Yadda muka gudanar da kasuwanci a fagen yakin basasa – Malam Abdullahi
Malam Abdullahi Muhammad dattijo ne dan kasuwa da ke sayar da kayayyakin masarufi a kan Titin Bank Road, Kaduna. A zantawarsa da wakilinmu, ya bayyana yadda ya fara kasuwanci kimanin shekara 50 da suka wuce da kuma yadda ya tafi bakin daga tare da sojojin Najeriya, lokacin yakin basasar kasar nan. Ga yadda hirar ta […]

Malam Abdullahi Muhammad dattijo ne dan kasuwa da ke sayar da kayayyakin masarufi a kan Titin Bank Road, Kaduna. A zantawarsa da wakilinmu, ya bayyana yadda ya fara kasuwanci kimanin shekara 50 da suka wuce da kuma yadda ya tafi bakin daga tare da sojojin Najeriya, lokacin yakin basasar kasar nan. Ga yadda hirar ta kasance:
Za mu fara da tarihinka a takaice?
Malam Abdullahi: Assalamu alaikum, sunana Abdullahi Muhammad. An haife ni a garin kiru da ke cikin jihar Kano kinamin shekara 80 da suka wuce. Iyayena sun sanya ni makarantar addini kamar yadda ake wa kowane yaro. Daga bisani da na dan kara girma sai na fara zuwa gona don tayasu aikace-aikace. A shekarar 1959 ne kuma sai na dawo garin Kaduna, inda na fara kasuwancin sayar da kayayyakin masarufi kamar su lemun kwalba da sauran kayayyakin bukatar yau da kullum. Kafin shekaruna su ja, idan na tashi daga shagon nan da marece, ina wuce wa ne unguwar Sarki nan gaban gidan Sarki Musulmi. Inda na baje kayayyakina a tire, ina hira da abokai, ina kuma kasuwancina. Ka ga riba biyu kenan. A gaskiya na dade a wajen nan ina harkokin kasuwanci. Wannan ya sa akwai mutane da dama da suke mamaki idan suka ga har yanzu ina wannan wuri, amma wannan ikone na Ubangiji.
Yaya za ka kwatanta kasuwancinka a da da kuma yanzu?
A gaskiya abubuwa suna canzawa, saboda a wancan lokaci duniya tana kwance ne. Ba za ka hada irin rikon amanar mutanen da ba da na yanzu. Misalin irin zaman lafiyar da akwai a wanacan lokacin, babu a yanzu. Maganar gaskiya mutum ba za a ce ya yi kuskure ba, idan ya ce komai ya canza.
Wadanne kalubale ne za ka ce ka fuskanta a rayuwarka?
Akwai amma wannan ba kalubale ba ne da ya shafi ni kadai ba, shi ne abubuwan da suka biyo bayan kisan Sardaunan Sakkwato Sa Ahmadu Bello. A lokacin muna unguwar Shanu ne, aka hana kowa zirga-zirgar kamar yadda aka saba. A gaskiya wannan ranar tana tsaya min a raina a koyaushe saboda irin girman rashin da kasar nan ta yi a wannan rana.
Wadanne garuruwa ka taba ziyarta?
Ni mutum ne da bai cika tafiye-tafiye ba sosai, amma akwai tafiyar da muka yi garin Umuahiya da ke cikin jihar Abiya ta yanzu, wato lokacin yakin basasar kasar nan wadda ba zan manta da ita ba. A lokacin mun tafi ne cikin tawagar sojojin Najeriya da ke yakar ’yan tawayen Biyafara. Amma ba mun je ne a matsayin soja ba. Mun je ne a matsayin ’yan kasuwa fararen hula a kungiyance da aikinmu shi ne samar wa sojojin kasar kayyakin bukata lokacin yakin. Akalla mun kai mu 20, kuma sai da aka tantancemu kafin tafiyar.
Wani abu da ba zan manta da shi ba a lokacin da muke can, shi ne wata rana da ’yan tawayen Biyafara suka kai mana hari a wani gari da sojinmu ba su dade da ’yantarwa ba, mai suna Ogu, inda harin ya kashe ’yan kasuwanmu da dama amma mu mun yi sa’a harin bai same mu ba, saboda a lokacin muna cikin wani rami. Kodayake da ma sojojinmu sun sha gargadinmu da mu daina kunna fitila idan dare ya yi, kuma a wannan daren wasu daga cikin ’yan kasuwanmu sai suka yi hakan. Wannan ya sa sojojin abokan gaba suka fahimci cewa akwai mutane a wajen a wurin, hakan kuma ya sa suka aiko da farmaki ta sama.
Wadanne irin kayayyaki kuke sayarwa sojojin a lokacin yaki?
Akwai goro da agoguna da takalma da man goge takalmi na Kiwi. Har ila yau, akwai kuma kayyakin abinci kamar su kifin gwangwani na Geisha da dai sauransu. Bayan mu kuma akwai wadansu mata wadanda aikinsu aikinsu shi ne girka wa sojojin abincin da za su ci a lokacin yakin. Mun kwashe kimanin wata uku bayan kawo karshen yakin, daga nan muka dawo Kaduna. Ko da isata ban bata wani lokaci ba na wuce shagona, na ci gaba da kasuwancina kamar yadda na saba kafin fara yakin.
Ya ya kake ji a yanzu idan ka ji wasu na kiraye-kirayen a raba wannan kasar?
Bana jin dadi kuma a gaskiya ba su san abun da suke fadi ba. Saboda idan an yi yadda suke so, ta ya ya za su rayu? Shi ya sa raba kasar nan bai da amfani kuma masu kiraye-kirayen ya kamata su gane haka. Raba kasar nan ba shi ne zai warware mana matsalolinmu ba.
Allah ya kiyaye idan a yanzu aka bukaci ka sake raka sojin Najeriya fagen daga, za ka yi?
A’a, ina?, ba zan bi su ba. Ai ko garin Lakwaja ba zan iya raka su ba.
Wace fa’ida ka samu a wannan sana’ar?
Babbar nasarar ita ce na samu na horor da wadansu wannnan sana’ar, wadanda za su kai mutum 20 kuma sun samu ci gaba sosai daga gareta. Har ila yau, ina alfahari da cewa na ba da tawa gudunmuwar lokacin yakin basasar kasar nan don ganin Najeriya ta zama daya.
Kana da wani buri?
Bani da wani buri da ya wuce fatan cika wa da kyau da imani. Kuma da wannan zan yi kira ga al’ummarmu da su tashi tsaye don yin sana’a saboda zaman kashe wando ba ya kawo ci gaba, sai ci baya.
Batun iyali fa?
Ina da mata daya da ’ya’ya biyar, biyu maza, uku mata. daya daga ciki dan sanda ne, guda kuma ma’aikacin gwamnati ne.