Yadda miliyoyin kudin da aka jefar a shara suka dawo wa mai su
Wani mutum ya zubar da kudin kasar Sin dubu 124 (kimanin Dirham 72,379), wato daidai da Naira miliyan 7,200,0000 a shara, sai ya samu kudin yayin da makwafciyarsa ta dawo masa da su. Lamarin dai ya auku ne a wani gari Liaoning da ke kasar Sin. Gidan talabijin na NDTb ya ruwaito cewa Wang ya […]
Wani mutum ya zubar da kudin kasar Sin dubu 124 (kimanin Dirham 72,379), wato daidai da Naira miliyan 7,200,0000 a shara, sai ya samu kudin yayin da makwafciyarsa ta dawo masa da su. Lamarin dai ya auku ne a wani gari Liaoning da ke kasar Sin.
Gidan talabijin na NDTb ya ruwaito cewa Wang ya fito wajen gidansa rike da jakunkunan leda biyiu na shara. daya daga cikin jakunkunan na dauke da kudi da za a kai banki ajiya, inda kuma sauran jakunkunan shara ce.
Sai ya cukwikuye jakar a cikin shara ya jefa wa masu kwasa. Da isarsa banki ya fahimci cewa jakar kudin ce ya jefar.
Wang ya kir a ’yan sanda ganin cewa ya kasa gano kudinsa a cikin shara. Kyamarar daukar hotunan al’amuran da ke wakana ta CCTb a yankin ta nuna wani mutum da ya dauki jakar ya wuce da ita.
Daga bisani an gano jakar a wajen wata mata, wadda kuma makwafciyar Wang ce, wadda ta kai wa ’yan sanda jakar kudin don su gano mai ita.
Wang dai hankalinsa ya kwanta bayan da aka dawo masa da kudinsa.