Yadda kasa ta binne matasan Najeriya 13 a rijiyar hakar zinare a Nijar

Gwamnan Maradi ya bukaci a dauki matakan inganta harkar hakar zinare a yankin.

Yadda kasa ta binne matasan Najeriya 13 a rijiyar hakar zinare a Nijar

’Yan Najeriya 13 da ’yan Jamhuriyar Nijar biyar ne hukumomi suka tabbatar da rasuwarsu bayan wata rijiyar hakar zinare ta rufta a kansu a Jamhuriyar Nijar.

Wani dan Najeriya mai suna Abubakar daga Jihar Zamfara, wanda dan uwansa ya rasu a iftila’in ya ce abin ya faru ne mako biyu da zuwansu neman arziki a yankin, amma zuwa lokacin, iyayensu ba su san da rasuwar dan uwan nasa ba.

“Ina da ’yan uwa cikin wadanda Allah Ya yi wa cikawa, yanzu dai na ga biyu kuma akwai saura a kasa; Gaskiya duk wanda ya ce ga adadin wadanda ke karkashin kasar nan ya fada ne dai kawai, jiya dai an fito da mutum 17,” kamar yadda wani ya shaida wa Babban Editan gidan Rediyon Amfani da ke Jamhuriyar Nijar, Chaibu Mani, wanda ya ziyarci wurin domin gane wa kansa.

Wani mai hakar zinare a wajen ya ce, “Ana sa ran akwai mutane ba daya ba, ba biyu ba a karkashin kasa, saboda duk wadanda ke rijiyar suna kasa abin ya faru ba a ciro su ba; Wadanda ke amsar kaya na waje ne aka fiddo su.”

Magajin Garin yankin, Malam Adami Girau, ya ce, “Abu na al’ajabi ya faru inda wadannan rijiyoyi suka fada gaba daya kuma suka rufta da mutane, rayukan mutane da yawa suka rasu; Akalla mutum 18 ne suka rasa rayukansu.”

– Yadda abin ya faru

“A lokacin da ma’aikatan ke gudanar da aiki, zuwa wajen Azahar sai wannan kasa ta rufta da mutane da dama; A gabana an zakulo gawa kusan 11,” injin Chaibu Mani wanda ganau ne, a zantawarsa da shirin Najeriya A Yau, wanda Aminiya ke gabatarwa ta intanet.

Lamarin ya faru ne a ranar Talata a kauyen Kwandago, inda aka gano arzikin zinare kimanin wata takwas da suka gabata a Karamar Hukumar Dan Isa da ke Jihar Maradi.

Chaibu Mani, ya ce tun da aka gano ma’adanan zinare a yankin Kwandago matasa masu tonon zinare daga Jamhuriyar Nijar, Najeriya, Chadi, Mali, Jamhuriyar Benin, Sudan da sauran kasashe makwabta ke ta tururuwar shigowa yankin.

– Rashin kyakkyawan tsari

A yayin da ake ci gaba da aikin ceto, masu hakar zinare a wajen sun ce akwai rashin kyakkyawan tsari, ta yadda wasu daga cikinsu ke yin yadda suka ga dama, wanda hakan na daga cikin abin da ya haddasa ruftawar kasar.

Wani daga cikinsu ya ce, “A ginan rijiyoyin ba a yi su bisa tsari ba.”

“Akwai rijiyoyin da ya kamata a tsayar da su, akwai wadanda ya kamata a ci gaba da aiki saboda irin wannan matsalar ta bar faruwa.

“Rijiyoyin ba a yi su a tsari ba, wurin da ya cancanta a gina rijiya 1o zuwa 15 shi ne aka fitar da rijiya 150 zuwa 200, wanda bai kamata ba” inji wani daga cikinsu.

– Su ke bata tsarin da aka yi —Magajin Gari

Magajin Garin yankin ya ce, “Yawan mutanen da suka shigo yankin cikin dan lokaci kalilan abin zai ba ka mamaki. Ai an yi tsarin, wasunsu ne suka ki bin tsarin.

“Akwai wadanda suke bin tsarin, amma sai wasu su kewayo cikin dare suna gine-gine suna batawa, shi ya kawo wannan matsalar.

“Kafin faruwar wannan abu ma akwai ’yan kungiya da suka zo daga Niamey, sun yi ziyara ko’ina, su da kansu suka ce min gaskiya abin da suka gani ba zai ba da dama a ci gaba da aiki a wannan wuri ba, matsawar ba a auki matakai ba.

“Muka ce to tunda ga ku, in Allah Ya yarda za mu yi amfani da shawarwarinku mu kawo gyara a wannan abu da ake yi.

“Har suka ce za su zo su duba, in akwai rijiyoyin da ya kamata a rufe, saboda an yi su kusa-kusa.

“Mun kare wannan hirar ke nan, na tafi na bar su, wurin karfe shida na yamma sai aka kira ni aka ce min ga wannan abu ya faru.”

– Mafita

A lokacin da ya ziyarci wurin da abin ya faru, Gwamnan Jihar Maradi, Chaibu Aboubacar, ya ce, “Muna musu ta’aziyya da wannan rashi da ya samu; Mun san samari ne ke zuwa nan suna aikin da suke don samun dan abin da suke ciyar da gidajensu.

“Wannan abu da ya faru mun yi kuka; Amma amma abun ya kamata shi ne a duba shi da kyau a tsara yadda za a gudanar da shi, domin mutane ba dabbobi ba ne, ko dabba bai kamata tana mutuwa haka kawai ba.

“Ya kamata a yi nazari a ga yadda za a tafiyar da shi ta yadda mutane za su amfana amma ba tare da salwantar da rayuwarsu ba.