‘Yadda muka fara shirye-shiryen aikin Hajji da kafar dama’

Hukumar Alhazai ta Jihar Katsina ta ce an fara shirye-shiryen Hajjin bana da kafar dama.

‘Yadda muka fara shirye-shiryen aikin Hajji da kafar dama’

Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Katsina ta ce dukkan alamu sun nuna cewar shirye-shiryenta na aikin Hajjin 2021 ta fara su da kafar dama.

Babban Daraktan Hukumar, Suleiman Nuhu Kuki ya ce, “Babbar nasarar da muka fara samu ita ce, daga cikin maniyyatan da suka biya kudadensu na aikin Hajjin 2020 wanda Allah Bai ba da damar aka yi ba saboda bullar cutar coronavirus, ana iya cewa bai wuce kashi daya bisa uku ba ne suka karbi kudadensu.

“Amma saura duk sun yi hakuri sun bar su duk kuwa da halin tattalin arzikin da ake fuskanta. Ka ga wannan wata nasara ce wadda za mu iya cewar mun fara samu kuma da kafar dama.

“Sannan akwai batun adashin gata da aka bullo da shi, bayan an bayar da umarni daga NAHCON cewa a ci gaba da karba; Mu a nan Jihar Katsina mun fara wayar da kan jama’a a kan muhimmaci da kuma yadda za’a rika yin zubin wannan adashe daga maniyaci, kuma Alhamdulillahi, ana samun cigaba a kan wannan.

“Kuma har zuwa wannan lokacin babu wani korafi da muka samu. Maniyata na ci gaba da biya, kuma muna yawan samun kyakkyawan rahoto daga wakilanmu da ke shiyoyinmu da ke cikin Jihar”, kamar yadda bayyana a hirarsa da Aminiya kan shirye-shiryen aikin Hajjin da ke kara matsowa.

Game da yin allurar rikafin cutar coronavirus da kasar Saudiyya ta ce babu wani maniyacin ta zai yi aikin Umra ko Hajjin face an yi mashi wannan allurar, “Mu a nan Jihar Katsina mun fara yi wa maniyatan da suka biya kudin su baki daya, ko ajiye wani sashe na kudin don kada a bar mu a baya.

“Maigirma Gwamna Aminu Masari ya tanadar wa Hukumar da wadatattar allurar da za a yi wa duk wani maniyyaci daga Jihar a kashi na farko da kuma na biyu”.

Ya kara yin kira ga maniyyatan da ba su yi karbi allura rigakafin ba da su yi hanzarin zuwa ofisoshin Hukumar da ake yi domin a yi musu.

Sannan wadanda ba su cika kudadensu ba da su kokarta su ci gaba da biya har zuwa lokacin da gwamnati ya da kayyade kujera a ban.

Ya ce, inda aka kara gode wa Allah shi ne yanzu batun yin biza ba sai an dauki wani lokaci ba, saboda yadda aka saukaka komai.