Yadda muka kafa jam’iyyar NEPU da PRP – Muhammadu dangalan
Muhammadu Dauda dangalan dan Jam’iyyar PDP ne da ya fara siyasa yana dan shekara 21. A yanzu yana da shekara 83 a duniya, a tattaunawarsa da wakilanmu na TUNA BAYA, ya yi bayanin yadda ya taka rawa wajen kafa Jam’iyyar NEPU, da PRP da kuma alakarsa da Malam Aminu Kano. Kuma ya yi bayanin matsalar […]

Muhammadu Dauda dangalan dan Jam’iyyar PDP ne da ya fara siyasa yana dan shekara 21. A yanzu yana da shekara 83 a duniya, a tattaunawarsa da wakilanmu na TUNA BAYA, ya yi bayanin yadda ya taka rawa wajen kafa Jam’iyyar NEPU, da PRP da kuma alakarsa da Malam Aminu Kano. Kuma ya yi bayanin matsalar amfani da kudi a siyasa da kuma bukatar ‘yan siyasa su yi amfani da akidar jam’iyya.
Yaya ka shiga cikin siyasa ganin kana cikin wadanda suka assasa Jam’iyyar NEPU?
Na fara siyasa ina karami. An haife ni a Fagge na Jihar Kano. A can kuma na yi karatun boko da na addini. Mun fara ne da kafa wata kungiya mai suna Taron Masu Zumunta (TMZ) tare da Malam Abba Mai Kwaru a matsayin shugaba. Makasudin kafa kungiyar shi ne taimakon juna a lokacin biki kamar aure ko kuma akasin haka. Malam Jibril mahaifin Farfesa Sani shi ne ma’aji ni kuma sakataren kudi sai kuma Musa kaura a matsayin babban sakatare.
Daga baya sai muka fara tunanin zama jam’iyyar siyasa, Malam Aminu Kano da Abba Mai Kwaru suka bada goyon baya. Da haka ne aka kafa Jam’iyyar NEPU da manufar taimakon al’umma. Mun yi niyyar amsa tambayoyin da muke yi na: Me ya sa aka tauye wa mutane hakki? Me ya sa ake rashin adalci, aka sanya mutane cikin wahala na dole kuma a bautar da su? dandanan sai muka samu karbuwa. Sai muka amince a tsakanin mu cewa za mu wayar da kan mutane a kan manufofinmu na shekara 10 kafin mu nema shiga takara. A ka’aidar jam’iyyar a wannan lokacin, idan mutum zama shugaba, dole zai tara ‘yan jam’iyya da sauran wadanda yake so ya yi aiki da su domin samun amincewa. Duk wanda jam’iyya ta ki amincewa da shi sai a cire shi a maye gurbinsa da wani.
Babban makasudin kafa Jam’iyyar NEPU shi ne a wayar wa mutane da hankali, musamman ‘yan Arewa a kan cewa Allah Ya halicci wannan kasar ne domin su, don haka dole a basu hakkinsu a matsayin su na ‘yan kasa ba bayi ba. Nasarar da muka fara samu ce ta sa mutane suka karbi jam’iyyar, amma bayan mun samu karbuwa, sai aka fara tursasa mutane domin su bar mu. Ni ne farkon shugaban Jam’iyyar a Fagge.
Sauran wadanda aka assasa jam’iyyar da su sun hada da Abba Mai Kwaru da Joshph Idowu da Magaji danbatta da Adamu danjaji. Mun yi zama na farko ne a gidan Abba Mai Kwaru a Fagge.
Kana dan shekaranka nawa lokacin da ka fara siyasa?
Na fara siyasa ina dan shekara 21.
Mene ne manyan matsalolin da kuka fuskanta a lokacin?
Babban kalubalenmu a lokacin shi ne yadda ake mana kallon mutane banza saboda akidar mu. Wannan ya janyo mana cikas matuka. Sun ce wai muna yaki da shugabanni, amm kuma ai a filie yake yadda sarakunan gargajiya da Turawan mulkin mallaka suke hada kai wajen tauye hakkin mutane. Daga karshe sai suka kafa ma’aikatan lardi wato Natibe Authority sannan suka ba sarakunan karfin da za su ci gaba da taka mutane, wannan ne matsalar kasar a wancan lokaci. Me ya sa ba za su girmama mutane ba? Wannan ne ya sa suke tunanin cewa mun kafa jam’iyyar ne domin mu bibbiyyi yadda suke gudanar da mulki. Amma maganar gaskiya ita ce mun kafa jam’iyyar ce domin kwato wa mutane hakki, na biyu kuma mu wayar da kan ‘yan Najeriya su kwaci ‘yancinsu. Burinmu shi ne mutane su kwaci ‘yancin zaben shugabannin da suke so.
An ce an daure da yawa daga cikin ‘yan jam’iyyar, kai ma an daure ka?
An daure ni na wata shida. An daure mu a Gidan Yarin Kurmawa daga baya kuma aka mayar da mu na Goron Dutse inda ya fi kunci da katura, a can tabarma ce kawai a dakin ‘yan Fursuna.
Mene ne laifinka?
Sun ce wai ina tunzura mutane su yi tawaye ga sarakuna.
Yaya rayuwa a cikin Fursuna?
Gaskiya Goron Dutse waje na maganin masu lafi. Kuma duk rayuwar gidan Fursuna ba dadi.
A lokacin kana da iyali”
Eh, ina da iyali.
Ya suka yi rayuwa a lokacin kana ginda yari?
Na riga na sadaurkar da aryuwa ta ga talakwa. Allah Ya san zuciya ta. A lokacin ba na wani tunanin iyalai na, kawai tunani yadda za a yi adalci ne kuma ban damu ba.
Ya za ka kwatanta alakarka da Malam Aminu Kano?
Ina godiya ga Malam Aminu Kano domin ya koyar da ni abubuwa masu kyau. Na biyu kuma shi ne yadda sa min albarka kwana hudu kafin ya mutu. Ya zo ofishinmu a kusa da gidan shi, ina saman bene a lokacin sai ya tambayi Sani Gule da Tadada da sauransu. Da muka sauko muka same shi, sai ya ce, “ina maka godiya domin na san kana fuskantar muzgunawa a matsayinka na sakatare. Amma ina so ka ci gaba da hakuri domin na san cewa bayan ni kai ne za ka iya ci gaba da dabbaka manufofin jam’iyyarmu.” Wadanda a ka yi wannan maganar da suke raye yanzu su ne Malam Bello da Sanata Garba Taura. Ya zo ne ranar Alhamis, sai kuma ya rasu a ranar Asabar. Kafin rasuwarsa, watarana ya zauna tare da ‘yan majalisarsa, ni lokacin ina kan hanya daga Fagge, sai na ce zan sauka a gidan shi domin in duba shi amma ban samu iko ba, cikin ikon Allah sai ranar Lahadi aka sanar da ewa ya rasu.
Me ka koya daga marigayin?
Na koyi tsayawa tsayin daka a kan akidar jam’iyyarmu domin mu tabbatar babu wani wanda ya danne kowa a jam’iyyar. Na koyi abubuwa da yawa a rayuwar siyasa ta daga gare shi.
Yaya kuka canja zuwa PRP?
A lokacin da aka dage takunkumin da aka dora wa jam’iyyun siyasa. Sai mu ka sake haduwa muka kafa PRP. Ina cikin kwamitin da aka ba alhakin hada tuta da sauransu. Mun yi taron ne a gidan Malam Aminu Kano, amma kuma kwamitin da za su fitar da da tambarin jam’iyya sai suka yi zama a GRA amma na mata sunan wanda ya jagoranci wannan kwamitin. Da ni da Iili Garba da wani wakili daga Gumel mai suna Ibrahim Wada wanda daga bisani ya zama mataimakin shugabanmu da Musa Iliyasu wanda shi ma daga bisani ya zama mataimakin dan takarar gwamna da marigayi Sabo Bakin Zuwo muna tare a cikin kwamitin. Mun yi babban taron kasa ne a Kazaure inda muka zabi Salihi Iliyasu da Ibrahim Tsoho a matsayin dan takarar gwamana da mataimaki. Daga baya sai hukumar zabe ta dakatar da su. Wannan ne ya sa Abubakar Rimi ya zama dan takarar mu a zaben 1979.
Me ya kawo rikcin tsakanin Abubakar Rimi da Malam Aminu Kano?
Malam Aminu Kano na da akida. Ya ce wa Abubakar Rimi da Balarabe Musa na Kaduna su fuskanci yadda za su taimaki mutane ba wai jin dadi ba, saboda wannan shawara da ba ya basu, duk da cewa ba ni a wajen taron, sai suka ji haushi. Ya ce musu lokacin jin dadi bai yi ba. Saboda haka sai suka hada mabiyansu da suke son irin rayuwarsu. Wannan ne ya sa suke kiranmu ‘Yan Tabo, mu kuma muke kiran su ‘Yan Santsi.
Su waye abokanan aikinka a PRP?
Akwai Musa Musawa da Shehu Shattima da Sani Darma da Adamu danjaji da Aminu Kano da sauransu
A lokacinku jam’iyyun siyasa kadan ne, mene ne ra’ayinka game da jam’iyyu da yawa?
Duk abin da aka ce jam’iyyun siyasa, ya kamata bukatar mutane ce a kan gaba. Shugabannin jam’iyya ne ya kamata su fitar da tsarin tafiyar da jam’iyya. Amma yanzu mun yi watsi da irin wannan tsari. Wannan ne ya sa muka shiga cikin wannan matsalar siyasar daga sama har kasa.
Mene ne ra’ayinka a game da siyasar uban gida?
Wannan yana faruwa ne idan mutum daya ya fi karfin kowa a jam’iyya. Shi zai fadi yadda yake so da kuma wadanda yake so a ba matsayi da matsayin da za a ba su. Idan aka ce komai na jam’iyya na hannun mutum daya ne, to lallai akwai matsala babba. Wannan ne ya sa muke cikin matsala a wannan kasar.
Ya za a magance matsalar?
Shi ne kawai a girmama kundin tsarin jam’iyyar. A ba jam’iyyar karfin ta. An yi dubi da gyara a kundin tsarin Jam’iyyar PDP sai uku. Na karshe shi ne wanda aka yi a 9 watan Disamba a shekarar 2017 bayan an samu tsaiko na shekara biyu.
Kasancewa bayan taron Abeokuta, an samu rikici, sannan kuma saboda shawarar Farfesa Jerry Gana da Sanata Ibrahim Mantu, sai aka kafa kwamitin mutum 30. Amma kwamitin bai samu damar yin aikin ba sai Ali Mofu Sheriff ya zama shugaban jam’iyya bayan ya samu goyon bayan gwamnoni. Hakanan kuma a taron Fatakwal, Sheriff ya nuna sha’awarsa na zama shugaban jam’iyya, amma sai muka dage a kan cewa kundin tsarinmu ya hana shugabannin riko su nemi shugaban jam’iyya. Wannan ne ya sa wani rikicin ya taso wanda ya sa Sheriff ya tafi kotu. Wannan ne ya sa mu wakilan jm’iyya na kasa muka rushe dukan mukaman, sai muka zabi mutum biyar wanda daga cikinsu muka zabi mutum biyu su zama shugabanni. Wannan ne ya sa Makarfi ya zama shugaban jam’iyyar PDP har muka samu nasara a kotu kafin babban taronmu na kasa da muka yi na karshe. Ya kamata a bi dokar da kundin tsarin jam’iyya ta tanadar domin shi ne ya sa muka samu nasarar cin yakin da ya dabaibaye mu na shekara biyu.
Me kuma kake yi bayan siyasa?
Ni tela ne kafin in fara siyasa duk da cewa daga bisani siyasa ta dauke ni baki daya. Ina cikin wadanda aka fara turawa Gusau mu nemo magoya baya, na je garuruwa da yawa a yankin Arewa ina neman magoya baya ga jam’iyyarmu. Zan iya tuna lokacin da na je Gusau sai na tsaya a kauyen Dabba inda na hadu da wani mutum mai kwazo wanda ya amshe ni sannan ya yi alkwarin ci gaba da yada manufar jam’iyyarmu.
Jam’iyyun siyasa nawa ka yi zuwa yanzu?
PDP kawai na yi bayan NEPU da PRP. Amma ba ni a cikin wadada suka kafa PDP, amma dai yazu ina cikin ta.
Ya za ka kwatanta siyasa a lokacin NEPU da PRP da kuma yanzu?
Ina bakin cikin yadda nake ganin yadda ake sa kudi a siyasar yanzu. Abin bakin ciki shi ne yadda matasan ‘yan siyasa suke son kudi fiye da kasa da cigabanta. Idan na tuna cewa wadannan mutane su ne shugabannin gobe, sai abin ya dame ni. Wane kasa muke gina wa kan mu haka? Ina tunanin cewa an yaudari matasan nan ne cewa amfani da kudi a siyasa ba matsala ba ce, kuma shi kadai ne hanyar da za su iya samun nasara.
Ya kamata wadannan matasan su gane cewa fa su ne shugabannnin gobe, kuma suna da nauyi mai girma da za su sauke.
Me kake yi yanzu domin samu abin za a sa bakin salati?
A lokacin da Yakubu Gowon ya karbi mulki ya hana siyasa, sai na zama ba ni da abin yi. A lokacin ne wani aboki na ya ce da ni tunda babu ranar da sojojin nan za su bar mulki, me zai hana in fara kasuwanci, sai na ce masa ba ni da jari sai ya ba ni bashin sayar da farantan gilasai, sai na karba na zuba a shago. Amma kuma a lokacin na hadu da danjuma Kankiya lokacin yana cikin kungiyar iyaye da dalibai na Firamaren Kuka sai muka zama abokai bayan na duba yadda aka kashe kudaden makarantar kuma na gano wasu almundahana da aka yi duk da cewa shugaban makarantar dan uwana ne. Ashe wannan abun da na yi ya burge Kankiya. Daga baya da zama manajan wani kamfanin Turai a Najeriya, bayan wasu ‘yan shekaru sai muka sake haduwa inda ya ce in same shi a ofishinsa. Da na je sai ya hada ni da wani babban kamfanin Siga na wancan lokacin. Harka da wanan kamfanin ne ya sa na sayi gida a ‘Yankaba kuma na samu wasu abubuwa da yawa. Amma duk da haka sai da na koma siyasa bayan an dage takunkumin da aka dora wa siyasa duk da cewa abokanai na irin su Bello Abiya sun roke ni kada in koma. Har yanzu ina da shago a Kasuwar Sabon Gari. Da wannan nake rike kai na. Ba na zuwan gidan wani ina maula.
Maganar iyali fa?
Ina da yara 12 da mata hudu, kuma ina gode wa Allah yara na duk sun girma suna yin sha’anin kansu, sannan kuma gasiya suna taimakona yadda ya kamata. Ina matukar alfahari da su.
Mece ce shwararka ga ‘yan siyasa?
Ya kamata su san cewa ana kafa jam’iyyun siyasa ne don al’umma ba don wasu daidaikun mutane ba. Sannan kuma ya kamata su san cewa siyasa ba a bin mutum daya ba ce, sannan kuma dukan ayyukan siyasa dole a yi shi kamar yadda kundin tsarin jam’iyya ta tanadar.