Yadda matsafa suka kwakule wa yaro idanu
Wadansu da ake zaton matsafa ne sun kwakule idanun wani yaro a Unguwar bula bayan asibitin da ke Madarkaci Jushi Banzazzau da ke karamar hukumar Zariya a jihar Kaduna. Wannan al’amari dai ya jefa al’ummar Zariya da kewaye cikin rudani da kuma furgici a lokacin da suka samu labarin kwakule idanun wani yaro mai suna […]

Wadansu da ake zaton matsafa ne sun kwakule idanun wani yaro a Unguwar bula bayan asibitin da ke Madarkaci Jushi Banzazzau da ke karamar hukumar Zariya a jihar Kaduna.
Wannan al’amari dai ya jefa al’ummar Zariya da kewaye cikin rudani da kuma furgici a lokacin da suka samu labarin kwakule idanun wani yaro mai suna Abubakar Usman dan kimanin shekara hudu da wadansu marasa imani suka yi.
Kakar yaron mai suna Hadiza, wanda kodayaushe suna tare da yaron, ta bayyana wa Aminiya cawa, ‘’A ranar lahadi da misalin karfe hudu na yamma jikana mai suna Abubakar za shi makarantar Islamiya na kawo Naira biyar na ba shi domin ya sayi madarar kandi ya ji dadin karatu a makaranta, domin mahaifiyarsu ta tafi gidansu yin sha’ani. Fitarsa ke da wuya tare da wansa mai suna Umar Usman, sai wani mara imani ya raba tafiyarsu, ya kuma kama hannunsa ya kai shi wani kangon gida inda ya aikata masa wannan mummunar lamari. Na fito kofar gida ke nan sai ga wani yaro dan unguwa a guje ya ce ga jikanki can Abubakar an kwakule masa idanu, nan da nan hankali na ya tashi, muka bazama don ganin halin da yake ciki.’’
Ta ci gaba da bayyana wa wakilinmu cikin kuka cewa, ’’Malam abun ba kyan gani, mahaifiyarsa mai suna Hauwa’u ita ma yanzu haka tana cikin wani hali, ta tattara ina-inata ta koma gidan mahaifinta saboda firgici, kuma har zuwa yanzu da nake maka wannan bayanin ta ki yarda ta ga dan nata. Ka ji halin da muke ciki.’’
Mahaifin yaron mai suna Usman Isa, wanda aka fi sani da Auta, ya kara wa Aminiya bayani cewa, ‘’A ranar lahadi ina bakin aikina da misalin karfe hudu sai aka kirawo ni aka ce in dawo gida ga abin da ya faru da Abubakar, ina zuwa gida na ga halin da yake ciki, sai na yi addu’a na ce Allah Ya ba mu mafita a cikin wanna lamari da ya jarrabe mu da shi, nan da nan muka sanar da ’yan sanda, kafin mu dauke shi zuwa asibitin (Saint Lukes) da ke Wusasa Zariya, a inda nan da nan jami’an asibitin suka fara kula da yaron na gaggawa, bayan an kammala duba shi, daya daga cikinsu ya yi mana bayanin irin matsanancin halin da yaron yake ciki. Kuma wannan wani mukaddari ne, domin yaran ba sa fita ko’ina, kullun suna tare da mahaifiyata, in dai ba makaranta za su je ba, don haka ina rokon Allah Ya ba mu halin juriya na kula da kuma daukar dawainiyarsu.
Aminiya ta garzaya Unguwar da lamarin ya ,faru inda ta tarar da al’ummar unguwar sun rusa kangon gidan da aka kai yaron aka kwakule masa idanun, suna kuma cewa za su dauki matakin da duk ya dace a kan irin wadannan gidaje da suke zargi marasa aikin yi na taruwa.
Babban likitan da ke kula da asibitin Wusasa (chief medical director) mai suna Dokta Gilbert, ya ce a ranar lahadi ne da misalin karfe biyar na yamma aka kawo wannan yaron Abubakar wanda aka kwakule wa idanu, a yadda muka fahimci halin da yake ciki sun kwakule idanun ne gaba daya, ainihin kwayoyin idanun gaba daya sun cire su, amma mun dauki matakin kare lafiyarsa, wajen kula da shi da kuma ba shi taimakon da ya dace, kuma muna sa ran yana samun sauki, sai dai fa kuma ya rasa idanuwansa.
Da samun labarin halin da wanna yaro yake ciki, Mai martaba sarkin Zazzau Alhaji Shehu Idris ya tura wakilansa domin a duba halin da yaron yake ciki, ya kuma ba da umurnin a dauke yaron a kai shi babban asibtin idanu da ke Kaduna domin kula da shi, da kuma ba da shawara idan zai yi wu a kai yaron duk inda ya dace domin a ceto rawuwarsa, da kuma alkawarin biyan ko nawa ne domin a samar masa lafiya.
Shugaban ‘yan sanda da ke kofar fada a cikin birnin Zariya, CSP Bashir Ahmad, a tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce sun tura jami’an tsaro domin sa ido a unguwar da abin ya faru.