Yadda mazan Afirka ke shigar matan Larabawa domin shiga Dubai
Mutanen dau ba kokarin tsallakawa can ne don fatan samun rayuwa mai inganci
A baya-bayan nan ne aka kama wasu maza uku ’yan asalin nahiyar Afirka wadanda suke ’yan asalin kasar Aljeriya bisa zarginsu da shigar mata a matsayin ’yan mata na Larabawa domin isa birnin Dubai da ke jasar Hadaddiyar Daular Larabawa.
Lamarin da ya yi kama da wani fim din barkwanci mai suna “White Chicks”, ana iya ganin wadanda suka aikata hakan
bakaken fata su uku da rabin fuskokinsu a lullube da kwalliya a fuskokinsu da tufafin mata, wanda aka gano suna daukar hoto tun a Aljeriya.
- Bashin da ake bin Najeriya ya karu zuwa tiriliyan 40
- Duk abin da muke yi ’yan sa-kai ne suka koya mana – Turji
Rahotanni sun ce, an kama mazan uku tun a jasar Aljeriya, bayan da jami’an tsaro suka lura cewa ba wadanda suke
ikirarin jinsin ba ne a matsayin matan Larabawa sanye da kayan gargajiyar mata da suka hada da mayafin rufe fuska da nikabi.
Sun yi juriyar rufe sassan fuskokinsu da wani mayafi mai kauri, kuma sun yi amfani da launin bakin tufafi mai kauri
don kara ba su damar wucewa a matsayin mata, amma hakan bai wadatar ba.
A cewar kafar labarai ta Kaya 959 ta Afirka ta Kudu, mazan uku na kokarin isa Dubai ne da fatar samun rayuwa mai inganci a kasar Larabawa mai wadata, amma abin bakin ciki a gare su, shirin nasu ya ci tura bai kammalu ba sai a Aljeriya.
Ba a san irin hukuncin da za su fuskanta ba, amma za a iya mayar da su kasarsu ta asali.
Hotunan wadannan mutum uku sun karade kafafen labarai kusan mako guda suna zagaya shafukan sada zumunta a
jaridun Afirka da na Larabawa, kuma suna samun martani iri-iri daga jama’a.
Yayin da wasu mutane suka bayyana su da sun jin kunyar yunkurin shigar mata
na bogi, wasu kuma sun yaba da fasahar kwalliyar da suka yi.
Wani mutum ya yi sharhi da cewa, “na gamsu a cikin hoton farko a matsayin ’yan matan Larabawa”.
Wani kuwa cewa ya yi, “ina son salon kwalliyar da suka yi.”
Duk da haka, batun asalin mutanen ya kasance batun muhawara a yanar gizo, inda wasu ke ikirarin cewa, su ’yan Najeriya ne, wasu kuma na cewa ’yan Mali ne, amma wannan ya kasance baya ga batun wannan labarin.
A baya mun fito da irin wannan kame-kamen, irin na wani mutumin Senegal da ya sanya kayan kwalliyar mata domin ya yi jarrabawa a madadin
budurwarsa, don haka ba a taba jin labarin irin wannan ba.