…Yadda matasa suka yi murnar nasarar Buhari a Nasarawa
Matasa sun kwana suna murna saboda cin zaben da Shugaba Muhammadu Buhari ya yi a Jihar Nasarawa. Matasan sun nuna cewa suna murna ne saboda abubuwa guda biyu: Na farko shi ne cin zabe a karon farko da Buhari ya yi a jihar. Na biyu kuma shi ne cin zaben kasa baki daya da ya […]
Matasa sun kwana suna murna saboda cin zaben da Shugaba Muhammadu Buhari ya yi a Jihar Nasarawa.
Matasan sun nuna cewa suna murna ne saboda abubuwa guda biyu: Na farko shi ne cin zabe a karon farko da Buhari ya yi a jihar. Na biyu kuma shi ne cin zaben kasa baki daya da ya yi.
Abdullahi M. Sani wanda yake Unguwan Rice Mill a Lafiya, yana dauke ne da tabarma da filo da jaka, inda ya ce yana neman ’yan hamayya ne ya ba su, don su gudu.
Shi kuma Musa Abdullahi wanda yake Unguwar Sarkin Fada da ke Lafiya ya shafa wa fuskarsa bakin gawayi ne, inda ya ce shi Kanuri ne, don haka yana neman mota ce domin zuwa Adamawa don ya jajanta wa ’yan adawa.
A bikin murnar, ba a bar mata a baya ba, domin Malama Jummai wacce take zaune a Unguwar Galadima a cikin garin Lafiya, ta zo wajen ne dauke da baban daro, inda ta ce, “Ina yawo ne ina neman ’yan adawa don in ba su allayyaho don su yi abinci.”
Sannan wani matashi kuma ya zo ne rike da kwali, inda ya rubuta cewa, “Almajirai suna da ranarsu, sai Baba Buhari!”
Aminiya ta ga motocin wasu jam’iyyu suna gittawa ta kan hanyar Makurdi da Shendam amma ba wanda ya musguna musu.