Yadda muka gano sabuwar hanyar gane ’yan kunar bakin wake – Jami’an tsaro
Hukumomin tsaro da ke fafatawa da mayakan kungiyar nan masu tada kayar baya da aka fi sani da Boko Haram a Jihar Barno, sun gano wata hanya mafi sauki ta gane maza da mata ‘yan kunar bakin wake a jihar.Wadansu daga cikin jami’an tsaron da suka tattauna da wakilinmu amma suka nemi ya sakaye sunayensu […]

Hukumomin tsaro da ke fafatawa da mayakan kungiyar nan masu tada kayar baya da aka fi sani da Boko Haram a Jihar Barno, sun gano wata hanya mafi sauki ta gane maza da mata ‘yan kunar bakin wake a jihar.
Wadansu daga cikin jami’an tsaron da suka tattauna da wakilinmu amma suka nemi ya sakaye sunayensu domin ba su da iznin hira da manema labarai, sun bayyana cewa fiye da kashi 90 na mata masu kai harin kunar bakin wake a jihar ‘yan mata ne wadanda shekarunsu ba su haura 13 zuwa 23 ba.
daya daga cikin hafsoshin ya ce, “Duk yarinyar da aka shirya za ta kai harin kunar bakin wake za ka ga kanta babu kitso, za ta kwance gashin kanta ta mai da shi baya ta daure. Ba mu taba ganin gawar ‘yar kunan bakin wake wacce kanta ke da kitso ba. Duk sai sun kwance gashin kansu, sun tsefe shi, sun daure shi ta baya kafin su kai harin.’’
Ya ci gaba da cewa,“Ba zan iya sanin ko wannan yana da nasaba da wani asiri ne ko tsafi ba, amma dai haka suke yi. Idan ka tuna, mata uku aka shirya za su kai harin kunar bakin wake a sansanin ‘yan gudun hijira da ke Dikwa. Biyu suka kai harin, a inda suka mutu tare da mutanen da suka kashe. Sojoji suka kama guda daga ciki. Ita gudar da muka kama ai tana gudu ne tare da sauran jama’a sai gelen da ta rufe kanta ya fadi muka ga kanta babu kitso kuma ta mayar da gashinta baya ta daure ya sa muka kama ta.’’
“Da muka yi mata tambayoyi ta ce lallai tana cikin maharani, sai dai ba ta shirya tada nata bam din ba ne domin ta san iyayenta suna cikin wannan sansanin, kuma ba ta son kasha su.’’
Su kuma maza daga bayan hannunsu, wato daga wuyar hannun zuwa gwiwar hannun muke gane su.
“Ka san akwai wani irin horo da sojoji ke yi da ake jan jiki a kasa, wani lokaci ma a karaashin waya mai suka. Su ma suna yin irinsa. Amma da yake ba su san yadda ake yi ba sai su yi ta gurje hannayensu, a karshe har su ji ciwo. Za ka ga wurin ya yi baki kirin, fatar ta mace ta yi tabo mai kauri. Su ma ta haka muke gane su,” inji wannan majiyar.
Shugaban hukumar bayar da tallafin gaggawa ta Jihar Barno (SEMA), Injiniya Satomi Alhaji Ahmed, wanda ya tabbatar da gaskiyar hakan, ya kara da cewa, tsefe gashi da mai da shi baya a daure da mata ‘yan kunar bakin wake suke yi al’ada ce ta kabilar Kanuri da suke yi wa matan da suka mutu kafin a binne su.
Injiniya Ahmed ya kara da cewa, “A bisa al’adarmu ta Kanuri, idan mace ta rasu ba za mu binne ta da kitso a kanta ba. Dole sai an kwance kitson, an tsefe kan kuma a maida gashi baya a daure kafin a binne ta. Manufar yin haka da mata ‘yan kunar bakin wake sukeyi shi ne, da zarar an yi musu haka, to sun yi shirin mutuwa ke nan ba, dawowa za su yi ba.’’
“Wannan zai tabbatar maka da cewa duk wacce ta fita da niyyar ta’addanci irin na kunar bakin wake to da shirinta ta fita, kuma ta san abin da za ta je ta yi. Babban abin mamaki shi ne, da dama daga cikinsu suna samun damar da za su jefar da bam dinsu su mika wuya ga hukuma, amma sai ka ga yin haka yana yi musu wuya,” inji Injiniya Ahmed.