Yadda muka ceto yaran da aka sato daga Jos – ’Yan Arewa a Legas
A ranar Alhamis din makon jiya ce Rundunar ’Yan sandan Jihar Legas ta yi nasarar kama wata mata da take dauke da wadansu yara biyu da ake zargin an sato su ne daga Jihar Filato lokacin da matar ke kokarin safarar yaran zuwa garin Anacha a Jihar Anambra. ’Yan Arewa da ke hada-hada a Kasuwar Duniya […]
A ranar Alhamis din makon jiya ce Rundunar ’Yan sandan Jihar Legas ta yi nasarar kama wata mata da take dauke da wadansu yara biyu da ake zargin an sato su ne daga Jihar Filato lokacin da matar ke kokarin safarar yaran zuwa garin Anacha a Jihar Anambra.
’Yan Arewa da ke hada-hada a Kasuwar Duniya ta Alaba ce suka yi sanadin kama matar tare da ceto rayuwar yaran biyu. Alhaji Muhammadu Buba mai magana da yawun Kungiyar ’Yan Kasuwar Alaba shi ne ya ankarar da ’yan sandan har suka kai ga kama matar, shi ne kuma wanda ya dauki hoton matar da na yaran, hotunan da suka karade kafafen sada zumunta kuma da yawa daga jaridun kasar nan suka yi amfani da su. Ya shaida wa Aminiya cewa abokinsu mai suna Malam Jamilu Injiniya ne ya gano matar ta hau babur mai kafa uku da yaran a yankin Ajangbadi, bayan ya lura yaran na sanye da kayan Hausawa ne a wannan lokaci ya kuma tabbatar da matar kabilar Ibo ce. Sai ya yi sauri ya hau babur dmai kafa uku ya zauna a gefen yaran, a haka sai ya fara yi wa yaran magana da Hausa, yaran na kallonsa, suna kallon matar daga nan ya tabbatar da yaran Hausawa ne, nan ya yi shiru ya kame bakinsa har suka zo tashar motoci ta ‘Chemis Bus Stop’ da ke cikin Kasuwar Duniya ta Alabar Rago, dama wajen tashar motoci ne da ke safarar zuwa garuruwan Ibo. A haka Jamilu ya ci gaba da bin matar tana tafe da yaran har ta shiga cikin tashar, ko da ta kula yana biye da ita ce sai ta yi wa Manajan tashar bayanin cewa, wani mutum na biye da ita,” inji shi.
Ya ce “Sai Manajan ya yi masa magana sai ya fada masa ba matar yake bi ba, daga nan ya samu waje a gefen tashar ya tsaya ta yadda matar ba ta ganinsa, amma yana hangen duk halin da ake ciki, can sai ya ga yadda matar ta sayi riguna iri biyu ta dawo ta canja wa yaran, kayan da ta sauya musu a tashar su ne kayan da suke sanye da su a hotunansu.
Da su aka yi ta turawa a kafafen sada zumunta, ko da ya ga ta sauya musu kayan sai ya tabbatar da manufarta nan da nan sai ya kira Wazirin Sarkin Hausawa da ke kasuwar ta waya ya kuma kira wadansu ’yan Arewa da dama da ke yankin.
Ya ce “Wazirin Sarkin Hausawan, shi ya kira ni a waya ya shaida min halin da ake cike sannan ya umarce ni da in je wajen kasancewar rumfata na kusa da tashar, nan da nan na nufi wajen ko da na je wajen na iske matar da yaran biyu, sai na kira Baturen ’Yan sandan yankin na shaida masa halin da ake ciki na bukaci ya turo ’yan sanda. Haka aka yi lokaci kadan sai ga su sun iso dauke da makamai sai muka yi dabara tare da ’yan sandan muka kewaye matar. Ganin ’yan sandan nan da nan ta ba da kai, ta ce za ta fadi gaskiyar lamari.”
Ya ce ta ce mijinta ne ya kawo mata yaran daga Jihar Filato a ranar Laraba da daddare ganin yaran ’yan Arewa ne ba ta saki jiki da su ba shi ne za ta mayar da su Anaca wurin mijinta. Ya ce da aka tambaye ta cewa mijinta ba yana Legas ba? Sai ta ce, za ta kai yaran Anacha ne wajen mijinta, nan da nan aka tabbatar da ba ta da gaskiya sai aka tafi da ita ofishin ’yan sandan yankin. Ya ce “A nan ni da Jamilu muka shigar da bayananmu a rubuce sai na dauki hoton matar da na yaran na tura a kafafen sada zumunta domin sanar da jama’a halin da ake ciki ko Allah zai sa sakon ya riski iyayen yaran.”
Ya ce, a yanzu ’yan Arewa mazauna Legas musamman a yankin Kasuwar Alaba sun farga kuma suna sanya ido sosai tun sanar da labarin satar yaran Arewa da wasu batagari ke yi suna kai su jihohin Ibo ana sayar da su. Ya ce a watan da ya gabata ma an sace ’yar wani abokinsu mai suna Walida wacce daga baya aka gano sassan jikinta a wani kango da ke yankin, “Wannan ma yana cikin abin da ya sanya al’ummarmu suka tashi tsaye domin sanya idanu, yanzu haka kowace tashar mota a wannan yankin namu musamman zuwa jihohin Kudu maso Gabas muna da ’yan sa-kai da ke sanya idanu,” inji Buba.