Yadda Messi ya zama gwarzon FIFA na shekerar 2022
Alexia Putellas ita ce gwarzuwar kwallon kafar mata ta duniya ta Fifa ta 2022.
Dan wasan gaba na Argentina, Lionel Messi, ya zama gwarzon shekara na Hukumar FIFA bayan lashe kyautar dan wasa mafi bajinta a shekarar 2022.
An bai wa Messi kambun ne yayin bikin bayar da kyautar gwarazan ’yan wasa da ya gudana ranar Litinin a birnin Paris.
- Jami’an tsaro sun cafke Alhassan Doguwa
- INEC ta ci gaba da tattara sakamakon zabe duk da zanga-zangar da ta barke a Abuja
Messi ya doke abokin wasansa na PSG kuma wanda suka barje gumi a wasan karshe na Gasar Kofin Duniya, Kylian Mbappe a tseren lashe wannan kyauta.
Hakazalika, ya shige gaban Karim Benzema baFaranshe da ya lashe kyautar Ballon d’Or a bara.
Wannan ne karo na biyu da Messi ke lashe kyautar ta gwarzon shekara na FIFA bayan makamanciyar kyautar da ya lashe a shekarar 2016 lokacin da FIFA ta balle daga kungiyar da ke shirya bayar da kyautar Ballon d’Or a Faransa.
Kyautar wadda manajojin kwallon kafar kasashe da ‘yan jaridu da kuma magoya baya ke kada kuri’a gabanin tantance dan wasan da zai lashe ta, daukacin wadanda suka kada kuri’a sun yi amannar cewa Kyaftin din na Argentina ya cancanta lura da namijin kokarinsa wajen kai Kofin Duniya gida.
Messi dai ya zura kwallaye 2 a wasan karshe da Faransa mai rike da kofin a wancan lokaci ta yi rashin nasara a hannunsu duk da kwallaye 3 da Kylian Mbappe ya zura a wasan.
Messi ya kuma lashe kyautar kwallon zinare yayin Gasar Kofin Duniya a Qatar a matsayin dan wasa mafi bajinta duk da kasancewar Mbappe mafi zura kwallaye a gasar.
’Yar wasan Barcelona, Alexia Putellas ita ce gwarzuwar kwallon kafar mata ta duniya ta Fifa ta 2022.
Haka kuma, Lionel Scaloni, wanda ya ja ragamar Argentina ta lashe Kofin Duniya a Qatar, shi ne ya lashe kyautar kocin da ba kamarsa.
Scaloni ya yi nasara a kan Pep Guardiola – wanda ya ja ragamar Manchester City ta dauki Firimiyar Ingila karo na shida da Carlo Ancelotti, wanda Real Madrid ta dauki La Liga da Kofin Zakarun Turai da FIFA Club World Cup da Euro Super Cup.