Yadda mesa ta hadiye kada a kasar Austiraliya

An yi artabun kwatar rai a tsakanin kada da mesa a kasar Austiraliya, inda maciyar ta hadiye kada, kamar yadda wadanda al’amarin ya auku a gabansu suka bayyana wa Kamfanin Dillancin Labarai na AFP.Mista Trabis Corlis, wanda ya kalli fafatawar da aka yi a tsakanion kada da mesa a gabar kogin Moondarra da ke kueensland, […]

Yadda mesa ta hadiye kada a kasar Austiraliya

An yi artabun kwatar rai a tsakanin kada da mesa a kasar Austiraliya, inda maciyar ta hadiye kada, kamar yadda wadanda al’amarin ya auku a gabansu suka bayyana wa Kamfanin Dillancin Labarai na AFP.
Mista Trabis Corlis, wanda ya kalli fafatawar da aka yi a tsakanion kada da mesa a gabar kogin Moondarra da ke kueensland, kusa da garin da ake hakar ma’adinai a tsaunukan Mounta Isa da ke kasar Austiraliya, inda ya bayyana cewa, mesar mai tsawon mita uku “da ke cikin koshin lafiya.” Ita kuwa kadar, tana da tsawon mita guda, kuma a lokacin fadan da aka fafata, ta nade a jikin mesa. “Sun dade sunan fafata fada a cikin ruwa,” kamar yadda ya bayyana wa Kamfanin Dilanin Labarai na AFP.