Yadda Maukibin kadiriyya na 63 ya wakana a Kano
A ranar Asabar da ta gabata ne mabiya darikar kadiriyya suka gudanar da bikin Maukibi karo na 63 a Kano. Maukibin na kadiriyya an faro shi ne a 1975, domin tunawa da ranar haihuwar shugaban darikar Sidi Abdulkadir Jailani. Iyalan marigayi Sheikh Nasiru Kabara a karkashin Halifarsa Sheikh kaibullah Nasiru Kabara ne ke jagorantar bikin […]

A ranar Asabar da ta gabata ne mabiya darikar kadiriyya suka gudanar da bikin Maukibi karo na 63 a Kano. Maukibin na kadiriyya an faro shi ne a 1975, domin tunawa da ranar haihuwar shugaban darikar Sidi Abdulkadir Jailani.
Iyalan marigayi Sheikh Nasiru Kabara a karkashin Halifarsa Sheikh kaibullah Nasiru Kabara ne ke jagorantar bikin Maukibin domin dorawa daga inda mahaifinsu ya tsaya, wanda ya fara asassa bikin ta fita da mutum 20.
Ya rage saura kwana biyu a gudanar da bikin, mabiya darikar kadiriyya daga kasashen Pakistan da Libya da sauran na Afirka suka fara shigowa Kano, sai kuma na birane da
kauyukan kasar nan, lamarin da ya sa garin Kano ya cika ya batse a lokacin bikin.
An fara bikin na Maukibi da wasu shagulgula da suka hada da karatun Mauludi da halara a ranar Laraba. Kuma washegari Alhamis kuma aka sake halara, sai kuma a ranar Juma’a aka yi Alhalkatul Kubra, kafin aka fita Maukibi a ranar Asabar.
Mabiya darika sun taru a kofar Gidan kadiriyya sannan suka bi ta titin Unguwar Makwarari zuwa gefen Kasuwar Kurmi da Unguwar ’Yan mota da Unguwar ’Yan awaki sannan suka fito kan titin kofar Mazugal har zuwa filin Masalalcin Wali Maigiginya (Kanzul Mudalsam) da ke titin Katsina,inda suke yada zango don gudanar da addu’o’i da jawabai.
Da yamma ta yi sai jama’ar suka juyo zuwa gari inda suke dauki hanyar Unguwar Gwammaja zuwa Kwanar Dala da Jakara daga nan su ratso ta Unguwar Kwanar Goda zuwa Mandawari, a karshe aka dire a Gidan kadiriyya da ke Unguwar Kabara.
A yayin zagayen mabiya darikar kadiriyya manya da yaran makarantun Islamiyya sun rika rera wakokin yabon Annabi da kasidojin darikar.
A yayin bikin mabiya darikar kadiriyya kan yi amfani da lokacin wajen sadar da zumunci a tsakaninsu. Haka ’yan kasuwa kan baje kolin kayayykinsu filin Wali Maigiginya da sauran wuraren da ake taruwa.
A jawabin Gwamnan Jihar Kano Injiniya Rabi’u Musa Kwankwaso wanda Shugaban Ma’aikata na Jihar Alhaji Shehu Minjibir ya wakilta ya ce gwamnatin jihar a shirye take wajen ganin jama’ar jihar sun samu ilimin addinin don magance rigingimun addini da suke tasowa a tsakanin jama’a. Sanann ya yi kira ga malamai su kara ribanya kokarinsu wajen nusar da jama’a game da muhimmancin hadin kai da zaman lafiya a tsakanin Musulmi.
A jawabin Shugaban darikar kadiriyya na Afirka Shaikh karibullah Nasiru Kabara ya ja hanakalin Musulmi ne kan su zama masu kankan da kai tare da neman gafara daga wurin mahalicci a kan laifuffukan da suka aikata.