Yadda mawakin Hausa ya kubuta bayan an sace shi a Adamawa
A ranar Asabar da ta gabata ce aka sace shahararren mawakin Hausa, Ado daukaka a Yola, Jihar Adamawa, inda ya kwashe kwanaki shida a hannun mutanen da suka yi garkuwa da shi, kafin ya kubuta a ranar Laraba da ta gabata. An sace mawakin ne bayan da ya saki sabon faifan wakokinsa, faifan da ke […]
A ranar Asabar da ta gabata ce aka sace shahararren mawakin Hausa, Ado daukaka a Yola, Jihar Adamawa, inda ya kwashe kwanaki shida a hannun mutanen da suka yi garkuwa da shi, kafin ya kubuta a ranar Laraba da ta gabata.
An sace mawakin ne bayan da ya saki sabon faifan wakokinsa, faifan da ke dauke da wata waka da ke jan hakali da gargadi ga ’yan siyasa masu satar dukiyar al’umma.
Ado, wanda mazaunin unguwar Lumo Koppi da ke Nasarawo, Jimeta ne, matansa na aure ne suka tabbatar wa manema labarai cewa: “Tun da ya fita Sallar asuba, wasu mutane suka zo gida nemansa, sai muka fada musu cewa ya tafi masallaci. Tun daga wannan lokacin kawo zuwa yanzu ba mu san inda yake ba.”
Ganin karshe da aka yi wa mawakin shi ne tun asubahin ranar Asabar da ta gabata, lokacin da ya fita domin gabatar da Salla.
“Mun je har ofishin ’yan sanda domin nemansa aka ce har yanzu ba a san inda yake ba.” Inji matarsa wadda ta nemi da a sakaya sunanta.
Mutane da dama wadanda suke yawan jin wakokin Ado, sun alakanta batansa da sabuwar wakarsa da ya saki mai taken ‘Gyara Kayanka’ wadda a cikinta yake bayyana cewa wasu ’yan jam’iyyar APC mayaudaran mutane ne.
“Yadda abubuwa ke faruwa a jihar nan ba za su haifar da da mai ido ba, domin suna so su hana duk masu ankarar da su ta hanyar waka a jihar nan.” Inji su.
Shugaban kungiyar masu kishin Adamawa, Hussaini Gambo, ya yi tir da sace mawakkn da aka yi kuma ya ce wannan ba abu ne mai kyau ba.
Ana kan neman shi ne, sai a ranar Laraba da ta gabata, aka tsince shi a wani daji da ke kusa da kauyen Lafiya-Lamurde mai nisan kilomita 80 daga birnin Yola.
Da yake gaya wa wakilinmu ta waya, yadda ya tsira, daukaka ya ce wadanda suka sace shi suna dauke da makamai kuma sun wahalar da shi, sun yi masa barazana, domin kuwa sun ce ya yi shiga sharo ba shanu cikin al’amuransu. Ya ce bayan da suka sace shi, sun rufe masa idanu, suka tsare shi a wani gida a cikin garin Yola tsawon kwana biyar, kafin daga bisani su fitar da shi zuwa wani daji kusa da Lamurde, suka jefar da shi.
Da yake karin bayani game da al’amarin, mawakin ya ce da mutanen suka same shi, kafin su sace shi, sun ce daga Kano suke kuma sun dade suna jin wakokinsa masu dadi na siyasa, don haka suna son ya kirkira masu wakar siyasa ne.
“Ina shiga motarsu sai suka sanya mani bindiga a ka, suka daure mani idanu, suka boye ni a wani gida da ke cikin Yola. Ba su doke ni ba amma sun rika ciyar da ni da biskit da madara sannan suka yi mani gargadin cewa daga yanzu in kiyaye, in daina shiga harkar mutanen da da ba ta shafe ni ba.
Duk da cewa mutane na zargin cewa sace shi ba za ta rasa nasaba da wakar da ya yi, wacce a ciki yake gugar zana ga wani dan majalisar jiharsu ba, amma dai mawakin ya ce a yanzu ba zai alakanta al’amarin da wakar ba.
Jami’in hullda da jama’a na ’yan sandan Jihar Adamawa, SP Othman Abubakar ya tabbatar da cewa lallai an tsinci mawakin ne a kauyen Tino da ke karamar Hukumar Lamurde. Ya ce an same shi cikin koshin lafiya sai dai ya zuwa yanzu ba su kama kowa da ake zargi ba.