Yadda Mayaƙan Lukarawa suka addabe mu —Sakkwatawa

Mayaƙan Lakurawa suna ƙwatar zakka tare da dukan masu aske gemu da sauraron kaɗe-kaɗe a yankin Jihar Sakkwato, inda suke yaudarar matasa da kuɗi domin shiga aƙidarsu

Yadda Mayaƙan Lukarawa suka addabe mu —Sakkwatawa

Al’ummomi da mahukunta a Jihar Sakkwato sun koka bisa yadda ’yan bindigar ƙasar waje masu tsattsuran ra’ayin addini, waɗanda aka fi sani da Lukarawa suke addabar su.

A ranar Alhamis Hedikwatar Tsaron Nijeriya ta tabbatar da ɓullar mayaƙan Lukarawa a jihohin Sakkwato da Kebbi, lamarin da ta ce ya ƙara dagula matsalar tsaro a yankin Arewa maso Yamma.

Wani mazaunin Jihar Sakkwato, Malam Muhammadu Bauni, ya ce, “mayaƙan suna iƙirarin ƙare mu daga ’yan fashin daji amma kuma suna takura wa rayuwarmu da wasu dokoki masu tsauri.

“Kwanan nan suka yi wa wasu matasanmu duka saboda sun aske gemu da sauraron kaɗe-kaɗe da kuma yin askin da bai dace ba.

“Mu Musulmi ne kuma ba ma adawa da Shari’ar Muslunci, amma ba zai yiwu a kafa gwamnati a cikin wata gwamnati ba.

“Abin da suke yi bai dace ba, saboda babu inda aka ayyana hukunci kan aske gemu ko sauraron kaɗe-kaɗe.

“Abu mafi takaici shi ne sun fara jan ra’ayin matasanmu sun shiga cikinsu, duk da cewa ba sa kashe mu ko yin garkuwa da mu domin karɓar kuɗin fansa.

“Su jami’an gwamnati ne damuwarsu. Yanzu kwana shida ke nan da suka zo suka tafi da wata ma’aikaciyar kiwon lafiya a wani ƙaramin asibiti, kuma har yanzu ba a kara jin ɗuriyarta ba.

“Su suka kai yawancin manyan hare-haren da ake kai wa jami’an tsaro.

“Idan suka ga baƙo, tafiya suke da shi sansaninsu su titsiye shi, idan suka lura cewa jami’in gwmanati ne, to kashinshi ya bushe, idan ba jami’in gwamnati ba ne, za su dawo da shi.

“Haka kuma suke wa mutanenmu, duk wanda ya yi kwanaki ba ya nan, idan ya dawo za su ɗauke shi su je su yi ma sa tambayoyi, kafin su sake shi. Haka muke rayuwa.”

Malam Muhammadu Bauni ya ce sun kai rahoto wajen jami’an tsaro da mahukunta amma har ta yanzu ba su ɗauki wani ƙwaƙƙwaran mataki a kan lamarin ba.

“Akwai dai lokacin da sojoji suka kawo samame garinmu suka kashe biyu daga cikinsu, amma daga lokacin ba su sake dawowa ba. Mu kuma ba za muniya faɗa da su ba, saboda yawansu, kuma suna da miyagun makamai.”

Wani mazaunin yankin ya ce Lukarawa suna magana da harsuna daban-daban kamar Turanci da Hausa da Fulatanci da Buzanci da Kanuri da kuma Tuba.

Ya ce a duk lokacin da Lukarawa suka gudanar da wa’azi ko lacca, sukan tabbatar sun fassara da harsuna daban-daban domin kowa ya fahimci saƙon da kuma aƙidarsu.

“Su da yawa suke zuwa, sai su tura wasu a kan bauta 10 zuwa 15, su su shiga wasu ƙauyuka da garuruwa.

“Suna kuma karɓar Zakka, kuma duk wanda ya ƙi biya, za su kwace dabbobinsa, har sai lokacin da ya biya kafin sun dawo masa da dabbobin,” jin ji shi.

Wani mazaunin yankin ya shaida wa sashen Hausa na BBC cewa Lakurawa sun yi sansanoni a ƙananan hukumomi biyar a Jihar Sakkwato, amma sun fi ƙarfi a biyu.

“Misali, a Ƙaramar Hukumar Gudu akwai da yawa, har a kusa da sakatariyar ƙaramar hukuma. Kusan ba bu inda ba da shiga ba tare da wani fargaba ba.

Suna yaudarar matasa da N1m

A ’yan kwanakin baya Shugaban Ƙaramar Hukumar Tangaza, Alhaji Isa Salihu Kalenjeni, ya yi zargin cewa Lukurawa na yaudarar matasan yankin da kuɗi Naira miliyan ɗaya-ɗaya domin shiga tafiyar tasu da juya wa gwamnati baya.

Ya bayyana wa wakilinmu ta waya cewa mayaƙan suna yin wa’azi tare da aiwatar da Shari’ar Muslunci a ƙauyukan yankin.

Ya ce, “Suna tursasa mutane biyan Zakka, suna ƙwace musu dukiya. Ko a kwanan nan sai da suka ƙwace Naira miliyan biyu a hannun wani mai shago. Sun kuma kwace wata mota sai da aka biyan N350,000 sannan suka sakw ta.”

Martanin Gwamnatin Sakkwato

Da yake magana game da lamarin, Mataimakin Gwamnan Jihar Sakkwato, Idris Gobir, ya ce da farko ana ɗaukar Lakurawa a matsayin ƙungiyar addini.

Ya ce amma daga bisani aka gano suna ɗauke da muggan makamai kuma an gano ayyukansu na laifi a ƙananan hukumomi biyar a jihar.

Gobir ya ce barazanar ƙungiyar na ƙara ƙaruwa, amma hukumomin tsaro na aiki tuƙuru domin shawo kan barazanar.

Ya bayyana haka ne a lokacin da masu halartar kwana na 33 a Kwalejin Tsaro na Ƙasa da ke Abuja, da suka kai ziyara jihar.

Sojoji sun tabbatar da zaman Lakurawa

A ranar Alhamis Daraktan Yaɗa Labarai na Hedikwatar Tsaro ta Nijeriya, Manjo-Janar Edward Buba, ya tabbatar da samuwan Lakurawa a Jihohin Sakkwato da Kebbi.

Edward Buba ya ce Lakurawan sun ƙara ta’azzara matsalar tsaro a yankin Arewa maso Yamma, amma tuni sojoji suka taka musu burki, kuma duk abin da za su yi, nan ba da jimawa ba sojoji za su ga bayansu.

Ya sanar da haka ne a lokacin da ya fitar da jerin manyan ’yan ta’adda tara da ake nema ruwa a jallo.