Yadda muka fara jaridar Trust shekaru 20 da suka wuce-Kabiru Yusuf

  Shugaban Kamfanin, Malam Kabiru Yusuf ya ce kamfanin Media Trust mai buga jaridun Daily Trust da Aminiya zai gudanar da kasaitaccen bikin cika shekarar 20 don ya yi waiwaye adon tafiya tare da hangen gaba.   Malam Yusuf ya bayyana haka ne yayin da yake yi wa manyan editocin kamfanin karin haske kan bikin […]

Yadda muka fara jaridar Trust shekaru 20 da suka wuce-Kabiru Yusuf

 
Shugaban Kamfanin, Malam Kabiru Yusuf ya ce kamfanin Media Trust mai buga jaridun Daily Trust da Aminiya zai gudanar da kasaitaccen bikin cika shekarar 20 don ya yi waiwaye adon tafiya tare da hangen gaba.
 
Malam Yusuf ya bayyana haka ne yayin da yake yi wa manyan editocin kamfanin karin haske kan bikin wanda za a gudanr mako mai zuwa.
 
Ya bayyana cewa kamfanin ya fara da jaridar mako-mako ta Weekly Trust saboda “Muna son aiki kuma mun yi kokarin samar da shi sannan a yanzu mun kai shekaru 20”.
 
Shugaban kamfanin wanda ya bayyana tarihin yadda kamfanin ya fara sauran jaridun ya ce  kamfanin ya fara ne a daki daya a garin Kaduna da jaridar mako ta Weekly Trust wacce ake bugawa a ranar Juma’a.