Yadda muka gano sundukan Taramadol 40 – Kwanturolan Kwastam
Kwamandan Hukumar Kwastam ta Apapa a Legas, Kwanturola Bashir Abubakar, ya yi karin haske a kan kin karbar na-goro da jami’ansa suka yi karba domin sakin sundukai 40 dauke da kwayoyin Taramadol da jirage 2 masu saukar ungulu da kudinsu ya kai Naira biliyan 7 da miliyan 138 da hukumar ta kama kwanan baya. A […]
Kwamandan Hukumar Kwastam ta Apapa a Legas, Kwanturola Bashir Abubakar, ya yi karin haske a kan kin karbar na-goro da jami’ansa suka yi karba domin sakin sundukai 40 dauke da kwayoyin Taramadol da jirage 2 masu saukar ungulu da kudinsu ya kai Naira biliyan 7 da miliyan 138 da hukumar ta kama kwanan baya. A yayin zantawa da Aminiya, Kwamandan ya ce, an yi wa jami’ansu tayin toshiyar baki ta Naira miliyan 150 a kan kowane sunduki:
Wane karin haske za ka yi a kan wannan al’amari?
Da farko dai zan gaya maka cewa, mun kama sundukai 40 da ke cike da miyagun kwayoyi da jirage 2 masu saukar ungulu a cikin sundukan wadanda duka karfinsu ya fi karfin abin da kasa ta yarda a shigo da shi. An shigo da kwayoyin ne daga kasar Indiya yayin da aka shigo da jiragen daga kasar Amurka. Kuma a dalilin wannan kame mun kama mutum uku da suka hada da biyu da suka mallaki kayan da wani jami’in Kwastam guda daya. Mun samu nasarar kamen ne da taimakon Allah da kwarewar aiki da yin amfani da na’urorin zamani wajen binciken kwakwaf da samun labaran sirri daga jami’anmu masu aiki a boye. Kuma a zaman aiki da na yi na wata 16 a hukumar a Onne da ke Fatakwal na taba kama irin wadannan sundukai guda 9. Hakan ne ya sa watanni biyu da fara aikina a Apapa, Legas, sai na fara mayar da hankali da sanya ido kan irin wadannan kwayoyi da gwamnati ta haramta shigo da su saboda illarsu.
Bayan kamen me ya biyo baya?
Bayan mun kama kayan, mun jinkirta don ganin wanda zai zo karbar kayan domin mu kama shi. Ashe mutanen da suka mallaki kayan sun zagaya suka tafi Abuja domin ganawa da shugabanmu na kasa, Kanar Hameed Ali a ofishinsa, suka nemi alfarma a hada su da mu domin a taimaka musu a saki kayan. Jarumtakarsa da kishin kasa da muke koyi da ita ce ya sa tun kafin su isa gare shi, ya riga ya samu labarin komai, musamman a kan irin mutanen da suka rika buga mana waya dangane da kayan. Ka ga bera ya kai kansa gidan kyanwa ke nan. Sai aka umarci su dawo gare mu domin sanin abin yi.
Bayan sun dawo daga Abuja ne suka zo gare mu inda na tura jami’aina tare da jami’anmu masu leken asiri a boye suka tattauna da su a wani otal da muka makala kyamarar daukar hotunan bidiyo da muryoyi ba tare da saninsu ba. Kuma mun nemi su tura mana sakonni ta wayar salula domin tabbatar da shaida a kan bukatarsu. An yi kamar wata daya muna yi musu shigo-shigo ba zurfi a wannan tattaunawa, inda suka yi alkawarin bayar da Naira miliyan 150 a kan kowane sunduki. Idan ka tara Naira 150 sau 40 zai ba ka jimlar Naira biliyan 6 ke nan. Bayan sun bayar da Naira miliyan 150 kudin sunduki daya sun nemi mu fara sakin daya daga cikin sundukan domin tabbatar da gaskiyar cewa za a sakar musu sauran kayan. Bayan mun amince da bukatarsu mun saki sunduki daya ne muka kama biyu daga cikinsu da wani jami’inmu da ake zargin ya hada baki da su wajen odar kayan.
A yanzu da zaben kasa ke gabatowa. Wane mataki kuka dauka domin dakile miyagun kwayoyi da makamai?
Tashi tsaye da na yi wajen ganin an kyautata tsaro a hukumar Onne da ke Fatakwal ne ya kai ga kame irin wadannan sundukai masu dauke da bindigogi da alburusai da yunifom din sojoji. Yanzu da na fara aiki a nan Apapa, daya daga cikin dokokin da na bayar ga dukan jami’ai fiye da 600 da ke aiki a karkashina shi ne, kafin kowane kaya ya fita dole ne a bude kowane sunduki a zazzage kayan da ke cikinsa domin gane abubuwan da suke ciki. Kuma kowane katan sai an bude shi. Masu tunanin shigo da irin wadannan miyagun kaya yanzu sun gudu sun bar wurin da nake aiki. Wannan yana taimaka mana kwarai da gaske a kan ayyukan da muke yi a bangaren tsaro. Kuma a lokacina, ba zan taba yarda wadansu mutane su cin karensu ba babbaka ta fannin yi wa tattalin arzikin Najeriya zagon kasa ba. Zan sa ido wajen yin aiki ba sani ba sabo domin samar da kudaden shiga da za su bunkasa tattalin arzikin kasa. Yawancin kamfanoni da masana’antu masu zaman kansu da ke gudanar da al’amuransu bisa gaskiya sun fi jin dadin aiki a wurin da nake jagoranci saboda na sanya dokoki masu yawa a kan matakan tantance kayan da suka yi oda daga waje da kudaden shiga da suke biya cikin aljihun gwamnati. To ka ga idan aka ce sai an bude kayan da ka shigo da su cikin kasa to za ka ji tsoron shigo da irin wadannan abubuwa.