Yadda muka gano gawar ’yarmu da aka kashe –KakartaYadda muka gano gawar ’yarmu da aka kashe –Kakarta

Asirin wasu masu satar mutane suna kashewa a garin Jos,     babban birnin Jihar Filato ya tonu, bayan da suka sace wata yarinya ’yar shekara tara mai suna Ummi Salma Abdullahi a Unguwar Filin Sukuwa da ke garin Jos suka kashe ta, a karshen makon jiya.Da take yi wa wakilinmu bayani kan yadda al’amarin ya faru, […]

Yadda muka gano gawar ’yarmu da aka kashe –KakartaYadda muka gano gawar ’yarmu da aka kashe –Kakarta

Asirin wasu masu satar mutane suna kashewa a garin Jos,     babban birnin Jihar Filato ya tonu, bayan da suka sace wata yarinya ’yar shekara tara mai suna Ummi Salma Abdullahi a Unguwar Filin Sukuwa da ke garin Jos suka kashe ta, a karshen makon jiya.
Da take yi wa wakilinmu bayani kan yadda al’amarin ya faru, kakar yarinyar Hajiya Hasiya Umar ta ce “A ranar Alhamis bayan mun gama kalaci da misalin karfe bakwai da rabi na safe, sai na ba ta kudi na ce ta je ta sayo mana masa. Da aka yi kamar minti 15 ban gan ta ba, sai na ce da yayarta ta tashi ta je wurin mai masar ta ce idan ba a ba yarinyar masar ba ta dawo gida.”
Hajiya Hasiya ta ce da yayar ta je ta tambayi mai masa sai ta ce mata da ta zo ba ta kai minti biyar ba ta zuba mata ta tafi. Ta ce akwai wani da ake kira Auwalu a unguwar, yarinyar tana fitowa sai ya karbi masar da aka aike ta da ita. Ya ba ta kwanonsa ya ce ta je ta sayo masa masar, da ta sayo masar ta fito daga gidan mai masar shi ne ba a gan ta ba.
Ta ce sai yayar ta zo ta ce Auwalu ya aike ta, “Ni kuma na tashi na je na samu Auwalu yana wanki yana waka, na ce masa ina Ummi Salma? Sai ya ce min yau kwana uku ke nan bai gan ta ba. Na ce an ce kai ne ka aike ta ta sayo maka masa, ya ce shi bai aike ta ba. Na ce mu je wurin mai masar da muka je mai masar ta ce yarinyar ta zo da kwanonka nan,” inji ta.
Kakar ta ci gaba da cewa “Sai na ce mu je ka nuna mini kwanonka da aka san kana amfani da shi da muka je sai ya dauko wata roba ya ce shi ne kwanonsa. Sai na koma wurin mai masa na ce mata wannan shi ne kwanon nasa? Sai ta ce ba shi ne ba. Na koma na ce an ce ba shi ne kwanonka ba. Sai ya ce ya tuna jiya ya ba wasu yara masu talla kwanonsa.”
Hajiya Hasiya ta kara da cewa, “Sai na nuna raina ya baci, na tafi don in kira ’yan uwan mahaifnta, sai wadansu masu aikin gini suka tare ni, suka ce sun ga Auwalu tare da yarinyar nan don haka in tuhume shi.”
Ta ce sai jama’a suka taru suka kama dukansa, sai ya ce “Yarinyar tana kan dutsen da ke kusa da mu. Jama’a suka je suka duba amma ba a gan ta ba.” Ta ce da ya ji duka sai ya ce ba shi ne ba, wani ne da ake kira Nafi’u shi ne ya aiki yarinyar. Ta ce ba a gano yarinyar ba sai a ranar Juma’a da misalin karfe biyar na yamma, inda aka gano gawarta a cikin wani gida da ba a kammala ba da ke kusa da inda ake sayar da masar. Ta ce an gano gawarta a cikin wani rami a wannan gida an nade ta da leda.Hajiya Hasiya UmaruShi ma da yake zantawa da wakilinmu, mai unguwar Filin Sukuwa da ke Jos, Malam Muhammadu Mai Unguwa ya ce ba su ji dadin faruwar wannan al’amari ba, ya ce a yanzu sun dauki matakan tsare unguwar.  Ya yi kira ga gwamnati kan ta hukumta mutanen da ake zargin.
Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Filato, DSP Felicia Anslem ta shaida wa wakilinmu cewa da farko sun samu labarin bacewar wata yarinya mai suna Ummi Salma Abdullahi da ke unguwar Filin Sukuwa. Ta ce daga baya an gano gawar yarinyar a wani gida da ake ginawa. Ta ce an kama Auwalu Sani da Nafi’u Usman da ake zargi kan wannan al’amari kuma su ne suka nuna wannan gida da aka gano gawar yarinyar.
Ta ce sun tabbatar da bakinsu cewa su ne suka kashe yarinyar kuma sun ce wani mai suna Alhaji Aminu Sale ne ya ba su Naira dubu 300 don su samo masa sassan jikin mutum. Ta ce a yanzu dai suna tsare da mutum hudu kan lamarin. Kuma  ana ci gaba da bincike a sashin binciken aikata manya laifuffuka na rundunar, ya ce da zarar an kammala za a gurfanar da su a gaban kotu.