Yadda muka kafa kasuwar ’yan tumatir ta Jos – Alhaji Aminu
Alhaji Aminu Yahaya Yunusa shi ne Shugaban Kasuwar ’Yan tumatir ta Farar Gada da ke garin Jos, babban birnin Jihar Filato. A wannan tattaunawa da ya yi da wakilinmu, ya bayyana tarihin kafuwar wannan kasuwa da kuma sunan da tayi wajen tara tumatur da albasa da attarugu da sauran kayayyakin lambu. Ga yadda tattaunawar ta […]

Alhaji Aminu Yahaya Yunusa shi ne Shugaban Kasuwar ’Yan tumatir ta Farar Gada da ke garin Jos, babban birnin Jihar Filato. A wannan tattaunawa da ya yi da wakilinmu, ya bayyana tarihin kafuwar wannan kasuwa da kuma sunan da tayi wajen tara tumatur da albasa da attarugu da sauran kayayyakin lambu. Ga yadda tattaunawar ta kasance:
Aminiya: Mene ne tarihin wannan kasuwa?
Ita dai wannan kasuwa wasu mutane ne guda uku, wato Alhaji Ubale da Alhaji Yahaya Inusa da kuma Alhaji Ibrahim ne suka sayi filin wannan kasuwa, suka sanya motar gireda ta share. Aka kafa wannan kasuwa shekara 30 da suka gabata. Daga baya karamar hukumar Jos ta arewa, ta mayar masu da kudinsu wajen ya zama nata.
Tun daga lokacin da aka kafa wannan kasuwa har ya zuwa wannan lokaci muna zaune lafiya. Babu wata matsala ta rashin jituwa da ta taba tasowa a wannan kasuwa, duk da rikice-rikicen da aka samu a wannan gari na Jos. Duk da kabilu daban-daban da Musulmi da Kirista da muke a wannan kasuwa muna zaune lafiya.
Aminiya: Kamar wadanne irin kaya kuke sayarwa a wannan?
A wannan kasuwa muna sayar da tumatir da albasa da tattasai da attarugu da alayyaho da dai sauransu. Kuma kowanne kaya da muke sayarwa a wannan kasuwa, yana da bangarensa da shugabansa. Wato akwai shugaban banagaren ‘yan tumatir da shugaban bangaren ‘yan albasa da shugaban bangaren ‘yan alayyaho da shugaban bangaren ’yan attarugu. A takaice muna da bangarori guda 23 a wannan kasuwa, kumakowanne bangare akwai shugabansa. Kuma dukkansu suna karkashina ne.
Aminiya: Daga wadanne wurare ne kuke samun kayayyakin da kuke sayarwa a wannan kasuwa?
Muna samun albasa daga jihohin Yobe da Sakkwato da Kebbi. Kuma muna samun tumatir daga nan Jihar Filato da Jihar Kaduna.
Aminiya: Daga wadanne wurare ne kuka samun bakin da suke zuwa sayen kayayyaki a wannan kasuwa?
Muna samun baki masu zuwa sayen kayayyaki a wannan kasuwa daga Fatakwal da Eleme da Onaca da Kalaba da sauran sassan kasar nan daban-daban.
Aminiya: A wadanne ranaku ne wannan kasuwa take ci?
Wannan kasuwa tana ci a ranakun Asabar da Litinin da kuma Laraba ne.
Aminiya: Daga lokacin da aka zabe ka a matsayin shugaban wannan kasuwa zuwa yanzu, wadanne irin nasarori ne ka samu?
A lokacin da aka zabe ni a matsayin shugaban wannan kasuwa, babu fitilu a wannan kasuwa. Don haka daga zuwa na na yi kokari na sanya fitilu har guda 70. Bayan haka kafin mu zo babu ofishin shugaba a wannan kasuwa. Daga zuwanmu na gina ofis tare da taimakon hukumar MDG’s. Haka kuma a lokacin da na zo na samu wannan kasuwa ramuka sun yi yawa, na yi kokari na cike wadannan ramuka da kasa.
Aminiya: Wane tasiri ne kake ganin wannan kasuwa take da shi a garin Jos?
A gaskiya wannan kasuwa ta ‘yan tumatir da ke Farar Gada Jos tana da matukar tasiri a wannan gari. Domin wannan kasuwa ta yi suna a nan Jihar Filato wajen tara kayayyakin lambu. Kuma a dukkan kasuwanni da ke karamar hukumar Jos ta arewa, babu kasuwar da take tara mutane masu dimbin yawa kamar wannan kasuwa.
Aminiya: Wadanne irin matsaloli ne kuke fuskanta a wannan kasuwa?
Babbar matsalar da muke fuskanta a wannan kasuwa ita ce rashin filin da motoci za su rika tsayawa saboda cushewar da kasuwar ta yi.
Aminiya: Wanne sako ko kira ne kake da shi ga gwamnati?
Kira na ga gwamnati musamman karamar Hukumar Jos ta Arewa, shi ne ta saya mana fili a kusa da wannan kasuwa, saboda yanzu wannan kasuwa ta cushe sakamakon dimbin jama’ar da suke ta karuwa a kasuwar. Idan motoci suka kawo mana kaya, sukan sha wahala wajen fita daga wannan kasuwa. Don haka muna kira ga karamar Hukumar Jos ta Arewa ta saya mana fili a kusa da wannan kasuwa, don a samu a fadada kasuwar. Kuma a samar mana da rijiyar burtsatse da haka mana hanyoyin ruwa a wannan kasuwa. Bayan haka, ina kira ga Gwamnatin Tarayya ta hana shigo da tumatir da tattasai daga kasashen waje. Idan aka yi haka abin zai dada karfafa manoman kayan lambu a kasar nan.