Yadda matsalar man fetur ta jefa jama’a cikin mafi munin kunci
Matsalar karancin mane fetur da aka fuskanta a karshen makon jiya da wannan mako da har yanzu ake fuskantarta ta jefa jama’ar kasar nan a mafi kuncin rayuwa, inda aka samu karancin wutar lantarki da rashin ruwan sha sannan al’amura suka nemi tsayawa cik a daukacin kasar nan. Baya ga haka matsalar wadda ta hada […]
Matsalar karancin mane fetur da aka fuskanta a karshen makon jiya da wannan mako da har yanzu ake fuskantarta ta jefa jama’ar kasar nan a mafi kuncin rayuwa, inda aka samu karancin wutar lantarki da rashin ruwan sha sannan al’amura suka nemi tsayawa cik a daukacin kasar nan.
Baya ga haka matsalar wadda ta hada har da na dangogin man fetur da suka hada da man dizal da kananzir da man jirgi ta sanya bankuna sun takaita lokacin gudanar da ayyukansu, yayin da kamfanonin sadarwa na wayoyin salula da suka hada da MTN da Airtel da Etisalat suka rika cewa mai yiwuwa a rika samun cikas wajen sadarwa tare da bayyana cewa akwai yiwuwar su rufe wasu tashoshinsu saboda karancin man dizal da suke amfani da shi.
Baya ga tashin gwauron zabon farashin motocin sufuri da matsalar ta haifar a baki dayan kasar nan, a tashoshin jiragen sama ma an rika samun cinkoson fasinjojin da ke so tafiye-tafiye saboda kamfanonin jiragen sama sun dakatar da ayyukansu sakamakon rashin man jirgin sama. Wasu bankuna sun sanar da cewa za su rika rufewa kafin lokacin da a baya suke tashi saboda karancin man.
Matsalar karancin man fetur din wadda ta haifar da cikas ga samar da wutar lantarki ta sa hatta Jamhuriyyar Nijar ta dandana rashin wutar lantarkin inda aka aka shafe kwanaki ana fama da matsalarta a Yamai fadar gwamnatin kasar da wasu manyan biranen kasar.
Darakta Janar na Kamfanin Nigelec da ke samar da lantarki a Nijar, Alassne Halid ya fadi a gidan talabijin cewa shafe kwanaki babu wuta a Najeriya saboda yajin aikin masu ruwa da tsaki a harkar samar da mai, lamarin da ya shafi bangaren makamashi a kasar ne ya shafi Nijar.
Rahotanni sun ce tun a makon jiya aka shiga matsalar Lantarki a Yamai da Maradi da sauran biranen Nijar.
Daga Legas wakilinmu ya ce karancin man ya tilasta wa masu ababen hawa ajiye motocinsu inda mutane da yawa suke taka sayyada zuwa wuraren ayyuka da sana’o’insu a sassa da dama na jihar.
Ya ce karancin man ya janyo tashin kudin sufurin mota da na jiragen sama da na ruwa da na kasa.
Aminiya ta gano babu cinkoson motoci a mafiyawan titunan jihar, yayin da gidajen mai da yawa suka rufe, sannan ’yan kalilan da ke sayar da man na sayar da shi da dan karen tsada.
Ya ce ’yan bumburutu su ci kasuwarsu ba tare da wata matsala ba inda suke sayar da lita daya ta mai Naira 400 zuwa 500.
Direbobi da dama da ya tattauna da su sun ce sun ajiye motocinsu saboda karancin man da tsadarsa ta yadda koda sun sayi man ba za su samu rib aba idan suka dauki fasinjoji.
Daga Maiduguri, wakilinmu ya ce jama’ar jihar da ke fama da matsalar tsaro, matsalar rashin man a garin Maiduguri, ta sa jama’a taka sayyada saboda tsadar kudin ababen hawa, sannan rashin wutar lantarki ya sanya su kwana cikin tsabagen zafi.
Ya ce jama’a sun yi ta kokawa kan tashin farashin fetur din inda aka sayar da lita daya kan Naira 140 zuwa sama. Kuma an rika samun dogayen layuka a bankuna wadanda suka takaita lokacin aikinsu saboda karancin fetur da dizal, lamarin da ya dada jefa jama’a a cikin kunci.
Daga Damaturu wakilinmu ya ruwaito cewa al’amuran yau da kullum na tafiyar hawainiya a sassan Jihar Yobe sakamakon karanci da tsadar albarkatun man fetur da al’ummar jihar suke fuskanta sama da mako hudu.
Aminiya ta gano akasarin gidajen mai na rufe, yayin da gidajen mai kamar na Mai Rago da dan Burga da sauransu ke sayar da litar mai daya a kan Naira 130.
Matsalar karancin man ta hana ’yan kasuwa da dama zuwa wasu jihohi don sayo kayayyaki kamar yadda suka saba, sakamakon tsawwalar kudin mota, inda jama’a suka rika zargin gwamnatin da ta bar gado a yau da haddasa karancin man da gangan don takura wa gwamnatin da ta gaje ta.
Masu dakon mai dai sun yi alkawarin za a kawo karshen karancin man fetur din da dangoginsa nan da makon da za mu shiga, bayan da wakilansu suka koma dakon man sakamakon janye yajin aikin da suka yi a ranar Litinin da ta gabata.