Yadda muka gudanar da siyasa lokacin neman mulkin kai – Isyaku Ibrahim
Wace gwagwramayar kuka yi aka kai ga samun ’yancin kan Najeriya a 1960? Ni dan asalin kasar Wamba ce da ke cikin Jihar Nasarawa ta yanzu. Manyanmu wadanda suka yi yakin da ya kai ga samun mulkin kai ’yan Arewa jarumai sun hada da Malam Sa’adu Zungur da Sa Ahmadu Bello Sardauna Sakkwato da Sa […]
Wace gwagwramayar kuka yi aka kai ga samun ’yancin kan Najeriya a 1960?
Ni dan asalin kasar Wamba ce da ke cikin Jihar Nasarawa ta yanzu. Manyanmu wadanda suka yi yakin da ya kai ga samun mulkin kai ’yan Arewa jarumai sun hada da Malam Sa’adu Zungur da Sa Ahmadu Bello Sardauna Sakkwato da Sa Abubakar Tafawa balewa da Aliyu Makaman Bida da Malam Aminu Kano da J.S. Tarka da Dabid Lot da Patrick Dokot da Abubakar Zugoji da Inuwa Wada da Baba Ribadu da Zanna Bukar Dipcharima da Sa Kashim Ibrahim da Alhaji Shehu Shagari da Maitama Sule da Waziri Ibrahim da sauransu.
Wane ne mai gidanka a siyasa?
Ni dan NEPU ne ta Malam Aminu Kano. Ana ta maganar cewa a samu ’yanci, wato mulkin kai a Najeriya. A wancan gwagwarmaya na neman mulkin kai, kasa ta zama ta ’yan kasa, za a samu komai bisa kan tsari da wadata, kasa za ta samu alfarma, a bai wa mutane ilimi da kokarin kawar da talauci da kuntatawa ta yadda mutane za su samu kyautatuwar rayuwarsu.
Su wane ne jagororin Kudu?
A Kudancin Najeriya Herbert Macauley ne shugaban jam’iyya da Nnamdi Azikiwe a matsayin Sakatare-Janar, su suka yi jagorancin jam’iyyarsu ta NCNC don tattauna mulkin kai a lokacin mulkin Turawa da sauran jam’iyyu kamar Action Group ta Obafemi Awolowo, lokacin Sa Richard ne Gwamna-Janar na mulkin Turawa. A 1948 aka je taron tsara tsarin mulki, abubuwan da suke so su kawo mana aka samu baraka, sai manyanmu suka ce ba su yarda ba. Da aka dawo gida sai NCNC a karkashin Herbert Macauley suka soma zaga Najeriya cewa ba su yarda da ka’idojin masu mulkin mallaka suke yi ba. Don haka suna son a tara kudi wanda za a kai kara ko a je Ingila a ce ba a yarda ba. Ana haka sai suke je Kano, ana dawowa sai Herbert Macauley ya mutu a jirgin kasa a tsakanin Kano zuwa Legas. Sai aka zo aka yi taro aka zabi Azikiwe ya zama shugaban Jam’iyyar NCNC a 1948. Sai aka yi taro a Kaduna a nan ne sai aka zabi Malam Sa’adu Zungur dan Arewa daga Bauchi kuma dan ajin su Sa Abubakar Tafawa balewa amma dan Kwalejin Katsina ne a matsayin Sakatare Janar na NCNC, shi kuma Azikiwe shi ne shugaba. Da Sa’adu Zungur ya kamu da rashin lafiya, sai ya koma gida, daga baya Allah Ya yi masa rasuwa.
Me kake ji game da sanayyarka da su Aminu Kano da Sardauna da Azikiwe da Awolowo da Tafawa balewa da sauransu?
Allah Ya yi min arzikin tun ina yaro, na samu karbuwa a wurin manyanmu inda na zama Sakatare na NEPU a Ibadan daga nan na zama Sakataren NEPU na Yammacin kasar nan. A 1959 sai Babban Sakataren NCNC Macullen ya aika in same shi a Legas, sai ya ce zan je Warri domin Azikiwe zai soma rajistar kamfe don a wayar wa mutane kai, saboda zaben 1959, zabe ne muhimmi domin samun mulkin kan kasa. Ya ba ni takarda na je na bayar aka kai wa Zik, sannan ya gan ni. Muka je Sapele aka yi kamfe a filin kwallon Warri. Washegari ya gaya wa Dokta M.I. Okpara yana Ministan Gona kuma shi ne Shugaban Kwamitin Kamfe, ya ce a sa ni a cikin wadanda za su yi kamfe.
Me ya sa NCNC ta sa ka a kamfe duk da kai dan NEPU ne?
Mun isa Kaduna, kuma washegari za mu je Zariya sai Zik ya ce ba zan bi su ba, za a sa ni a jirgin kasa in je Enugu akwai abin da zan yi. Lokacin Mbazulike Ameachi shi ne Sakataren Tsare-Tsare na Kudu maso Gabas ya zo tasha ya dauke ni muke je gidansa, ya ba ni masauki na samu ruwa na yi sallolina muka ci abinci. Washegari da safe muka je Sakatariyar NCNC ya ba ni motoci shida da Fam 350 ina ba su kudin mai. Ya ce in je in raba a Lardin Binuwai domin suna da yankuna biyar. Ya ce in dauki dafa-duka in raba baswaja biyar. Yanki na farko a wannan lardi shi ne na Idoma da Oturkpo da Tibi da Wukari. Na je garin Makurdi na wuce Katsina-Ala da Gboko, na ba da fam 50 kudin mai. Na wuce Wukari amma sai aka ce min Aku Uka na Wukari ya hana yin lacca. Da safe sai na tafi da ’yan jam’iya muka je fada muka yi gaisuwar ban girma, na ce da Sarki mun zo neman alfarma, ya ce na me, na ce na ji ka hana yin lacca amma ina neman izini, ba a gaya maka na hana lacca ba, na ce an gaya min, amma ina neman alfarma. Sarki ya ce mene ne dalilina, na ce zaben da za a yin don mulkin kai ne, mun ce mun fi ’yan Kudu yawa, in ba mu ilimantar da mutanenmu ba, mu ne za mu yi asara muna da yawa, amma in ba mu yi kamfe ba don wayar da kan jama’a dangane da NEPU da NPC da UMBC duk na mutanen Arewa ne muna da hakki mu gaya musu cewa wannan zaben zai kare mana mutunci, domin Sarki mai jama’a ne. Sai ya ce wai ubangidanku Malam Aminu Kano abin da ya koya muku ke nan magana kamar Aku-Kuturu. Sai ya yi shiru ya ce za a ba ka izini amma in ka yi babatu ka ga turken dokin nan a nan za a daure ka. Na ce muna so mu bi doka kuma ban fito daga gidan da ake koya min haka ba. Na yi lacca aka cika na ba da mota a Wukari da Fam 45.
Me ya sa Sarkin Wukari ya ba ka izini yin lacca bayan ya hana?
Shi Sarki Aku Uka yana da mulki, kuma mazanjiya ne don ba ya son ya ji Arewa na da bangare kamar NEPU da NPC da UMBC, shi dai Arewa da Najeriya kawai yake son a yi wa aiki shi ya sa sai an tantance mutum kafin ya yi lacca a kasar Wukari.
Yaya kuke yin lacca da adawa a lokcin?
Bayan na kammala kamfe a Wukari zan koma Gboko, ina tafiya sai na ga motar UMBC mutumin mai suna Tun Gull ya tsayar da ni muka tsaya, ya ce na ji ka yi lacca, Aku Uka ya ba ka izini ne? Na ce ya ba ni. Sai ya ce kai daga ina kake, sai na ce daga Wamba nake sai ya tambayi sunana. Sai na ce Isyaku Ibrahim, sai ya ce da Ingilishi “You little rat.” Sai na ce don me ya ce min haka? Sai ya ce na zauna a gidanku ina “Jami’in Gandun Daji.” Sai na ce kai ne dan Tibi din nan. Ni ina yaro na san shi ina shekara biyar zuwa shida sai aka tura ni karatun allo a Keffi, shi kuma an sama masa wuri ya gina gidansa. Ban sake ganinsa ba sai a wannan rana da muka hadu. Sai ya ce ka girma, ka yi karatu har ka zama dan siyasa, sai na ce eh. Na ce ni ne Sakataren NEPU na Yamma. Ya yi wa Babana addu’a. JS Tarka da Patrick Doksi da Dabid Lot su suka kafa UBMC, to amma Tarka kusan shi ne shugaba wanda ya zama Kwamishinan Sufuri, lokacin Gowon. Washegari shi yana lacca da baki kuma ni ma ina nawa da lasifika. Da yamma sai ya aika aka kira ni. Ya ce ban gan shi yana lacca ba, amma ni ma ina nawa? Sai na ce me ya hada ni da dan UMBC ni ina dan NEPU-NCNC Alliance, ya yi dariya, muka ci abinci.
Yaya aka yi Malam Aminu Kano ya yi juyin mulki ga Abba Maikwaru ya zama Shugaban Jam’iyar NEPU?
A kasar Lafiya wacce garin NEPU ne aka yi wannan juyin wainar, domin shi Malam Aminu Kano ya zama Shugaban NEPU. An dade ana kutungwuila a siyasa. Abba Maikwaru aka yi masa dabara aka tura shi Legas wai ya je wajen Action Group ko za a yi hadin gwiwa da su ko kuma da NCNC. Amma gaskiyanr abin shi ne da NCNC ake son a yi.
Wadanne irin motoci ne kake raba wa larduna don a yi kamfe?
Motar baswaja (da ake kira kunkuru). Na bayar a Lafiya, muka zo na ba da kudin na wuce Keffi da Nasarawa. Amma a Nasarawa ne muke da ’yan NEPU da yawa Keffi su ’yan NPC ne. Sai na wuce Nasarawa na ba su mota. Kullun akwai rigima tsakanin Keffi da Nasarawa, sai na ba su Fam Hamsin. karshen watan Fabrairu na kare wannan aiki na raba motoci na koma Enugu da ragowar Fam 17, sai Mbazulike Ameachi ya ce na mene ne? Sai na ce ragowar kudin ke nan. Sai ya yi dariya ya ce in rike. Aka zo za a soma kamfe sai Zik ya aika ya ce in zo Enugu. Washegari ya kaddamar da kamfe na neman zama Firayi Minista. Ranar 29 ga watan tara (Satumba) na 1959 a Asaba. Muka fara zaga manyan birane a Arewa muka je Ilorin da Bida da Zariya da Sakkwato da Katsina da Kano da Bauchi da Katagum/Azare da Gombe da Biu da Maiduguri da Mubi da Yola da Jimeta, lokacin ba gada sai dai a yi fito a kan kwale-kwale ko karamin jirgin ruwa a haye da motocinmu. Muka je Jos da Makurdi da Enugu da Ogoja da Kalaba da Fatakwal da Ribas da Bonny da Kalabari da Digimi da Okrika da Brass, lokacin kananan wurare ne. Mun kwanan biyu sannan muka isa Fatakwal ranar 11 ga Disamban 1959.
Yaya aka kafa gwamnatin siyasa ta farko?
Jam’iyyar NPC tana da mafi yawan ’yan majalisa, amma ba za ta iya kafa gwamnati ita kadai ba. Don haka Awolowo ya nemi Zik don su kafa gwamnati domin a kebe mutanen Arewa, shi kuma Zik ya fi son Arewa shi ya sa yake da hadin gwiwa NCNC-NEPU a lokacin kamfe sannan ya so a yi a gwamnati a tsakanin NCNC-NPC don mu NEPU muna da kujeru takwas ne kawai, shi ya sa Malam Aminu Kano ya zama mai tsawatarwa.