Yadda muka bankado yunkurin tazarce a taron kasa – Wakilan Arewa
*Kutigi ya ce ba abin da ‘yan Arewa za su iya Wakilan Arewa a taron kasa, a karkashin kungiyarsu ta NDF, sun zargi shugabannin taron da shirya tarzarce ga Shugaba Goodluck Jonathan da sauran masu rike da mukaman siyasa, inda sabon kundin tsarin mulki da aka bullo da shi zai ba su damar wa’adin mulki […]

*Kutigi ya ce ba abin da ‘yan Arewa za su iya
Wakilan Arewa a taron kasa, a karkashin kungiyarsu ta NDF, sun zargi shugabannin taron da shirya tarzarce ga Shugaba Goodluck Jonathan da sauran masu rike da mukaman siyasa, inda sabon kundin tsarin mulki da aka bullo da shi zai ba su damar wa’adin mulki a karo na uku.
A wani taron ’yan jarida da kungiyar wakilan Arewa ta NDF ta kira, tsohon Sufeto-Janar na ’yan sanda, Ibrahim Coomassie ya ce kungiyarsu na zargin shugabannin taron da kulla makirci inda wata jaridar kasar nan ta buga babban labarinta a ranar 30 ga watan Yunin bana, inda aka bayyana yadda wani daga cikin wakilan taron ya shirya wa Shugaba Jonathan dabarun da za su ba shi damar zarcewa a mulki a karo na uku, tare da sauran masu rike da mukaman siyasa, da zarar an bullo da sabon kundin tsarin mulki ga Najeriya.
Tun a ranar Litinin aka raba wa wakilan taron sabon kundin tsarin mulki, wanda ake kokarin ganin ya maye gurbin wanda ake amfani da shi a halin yanzu. Kuma shugaban taron kasar, Idris Kutigi da mataimakinsa, Bolaji Akinyemi ba su halarci zauren taron ba a wannan ranar. Sakatariyar taron Gloria Azinge, wadda ta wakilci shugaban taron, ta sanar da wakilan cewa babu wata tattaunawa da za a yi, tamkar yadda aka tsara a da.
Sai dai kuma shugaban taron kuma tsohon babban mai shari’a na kasa Idris Kutigi ya ce Shugaba Jonathan ne ya ba shi dama ya rubuta sabon tsarin mulki kuma tunda ’yan Arewa su ne marasa rinjaye a taron, sai dai su fice daga taron domin babu abin da za su hana.
Kutigi ya fadi haka ne shekaranjiya Laraba a Abuja lokacin da yake ganawa da shugabannin wakilan Arewa da ke halartar taron.
Shugaban ya kira taron na gaggawa ne domin magance dambarwar da batun sabon tsarin mulkin ya jawo. Amma da wakilan suka ce masa taron kasa ba shi da hurumin sake rubuta sabon tsarin mulki, sai Kutigi, kamar yadda majiyar Aminiya a wurin taron ta bayyana, a fusace ya ce, ‘‘Shugaba Jonathan ne ya ba ni umarnin rubuta sabon kundin tsarin mulki ga al’ummar Najeriya.”
Ya kara da cewa, ’yan Arewa su ne marasa rinjaye a wurin taron, don haka suna da damar kaurace wa taron idan ba su amince da rubuta sabon tsarin mulki ba.
Wakilan na Arewa dai sun hau kujerar na-ki, suka ce ba su yarda da wani kundin tsarin mulki ba. Haka dai taron ya tashi ba tare da an cimma wata matsaya ba
A lokacin da Coomassie ya gabatar da jawabi ga manema labarai ranar Talata, ya yi nuni da cewa, sun nuna takaicin ganin yadda aka fito da fasalin sabon kundin tsarin mulkin, inda ya tuna cewa wani wakili a cikin taron ya taba jan hankalin taron game da sabon kundin tsarin mulki, a karkashin muhimman al’amuran kasa.
Ya ce, a daidai irin wannan lokaci da ya kamata shugabancin taron ya fito karara ya yi bayani game da al’amarin, sai shugabannin suka nuna rashin saninsu game da kundin, inda shugaban taron Mai shari’a Kutigi ya bayyana wa wakilan taron cewa, “Ba mu san komai ba game da takardun da aka rarraba. Ba mu da masaniya game da wani al’amari da aka amince da shi a karkashin wani kwamiti, ba mu kafa wani kwamiti na daban ba, baya ga tsayayyen kwamitin da muka kafa. Ba mu da masaniya kan hakan. Babu ruwanmu da shi. Wannan al’amari ma tuni aka yi watsi da shi,” kamar yadda aka buga a kofen kundin taron na ranar 30 ga Yuni.
Tsohon Sufeto-Janar din ya ce, “Kamata ya yi a ce, an kashe maganar “sabon kundin tsarin mulki” bayan maganar Kutigi. Amma ba haka al’amarin ya kasance ba. An sake bijiro da al’amarin, a lokutan zaman taron, kuma a kodayaushe akan wancakalar da shi.
Ya ce, wurin da kawai aka amince a yi amfani da kuri’ar raba gardama, shi ne kan al’amuran da suka jibinci kirkiro sababbin jihohi ko daidaita kan iyaka, bisa la’akari da tanadin Sashi na 8 a Kundin tsarin mulkin Najeriya na shekarar 1999. Wannan al’amari yana da tayar da hankali da cusa takaici.
Coomassie ya ce wakilai sun cika da mamaki, al’amarin ya tayar musu da hankali tare da cusa takaici ganin yadda kwatsam aka fito da “fasalin sabon kundin tsarin mulkin 2014,” a cikin jerin kundayen da aka raba wa wakilan taron a ranar Litinin.
“Mu wakilan Arewa a wajen taron muna tabbatar wa masu kishin Najeriya da masu kaunar dimokuradiyya, cewa ba mu da wata alaka ko masaniya da yunkurin samar da “fasalin sabon kundin tsarin mulkin 2014. “don haka, babu wata tantama mun yi watsi da shi, sannan mun nesanta kawunanmu da shi. Uwa-uba, babu wani abu da za mu yi da shi, saboda dalilan da suka shafi doka da tarbiyya tagari da siyasa,” inji shi.
Dalilin adawarmu
kungiyar NDF, ta yi bayanin cewa su ba zababbun wakilai ba ne, don haka ba su da hurumi da karfin ikon fitar da fasalin sabon kundin tsarin mulki ga Najeriya.
“Maimakon haka, mun taru don yin hidima, a matsayin masu bayar da shawara na wucin gadi ga Shugaban kasa ne, a matsayin masu wakiltar ra’ayoyi mabambanta a fadin tarayya, shi ya sa ba mu da karfin ikon da doka ta ba mu na samar da “sabon” kundin tsarin mulki ga Tarayyar Jamhuriyyar Najeriya,” za a iya samar da sabon kundin tsarin mulki ne kawai a majalisar da aka kafa.
A cewarsa, Sakatariyar taron ta bayyana a babi na bakwai a Littafi na farko, cewa “sabon kundin tsarin mulkin za a tabbatar da amfani da shi ne, ta hanyar kada kuri’ar raba gardama a daukacin fadin kasa, wanda za a gudanar don wannan manufa. Ya ce, nuni da kuri’ar raba gardama da Shugaba Jonathan ya yi a wajen kaddamar da taron kasar a ranar 17 ga Maris, al’amari ne da ba shi da tabbacin ma’ana, illa dai a yi ta hasashe, domin ta yiwu ya zama karin haske kafin Majalisar kasa ta gabatar da wani sashe na tanade-tanaden Kundin tsarin mulki da zai bayar da izinin kada kuri’ar raba gardama. “Muna nufin cewa, tunda akwai irin wannan hukuma (majalisar kasa), gabatar da irin wannan shirin tuni aka yi watsi da shi a Majalisar kasa.”
Manufar tazarce
Alhaji Ibrahim Comassie ya ce idan aka yi la’akari da juye-juyen da ake yi, a bayyane yake karara miyagu sun kutso kai cikin taron, wadanda manufarsu, su yi zagon kasa ga tsare-tsaren dimokuradiyya, sannan su jefa kasar nan cikin rikice-rikicen siyasa.
“daukacin manufar samar da “sabon kundin tsarin mulkin 2014” ga Najeriya, dabara ce da yunkurin da wadansu mutane suke yi domin su fake da hukuncin kotun daukaka kara na shekarar 2002, kamar yadda Mai Shari’a George Adesola Oguntade (a lokacin yana rike da mukamin), inda ya warware badakalar shari’ar tsakanin Ministan Shari’a na Tarayya da Jam’iyyar ANPP da wadansu (A.G., Fed da ANPP [2003] 15 NWLR (Pt 844).
“A lokacin da Gwamna Abubakar Audu na Jihar Kogi aka kalubalance shi kan cancantarsa ta tsayawa takara a karo na biyu cikin shekarar 2003, bayan wa’adin mulkinsa ya kare a cikin watan Mayun 2003.
“Abin takaddama a kai shi ne, an zabe shi a matsayin Gwamnan Jihar Kogi a tsakanin shekarar 1991, kuma wa’adinsa na mulki shi ne, tsakanin 1991 zuwa 1993, al’amarin da aka dauka a matsayin wa’adin mulki karo na farko, sai kuma ya sake kafa gwamnati a tsakanin shekarun 1999 zuwa 2003, al’amarin da aka dauka a matsayin wa’adin mulki a karo na biyu. Idan an yi la’akari da wannan, za a iya hana shi sake tsayawa takarar wani wa’adin a shekarar 2003, domin yin hakan na nuni da saba wa kundin tsarin mulki da ya maye gurbin tsarin da ake amfani da shi., wanda ya tanadi cewa za a iya zaben mutum a matsayin gwamna sau biyu ne kawai, ba tare da wani kari ba.
“A hukuncin da aka yanke, Kotun daukaka kara ta tabatar da cancantar Gwamna Abubakar Audu na Jihar Kogi ya sake tsayawa takarar gwamna, bisa la’akari da cewa wa’adin mulkinsa karo na farko (shekarun 1991 zuwa 1993), an gudanar da shi ne a bisa wani tsarin kundin mulki na daban (wato CFRN 1989), alhali a halin yanzu ana amfani da Kundin Tsarin mulki na shekarar 1999 ne, wanda shi sabon kundin tsarin mulki ne,” inji shi.
Coomassie ya ce a ra’ayin kungiyar NDF, yin amfani da sabon kundin tsarin mulki wata dabara ce ta bai wa masu rike da mukaman gwamnati, wadanda aka haramta musu yin tazarce a karo na uku, a matakan Tarayya da Jihohi, su sake tsayawa takarar mukamansu, ta hanyar fakewa da sabon kundin tsarin mulki.
“Wannan al’amari na da wata illa wajen tauye damar ’yan siyasa masu tasowa a daukacin jam’iyyun siyasa, tare da daukacin ’yan Najeriya da aka danne musu hakkinsu na yin zabin da suke bukata, kamar yadda yake kunshe a kundin tsarin mulkin.
“Idan ba a shawo kan al’amarin ba, manufar tazarce da wa’adin mulki karo na uku, kamar yadda aka so yi a da (shekarar 2005), na iya jefa Najeriya cikin wani mawuyacin hali na rikicin siyasa da ka iya tayar da hankula da keta doka,” a cewar Coomassie.
Wadanda suka halarci taron ’yan jaridar tare da Ibrahim Coomsassie, sun hada da tsohon ministan Babban Birnin Tarayya, kuma Shugaban Hadin gwiwa na kungiyar NDF, Jerry Useni da Iyorchia Ayu da Bashir dalhatu da Muktar Muhammad da Farfesa Awwalu Yadudu da Jonathan Temlong da sauransu.
Muhimman sauye-sauyen da ke sabon kundin tsarin mulki
Sabon kundin tsarin mulki na kunshe da sauye-sauye, wadanda aka amince da su a zaman muhawarar taron kasa kan rahotannin kwamiti a watannin Yuni da Yuli. Wadannan sauye-sauye sun hada da kirkiro sababbbin jihohi 18 da soke kananan hukumomi 774 da kirkiro ’yan sandan jihohi da tsayawa takarar zabe ba a karkashin jam’iyya ba, sannan an kayyade yawan ministoci zuwa 18.
Baya ga soke kananan hukumomi 774, sabon kundin ya bayar da karfin iko ga jihohi da su kirkiri kananan hukumominsu, tare da tsarin gudanar da su. Sababbin jihohi 18 su ne: Aba da Adada da Amana da Anioma da Apa da Edu da Ekiti da Ghari da Gurara da Ijebu da Kainji da Katagum da New Oyo da Njaba-Anim da Ogoja da Oil Ribas da Ose da Sabannah.
An bai wa wakilai kwanaki bakwai su yi nazarin sabon kundi da aka raba musu, sannan su sake taruwa don tattaunawa a kai.
A ranar 14 ga Yulin bana, aka dakatar da zaman taron, inda aka bukaci sakatariyar taron ta tattara al’amura 20 da aka amince da su a karkashin ayyukan kwamitoci 20 da suka bayar da rahoto. Sakatariyar taron ta wuce gona da iri, domin ta yi nuni da cewa rahotannin taron za a yi amfani da su ne wajen samar da sabon kundin tsarin mulki ga kasar nan.