiyar da za ta bayar. “Ina ganin babu komai don na aure ta don za ta saya min mota. Matukar za ta zabe ni a matsayin miji, to, babu abin da zai hana ni auren ta.” inji shi.
Shi kuwa Yahya Sani ya ce, ba kudinta ne ya dame shi ba, aure ne kawai a gabnsa. “Wallahi dama na dade ina neman matar aure, jin haka ya sa na ce bari in zo in gani, idan Allah Ya sa an dace, shi ke nan. Amma wallahi ko ma ba ta saya min mota ba, zan zauna da ita lafiya,” inji shi.
A hirarta da Aminiya Zainab wacce ’yar asalin Jihar Osun ne, ta ce ta dauki matakin ne saboda yaudararta da tsohon saurayinta da suka dade ya yi, bayan ta kashe masa kimanin Naira miliyan biyar. “A baya na yi soyayya da wani saurayi da muka shafe shekaru sai a rana a tsaka ya wulakanta duk da kudin da na kashe masa. Hakan ya sa na fito neman mijin aure don in huce wancan haushi,” inji ta.
Budurwar ta ce tana kasuwanci ne a Kasuwar Singa da ke Kano, kuma ta ce ita budurwa ce wacce ba ta taba yin aure ba, don haka ita ma saurayi take son aure. Ta ce duk da cewa ba ta samu damar zabar miji a cikin dimbin matasan da suka taru ba, ta tabbata idan kura ta lafa za ta samu miji a cikinsu.
Da Aminiya ta tuntubi Ustaz Aminu Ibrahim Daurawa kan lamarin a addini, ya ce hakan da ta yi ba laifi ba ne, domin Hadisi ya nuna cewa za a iya auren mace don dukiyarta. Sai dai ya ce akwai bukatar idan za a yi auren a tsakarkake niyya don samun alherin da ke ciki. “A mahanga ta addini wannan abu da ta yi ba laifi ba ne, kuma koda ta samu miji ta wannan hanya auren ya yi. Sai dai muna kira a rika tsarkake niyya a duk wani abu da za a yi, musamman ma harkar aure. A al’ada ce ba a saba jin haka ba, ake ganin ta zo da wani sabon salo,” inji shi.