Yadda maza ke cin kasuwar kwalliyar Sallah a Kano
Sai dai a wannan shekara an samu maza da suka yi tarayya a cikin sana’ar da aka fi sanin mata a ciki.
Bisa al’ada a Jihar Kano, mata aka sani da yi wa ’yan uwansu mata ƙunshi da kitso, da sauran kyale-kyale kowacce sallah.
Wannan ya faru ne dalilin tasirin al’ada da kuma addinin Musulunci da jihar ta yi ƙaurin suna da shi.
To, sai dai a bana Aminiya ta lura maza sun fara shiga sana’ar gyaran gashi da ƙunshi, duk da cewa abu ne da ba a saba ganinsa ba a jihar.
Wani matashi da ya nemi a sakaya sunansa, ya ce ya fara sana’ar gyaran gashi ne domin rufa wa kansa asiri, duk kuwa da surutun da yake sha daga abokansa da ma sauran mutane.
“An sha kirana da ɗan daudu, a gaba da bayan idona, amma ba na damuwa saboda halalina nake nema. Su da suke zagina, su suke fama da talauci.
“A wannan sana’ar na gamu da ƙawaye da abokanan arziƙin da a yanzu sun zamo tamkar ‘yan uwa a wajena.”
Shi ma dai wani fitaccen mai gyaran jikin da aka fi sani da ‘Mai Kyau’, ya bayyana wa Aminiya cewa babu abin da zai ce da sana’ar sai godiyar Allah.
“Idan kika duba kofar shagona, ya fi na kowa cika. Ke ma shaida ce. Kwastamomin ba iya Kanawa ba ne har da waɗanda suke zuwa daga wasu ƙasashen kamar Saudiyya.
“AlhamdulilLah shagunana yanzu uku ne, kuma ina da ma’aikatan da nake biyan su albashi. Ba ruwana da surutun mutane saboda ba sata nake yi ba. Neman na rufa wa kai asiri nake yi.
Kalubalen da Mata ke fuskanta a sana’ar
Baya ga mazan, Aminiya ta tattauna da matan da ke cikin wannan sana’a, inda wata mai suna Aisha Shola ta bayyana mana cewa babban ƙalubalen da suke fuskanta a bana bai wuce ƙarancin kwastomomi da tsadar kayan gyaran gashin ba.
“Bana muna fama da ƙarancin kwastomomi, ga tsadar kayan gyaran gashi.
“Misali ƙarin gashin da a baya ake sayarwa Naira 2000 zuwa N5000 a bara, bana N5,000 ne wani wajen ma N7,000. Kitson da a baya mu ke yi Naira 2,000 yanzu daga Naira 5,000 ne zuwa Naira 10,000.
“Don haka mutane ke zaɓen abin da suke ganin dole ne su bar mu da rashin ciniki,” in ji ta.