Yadda mazauna Gaza suke azumi a tsakiyar hare-haren Isra’ila
Fiye da mako biyu kenan da al’ummar Falasdinu da ke yankin zirin Gaza suka samu kansu cikin hare-haren sojin Isra’ila.Tun kafin wannan rikicin, zirin Gaza yanki ne da Isra’ila ta yi wa kawayya. A cikin watan azumin nan ne kuma ta fara kai farmaki ga mazauna yankin wadanda galibinsu Musulmi ne.Wata mata mai suna Aza […]
Fiye da mako biyu kenan da al’ummar Falasdinu da ke yankin zirin Gaza suka samu kansu cikin hare-haren sojin Isra’ila.
Tun kafin wannan rikicin, zirin Gaza yanki ne da Isra’ila ta yi wa kawayya. A cikin watan azumin nan ne kuma ta fara kai farmaki ga mazauna yankin wadanda galibinsu Musulmi ne.
Wata mata mai suna Aza da ke zaune a can, ta bayyana wa kafar yada labaran Sudan bision cewa, “azumin bana ya sha bamban da na bara saboda rikicin da ke faruwa a nan.”
Matar ta ce: “Yakamata ne ni da ’yan uwana mu fara shiryawa Sahur ta hanyar tashi da misalin karfe 3:00 na safe. Amma hakan ba ya yuhuwa. Muna amfani da irin wannan lokaci ne da gari ya yi tsit don runtsawa mamadin Sahur, saboda a lokuta da dama karar farmakin Isra’ila ba ya barinmu barci a farkon dare. Baya ga wannan, muna zama cikin duhu ne a kowane dare saboda yadda ake dauke wutar lantarki. Hakazalika, sakamakon yanayin zafi da muke ciki a nan, barci na yin wuya idan fanka ko na’urar sanyaya daki ba sa kunne,” inji ta.
Aza ta kara da cewa da rana ma yanayin ba mai dadi ba ne. “Muna da sa’o’i takwas ne da za mu yi wanka da wanki da sauran aikace-aikace kafin rana ta fadi. Rayuwata ba ta da bambanci da ta sauran Falasdinawa miliyan daya da dubu dari takwas da ke yankin.”
Matar ta ci gaba da cewa: “Sahur da buda baki wani muhimmin lokaci ne a watan azumi. Amma mu a nan da wuya ka ga wadansunmu sun kai wani abu baka saboda hankalinmu ya fi tafiya wajen sauraron labarai don neman sanin ta inda haren-haren Isra’ila ke zuwa,”inji ta.
Wannan rikicin da ke faruwa ba wai kawai yana hana mazauna Gaza cin abinci da warwala yadda ya kamata ba ne. Har ila yau, rikicin ya yi sanadiyyar dakile dukkannin taimakon abinci da kayayyakin taimakon da ke shiga yankin wanda ke karkashin kawayyar Isra’ila. A halin da ake ciki duka iyakokin Gaza da sauran kasashe kamar Masar suna rufe ne. Amma ko da ma iyakokin suna bude, da wuya firgici ya bar mazauna yankin su samu sukunin zama don yin Sahur da buda baki saboda yadda ake zubar jini ba kakkautawa.