Yadda mu ke tantance ingancin mota da kwamfuta – Daraktan bOA
Cibiyar tantance ingancin motoci ta Abuja, ita ce ta farko a Najeriya da ke gudanar da ayyukanta da kwamfuta, Wakilinmu ya zanta da Daraktan bOA na yankin Birnin Tarayya, Malam danjuma Aliyu Garba, inda ya bayyana dalilan kafa cibiyar da kuma yadda suke gudanar da ita. Aminiya: Ka gabatar mana da kankadanjuma A. Garba: Sunana […]
Cibiyar tantance ingancin motoci ta Abuja, ita ce ta farko a Najeriya da ke gudanar da ayyukanta da kwamfuta, Wakilinmu ya zanta da Daraktan bOA na yankin Birnin Tarayya, Malam danjuma Aliyu Garba, inda ya bayyana dalilan kafa cibiyar da kuma yadda suke gudanar da ita.
Aminiya: Ka gabatar mana da kanka
danjuma A. Garba: Sunana danjuma Aliyu Garba, ni ne shugaban hukumar bIO na yankin birnin tarayya Abuja
Aminiya: Me ya ba ku sha’awar kirkiro cibiyar tantance ingancin motoci da kwamfuta?
danjuma Garba: Kamar yadda duniya ke samun ci gaba a kullum a fannin abubuwa na zamani, haka hadurra ma ke karuwa a kullum, bincike ya nuna cewa rashin ingancin ababen hawa na gaba-gaba wajen haddasa hadari. Ana cikin haka sai wani kamfani da yake amfani da hanyoyin zamani wajen tantance ingancin motoci ya nemi yin hadin gwiwa a tsakaninsa da Ma’aikatar kula da birnin tarayya Abuja a kan wannan al’amarin. An kulla yarjejeniyar ne a lokacin tsohon ministan Abuja da ya gabata Bala Muhammad.
Da farko sun kafa irin wannan wuri a kan titin Kubwa zuwa Zuba, da kuma yankin Kubo da ke kan titin Nyanya, kuma akwai shirin kafa ire-iren wadannan wurare har shida a sauran kusurwowin shigowa Abujan, don saukaka wa al’umma hulda da wajen a duk inda suke. A ka’idar mota ko da sabuwa ce ka sayeta yana da kyau ka kaita irin wannan waje a tantance ingancinta, saboda wani lokaci kamfani na kuskure a wajen kera mota.
Haka nan mota idan ana jigilar da ita ya kamata duk wata shida a yi mata gwaji, ita kuma ta shiga haka nan ana bukata duk shekara a dubata sau daya. Kamfanin zai ci gaba da ikon gudanar da wajen zuwa shekara 15, daga nan ne kuma wajen zai zama mallakin ma’aikatar birnin tarayya dari bisa dari, sai dai a yanzu haka kashi 10 cikin 100 na abin da suka samu ne mallakar hukuma. Kuma jami’an da ke aiki a wajen daga wajenmu suke, inda a ka ba su horo na musamman na gudanar da shi.
Aminiya: Wadanne irin ayyuka suke aiwatarwa?
danjuma Garba: Abubuwan da suke yi sun kasu kashi biyu a kwai wanda ake yinsa kai tsaye, akwai kuma wanda a ke tantance shi da kwamfuta. Alal misali kamar tantance fitilar mota don ganin haskenta bai gaza ba, ta yadda matuki ba zai ga hanya yadda ya dace ba, ko kuma bai dara ba, ta yadda zai cutar da mai zuwa daga daura da shi, sai kuma tabbatar da cewa ya na kan saitin bai karkata kasa ko sama ba, wannan duk da na’urar kwamfuta ce a ke tantancewa. Akwai kuma tantance tsayuwar taya (wheel balance) da karfin burki, sai kuma inda za a haska karkashin mota da fitila daga cikin wani rami, don tantance yanayin karkashinta, kafin daga bisani a buga maka sakamako ta kwamfuta ko motarka ta cika ka’idojin hawa hanya ko ta gaza.
Idan ta gaza za a ba ka kwana 30 ka je ka yi gyara, bayan nan sai ka sake dawowa, sai dai abin da a ka biya a hanunka na farko ya wadatar ba za ka biya a yayin dawowarka ba, sai dai idan ka wuce lokacin da a ka ba ka ba ka dawo ba akwai tara. Izuwa wannan wata na Agusta cikin motoci dubu 11 da a ka tantance, kashi 70 a cikin 100 sun ci jarabawa, a yayin da kashi 30 kuma suka gaza. Sai dai har yanzu shawara muke bayarwa, don tsaro ga mai mota da kuma al’umma, ba bu tirsasawa a ciki.
Aminiya: Direbobin tasi na korafin ku na kuntata masu. Da farko ku na tilasta musu yin fentin Abuja, sannan idan suka yi fentin ma ba su tsira ba ?
danjuma Garba: Fentin tasi ba lasisin aikata laifi ba ne. sai dai idan direba ya kiyaye sauran ka’idoji, kamar na tsayawa a wurin da a ka amince, inda ya yi haka ba dalililin kama shi.
Aminiya: Direbobi na samun matsala a wajen lasisin tuki a kwai zargin cewa, idan mutum ya biya kudin lasisi ta hukumar FRSC kuna nuna rashin amincewarku da lasisin kamar yadda su ma a ke zarginsu da yi wa masu lasisin wajenku; shin a ina ne ya kamata direba ya nemi lasisi?
danjuma Garba: Lasisisi da muke kamawa bai da nasaba da inda a ka ba da shi. Abin da muke la’akari da shi, shi ne, lasisin da kwamfuta bai amince da shi ba, hakan ko na faruwa ne a sakamakon bukatar lasisi ta bayan fage da wasu ke yi ba tare da sun bi ka’ida ba. ka’idar ita ce idan sabon lasisisi ne ka tabbata ka halarci makarantar koyan tuki, sannan bayan an tabbatar da koyonka, ka zo wajenmu a dauki bayananka, wanda ya hada da zanen yatsun da aka dauka a kwamfuta ka zauna a gaban kemera. Idan ko sabuntawa ne kana iya cika bayanai a duk inda kake ta kwamfuta sannan ka taho wajenmu daga bisani ka karbi lasisi.
Aminiya: takwarorinku na FRSC an sansu da karban tara ta banki sannan a ba da rasiti, a yayin da ku kuma a ke cewa ku na karban kudi ne kai tsaye ba tare da ba da rasiti ba?
danjuma Garba: Wannan ba gaskiya ba ne, muna ba da takardun biyan kudin banki ga wadanda muka kama da laifi, don biyan kudinsu ta banki. Kodayake ana iya samun batagari da suke yin hakan, to kiranmu ga al’umma shi ne a duk lokacin da aka ci su tara, su tabbata sun biya kudi ta banki sannan su kawo wajenmu su karbi rasiti, su guji nuna sauri da mika cin hanci a maimakon biyan tara da aka yi musu.