Yadda muka ji lokacin da muka ga kaset din yankan rago ga danmu – Iyalan Soja
Iyalan sojan saman nan Abubakar Umar da ’yan Boko Haram suka kashe kuma suka nuna a shafin youtube na intanet sun ce abin takaici ne yadda aka dauki tsawon shekara guda kafin a ga faifan hallaka dan nasu.’Yan kungiyar Boko Horam sun saki faifan a youtube a kwanakin baya, inda aka nuno suna yi wa […]
Iyalan sojan saman nan Abubakar Umar da ’yan Boko Haram suka kashe kuma suka nuna a shafin youtube na intanet sun ce abin takaici ne yadda aka dauki tsawon shekara guda kafin a ga faifan hallaka dan nasu.
’Yan kungiyar Boko Horam sun saki faifan a youtube a kwanakin baya, inda aka nuno suna yi wa Abubakar Umar da ke aiki a karkashin rundunar sojan sama ta Enugu tambayoyi sannan suka kwantar da shi suka yanka shi inda suka raba gangar kansa da jikinsa.
Wan marigayin mai suna Ahmad Umar ne ya fara ganin faifan kafin ya nuna wa mahaifiyarsu inda ita kuma ta nuna wa matarsa, amma matar ta kasa kallon har karshe bayan da ta shaida lallai mijinta ne.
Mahaifiyar sojan, Malama Fatima Umar, ta ce danta na da kwazo kwarai, shi ya sa ya shiga aikin sojan sama a shekarar 2009, kuma bai taba zuwa hutun shekara ba.
“Bayan ya yi auri Asma’u, sun haihu aka sa wa dan suna Ahmad. Ya tafi Borno ne dansa na da wata uku, kuma zai cika shekara biyu a Nuwamba mai zuwa.
Malam Fatima Umar ta ce ba dadi mutum ya mutu har a shekara, hukuma ba ta sanar da iyalansa ba. Sannan sun fara gani ta intanet ne ranar 4 ga watan azumin Ramadan din bana.
Ta ce, a da kullum suna waya, amma da aka yanke layin sadarwa, sai suka daina jin duriyarsa, kuma da waya ta dawo sai suka kara damuwa don bai kira ba.
Matarsa, Asma’u ta je Enugu aka ce mata ana bincike. Da ta je Borno sai aka ce mata ya ce zai shiga bayi, amma ya aje bindigarsa ya gudu. Da ta dawo sai surukarta ta bi ta suka koma Borno inda aka ce musu ana bincike. Sannan sun kwana a asibiti don ’yan Boko Haram sun kona barikin sojan saman na Borno.
Asma’u Abubakar ta ce an tura shi Borno ne shekara daya da rabi da suka wuce.
Bayan ganin mummunar kisan ne, sai suka sanar da rundunar sojan sama da ke Kaduna inda suka tausaya musu.
Manyan rundunar sun ziyarci iyalansa a Kaduna don so jajanta musu da takardar shaidar cewa an kara masa girma daga mai igiya daya zuwa saje. Kuma an ba su takarda sun sa hannu don ganin an biya su hakkokinsa.
Wansa Bashir ya ce kanensa ya fara sakandaren Unguwan Sarki ya kammala a Kwalejin Gwamnati ta Kaduna, kumac wata bakwai ba su ji duriyarsa, kafin fitowar faifan.
“Muna bukatar hukuma ta binciki wanda ya aike shi ya sawo masa fanka, wanda hakan ne ya yi sanadin kama shi da hallaka shi da aka yi. Don irin kisan da aka yi masa ya yi muni,” inji Bashir.
Mahaifiyar marigayin ta ce ba za ta hana kowane danta shiga aikin soja ba, don kowa da irin yadda zai mutu.