Yadda matashin da ya yi wa mata 40 fyade a Kano ya shiga hannu

Wani matashi wanda ake zargi da yi wa mata fiye da 40 fyade ciki har da tsohuwa mai shekaru 80 ya shiga hannu a jihar Kano. Yanzu haka Muhammad Zulfarau Alfa wanda aka fi sani da ‘Mai Siket’ —mazaunin garin Kwanar Dangora, na hannun ‘yan sanda. Kakakin Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Kano DSP Abdullahi Haruna […]

Yadda matashin da ya yi wa mata 40 fyade a Kano ya shiga hannu

Wani matashi wanda ake zargi da yi wa mata fiye da 40 fyade ciki har da tsohuwa mai shekaru 80 ya shiga hannu a jihar Kano.

Yanzu haka Muhammad Zulfarau Alfa wanda aka fi sani da ‘Mai Siket’ —mazaunin garin Kwanar Dangora, na hannun ‘yan sanda.

Kakakin Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Kano DSP Abdullahi Haruna Kiyawa ne ya tabbatar da kame Mai Siket da misalin karfe 2.00 na dare, yana kokarin aikata laifin.

“Gaskiya ne, mun kama matashin za kuma mu gabatar da shi ga manema labarai nan bada jimawa ba.

“Jama’ar garin Kwanar Dangora na cike da farin cikin kame wannan matashin za kuma mu tabbatar an yi adalci”, inji shi.

Abdullahi Haruna ya ce wanda ake zargin ya yi yunkurin tserewa amma an kama shi ne da taimakon mutanen yankin bayan wata mata ta kama shi a dakin ‘ya’yanta a da tsakar dare.

Kwamishinan ‘yan sandan Kano, CP Habu Ahmad ya bayar da umurnin binciken wanda ake zargin kafin a hukumta shi,” a cewarsa.

Ya kara da cewa Mai siket ya amsa laifinsa sannan ya ce a shekarar bara kadai ya yi wa mata fiye da 40 fyade.

Matashin ya ce wadanda ya keta mutuncin nasu sun hada da kananan yara.

Mai sike ya yi kaurin suna wurin yi wa mata fyade ta yadda wasu ke zaton ko aljani ne.