Yadda Mawaki Sani dan Indo ya yi ban kwana da duniya

A safiyar ranar Litinin da ta gabata ce Allah Ya yi wa shahararren mawakin Hausa, Alhaji Sani dan Indo rasuwa a gidansa da ke garin Gadar Tambaruwa, Jihar Kano.Aminiya ta rawaito cewa marigayin ya rasu ne jim kadan da dawowarsa daga wurin wani wasa a garin Sara da ke Jihar Jigawa.Malama A’isha Sani, ita ce […]

Yadda Mawaki Sani dan Indo ya yi ban kwana da duniya
Yadda Mawaki Sani dan Indo ya yi ban kwana da duniya

A safiyar ranar Litinin da ta gabata ce Allah Ya yi wa shahararren mawakin Hausa, Alhaji Sani dan Indo rasuwa a gidansa da ke garin Gadar Tambaruwa, Jihar Kano.
Aminiya ta rawaito cewa marigayin ya rasu ne jim kadan da dawowarsa daga wurin wani wasa a garin Sara da ke Jihar Jigawa.
Malama A’isha Sani, ita ce uwargidan marigayin. Ta bayyana cewa maganarsu ta karshe da shi, ita ce lokacin da ya umarce ta da ta bude masa madara.
“Misalin karfe 11:00 na dare sai ya ce na bude masa madarar ruwa. Bayan na bude na mika masa sai na shiga daki na kwanta. Ni ban san ma lokacin da ya shigo ya kwanta ba. Can wajen misalin karfe 5:00 sai na ji shi yana kakari. Sai na farka inda na gan shi a cikin wani yanayi. Hakan ya sa na yi sauri na fita kofar gida, inda na kira mutane don su zo su taimaka mana. Zuwansu ke da wuya suka tabbatar da cewa ya rasu.” Inji ta.
A cewarta, duk da cewa marigayin mijin nata yana fama da cutar hawan jini, amma bai yi mata korafin wani abu yana yi masa ciwo ba kafin ya kwanta barci.
Zubairu Sani, dan kimani shekaru 25, shi ne babban da namiji a cikin ’ya’yan marigayin. Ya bayyana cewa ya kadu sosai da mutuwar mahaifin nasa, kasancewar lafiya lau suka rabu da mahaifin nasa; sai dai wayar gari ya yi da labarin mutuwarsa.
Da Aminiya ta tambaye shi ko zai ci gaba da sana’ar da mahaifinsa yake yi, matashi Zubairu wanda dalibi ne a Kwalejin Fasaha da ke Kano ya bayyana cewa ba zai iya cewa koami a kan hakan ba; kasancewar komai na rayuwar mutum yana hannun Allah.
“Duk da cewar ba na shiga cikin sahun masu yi masa kida ko amshi amma yawanci duk tafiyar da zai yi tare da ni ake zuwa. Ba zan iya cewa zan ci gaba da sana’ar mahaifina ba ko a’a, kasancewar Allah ne ke shirya komai. Idan Allah Ya nufi abincina, to sai ki ga Allah Ya nufe ni da yin sana’ar. A yanzau dai ina fuskantar harkar karatuna ne a Kwalejin Fasaha da ke Kano.” Inji shi.
Lawali Wazirin dan Indo, shi ne babban yaronsa da suke gudanar da wanann sana’a tare wanda kuma yakan wakilci marigayin a lokuta daban-daban. Ya bayyana wa Aminiya cewa a daren da marigayin zai rasu, ya yi kiransa inda ya gaya masa cewa akwai bukukuwa biyu da aka gayyace su, don haka shi zai je guda daya, sanann shi marigayin ya tafi wurin daya bikin.
“A cikin daren, kafin ya shiga gida wurin iyalinsa, ya yi kirana yake gaya min cewa an gayyace mu bukukuwa biyu a mako mai zuwa. Don haka ya gaya min cewa ni zan tafi na garin Marabar Jos, shi kuma zai je na Sakkwato. A nan na amsa masa da to. Ashe ba zai je ma wurin bikin ba” Inji Wazirin dan Indo.
Shi ma Yusuf Bagobiri Makadi, wanda ya bayyana cewa sun dade tare da marigayin tun lokacin da ya fara waka a Sakkwato ya bayyana marigayin a matsayin mutum mara kyashi.
“Alhaji ba shi da kyashi. Mun zauna da shi zama na dadi da taimako da jin kai. Kullum tunaninsa ya taimaka wa na kasa da shi. Mu kuma a matsayinmu na yaransa mun yi masa biyayya daidai gwargwado.” Inji shi.
Malam Sa’adu Muhammad, shi ne babban marokin marigayin ya bayyana marigayin a matsayin mutum mai son zaman lafiya, inda ya ce marigayin ba shi da abokin fada ko gaba a tsakaninsa da mawaka ’yan uwansa da kuma jama’ar gari.
A cewarsa, ko gabar da ta wanzu tsakanin marigayin da kuma mawaki marigayi Ali Makaho, dan Indo din bai yi nufin yin gabar ba, sai dai don babu yadda zai yi kasancewar abin ya fi karfinsa.
“Asalin rigimar, ba wai da Ali Makaho aka yi ba, abin ya faru ne tsakanin marigayi dan Indo da Haruna Uji. Ba na mantawa a Garun Gabas aka gayyace mu biki, sannan kuma an gayyato Haruna Uji. Sai aka fara ba Haruna Uji dama ya yi wasa. A lokacin kudi na da daraja, dan Indo ya fitar da Naira dubu biyu ya lika wa Haruna Uji. Bayan ya gama wasansa a wurin sai aka umarci dan Indo ya koma kofar gidan Sarki ya yi nasa wasan a can.
“To, me zai faru muna zuwa wurin za mu fara wasa sai ga Haruna Uji ya zo wurin yana kokarin fara wasa. Ganin haka sai marigayi dan Indo ya yi kirana, yake tambayata yaya haka, Haruna Uji zai zo wurin ya nemi yin wasa? A nan ni kuma na gaya masa cewa tunda a matsyainsa na babba bai ja girmansa ba, to mu ma ba za mu ji nauyin take girman nasa ba.
“Kasancewar kayan kidanmu ya fi nasa, a nan muka saki kidan da ya fi nasa, to tun daga wannan lokaci sai aka rika samun rashin jituwa tsakanin dan Indo da Haruna Uji. Shi kuma Ali Makaho sai ya karbi rigimar don goya baya ga Haruna Uji. To daga nan fa sai yamutsi ya koma tsakanin Ali Makhao da dan Indo, suka yi ta yi wa junansu wakokin batanci. A karshe dai maigidan dan Indo, Alhaji Zubairu Baba ya yi wa dan Indo magana cewa kada ya sake mayar wa Ali Makaho wata magana. To, kin ji asalin rigimar, ba kamar yadda mutane ke dauka ba.” Inji babban marokin dan Indo.
Rahotanni sun bayyana cewa marigayi dan Indo, wanda asalinsa dan Jihar Sakkwato ne ya fara wanann sana’a ta waka tun zamanin Shugaban kasa Shehu Shagari.
“Da ma ya dade yana waka tun zamanin Shagari, a lokacin bai dawo Kano da zama ba. Farkon zuwanmu Kano, an gayyace mu mu yi wa man shafawa Stella Mai Gurguwa talla. To tun daga nan mukan shigo Kano mu yi wasa mu koma. To muna nan muna haka sai wata rana a bikin Jummai Fagge sai Allah ya hada mu da Alhaji Zubairu Baba. A nan ya nemi dan Indo ya dawo Kano da zama, a nan ne kuma ya saya masa gidan da yake ciki, wanda shi kuma cikin budin Allah marigayin ya sayi filaye a kusa da gidansa ya gina gidaje ya sanya mu (yaransa) ciki; a hankali muka rika zuwa gida muna dauko iyalanmu suna dawowa Kano.”
Marigayin ya rasu yana da shekaru 55 da haihuwa. Haka kuma ya rasu ya bar matar aure daya da ‘ya’ya shida. Tuni dai aka yi jana’izar marigayin kamar yadda addini ya tanada.