Yadda muka ji mutuwar A’isha dankano – ’Yan fim da ke Amurka

’Yan fim din Hausa wadanda a halin yanzu suke halartar kwas a birnin Los Angeles da Kalifoniya da ke kasar Amurka, sun bayyana cewa mutuwar fitacciyar jarumar A’isha dankano ta girgiza su, ta sanya duniyarsu shiga halin kunci.Fitaccen jarumi Ali Nuhu ya bayyana wa Aminiya cewa ya riski labarin mutuwar ne a lokacin da ya […]

Yadda muka ji mutuwar A’isha dankano – ’Yan fim da ke Amurka
Yadda muka ji mutuwar A’isha dankano – ’Yan fim da ke Amurka

’Yan fim din Hausa wadanda a halin yanzu suke halartar kwas a birnin Los Angeles da Kalifoniya da ke kasar Amurka, sun bayyana cewa mutuwar fitacciyar jarumar A’isha dankano ta girgiza su, ta sanya duniyarsu shiga halin kunci.
Fitaccen jarumi Ali Nuhu ya bayyana wa Aminiya cewa ya riski labarin mutuwar ne a lokacin da ya shiga shafin Twitter, inda ya ga sanarwar mutuwar. Ya bayyana cewa mutuwar ta girgiza shi, inda a karshe ya yi wa marigayiyar addu’ar samun rahama.
Darakta Kamal S. Alkali ya bayyana cewa ya samu labarin rasuwar jarumar ne bayan sun kammala sauraron wata lacca, inda bayan sun samu hutu sai ya shiga shafin Instagram, a nan ya ga fitaccen dan jarida mai daukar hoto Sani Maikatanga ya kawo labarin rasuwar jarumar. Ya ce a lokacin da ya karanta labarin yana tsaye amma ji ya yi kafafunsa sun kasa daukarsa, dole ya samu wuri ya zauna.
Daraktan ya bayyana cewa akwai wani fim dinsa mai suna Bakar Lema kuma marigayiyar ita ce za ta ja ragamar fim din, inda rasuwarta ya sanya hannun agogo ya dawo baya. Ya yi mata addu’ar samun jinkai, sannan ya bukaci masoyan harkar fim su rika yi wa mata addu’a.
Mawaki, furodusa kuma darakta, Nazifi Asnanic ya ce darakta Kamal S. Alkali ne ya sanar da shi labarin rasuwar jarumar, inda nan da nan ya ji gumi ya keto masa duk da cewa a lokacin ana sanyi.
Jarumi Bello Muhammad Bello ya ce yana da kyakkyawar alaka da marigayiya, inda a lokuta da yawa sukan ba juna shawara kan yadda za su tafiyar da harkar fim, don haka mutuwar ta zo masa a ba zata, kuma ta yi matukar kada masa hantar ciki. Ya bukaci al’umma su sanya marigayiyar ciki addu’arsu a duk lokacin da suka tuna da ita, sannan ya yi addu’ar Allah Ya sa wadanda suka rage su cika da imani.
Jaruma Hadiza Gabon ta bayyana cewa ba ta san lokacin da hawaye ya rika kwarara daga idanunta ba, kasancewar ta dauki marigayiyar tamkar yayarta, inda a lokuta da dama takan ziyarce ta, sannan su zauna su yi hira cikin farin ciki da jin dadi.