Yadda mazauna iyakar Najeriya da Nijar suka shiga ha’ula’i bayan rufe boda

Mun ziyarci garuruwan Illela, Maigatari, Jibiya da Kwangalam da ke kan iyakar Najeriya da Nijar don jin halin da suka tsinci kansu bayan rufe iyakokin

Yadda mazauna iyakar Najeriya da Nijar suka shiga ha’ula’i bayan rufe boda

Motoci a kan iyakar Najeriya da Nijar

’Yan Najeriya mazauna yankunan da ke iyakar kasar Jamhuriyar Nijar na dandana kudarsu sakamakon tsadar rayuwa da tashin gwauron zabon kayan masarufi, tun bayan rufe bodar da Najeriya ta yi a watan Agusta.

Anya wannan rufe boda da Kungiyar ECOWAS ta sa aka yi, ba za a ci kai da kai ba?

Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci ya ziyarci garin Illela a Jihar Sakkwato da Maigatari a Jihar Jigawa, da kuma Kwangalam da Jibiya a Jihar Katsina, domin jin halin da mazauna garuruwan suka tsinci kansu a tsawon lokacin da ka rufe bodar, a matsayin garuruwan ma masu alakar kasuwanci da makwabtansu da ke Nijar.

Shirin na kuma dauke da fashin baki tare da wani masanin tattalin arziki a game da wannan al’amari.

Domin sauke shirin kai tsaye, latsa nan

Jerin Manyan Dambarwan Kano a 2024

Rufe ‘boda’ ya kawo yunwa da rashin aiki a Arewa —CNG

Bin diddigi: Gaskiyar batun kai hari a Bankin CBN

NAJERIYA A YAU: Gaskiyar Lamari Game Da Harin Sojoji Kan Al’umma A Sakkwato