Yadda muka kama ’yan kungiyar asiri ta badu 30 – Sarkin Hausawan Ikere
Sarkin Hausawan Ikere ya bayyana yadda suka sha fama da ’yan kungiyar asiri ta badu, inda suka yi hadin gwiwa da jami’an tsaro da sarakunan Yarbawan yanki, har suka yi nasarar kame ’ya’yan kungiuyar 30. Kuma a ‘yan watannin da miyagun aikace-aikacensu ya fara addabar jama’a, musanmman a ’yan kunan Igijo da Ikorodu a […]
Sarkin Hausawan Ikere ya bayyana yadda suka sha fama da ’yan kungiyar asiri ta badu, inda suka yi hadin gwiwa da jami’an tsaro da sarakunan Yarbawan yanki, har suka yi nasarar kame ’ya’yan kungiuyar 30. Kuma a ‘yan watannin da miyagun aikace-aikacensu ya fara addabar jama’a, musanmman a ’yan kunan Igijo da Ikorodu a Legas da ke makwaftaka da Jihar Ogun da yankunan Mowe da Ibafo duk a jihar Ogun, jama’ar da ke zaune a wannan yankin sun shiga tashin hankali matuka bayan bullowar ‘yan kungiyar asirin da ake kira badu ‘Badoo,’ wadanda suka addabi mazauna yanki da kisa, inda rahotanni suka nuna cewa sukan shiga gida su hallaka ilahirin mutanen gidan, sannan su sha jininsu, inda suke yawo da farin kyale su zuba kwanyar kan a ciki, wanda suke karbar Naira dubu 500 a duk farin kyale daya da suka hallaka mutum.
Da lamarin ya ki karewa jama’a da dama suka fara kaurace wa gidajensu a yankunan Ikorodu, sannan suka dauki matakin kone duk wani dan kungiyar asirin da ya shiga hannunsu, a irin wannan matakin jama’ar yankin sun kashe ‘yan kungiyar da dama. A lokuta da dama irin wannan kisan na rutsawa da wadanda ba su ji ba, ba su gani ba, ko a watan da ya gabata irin wannan kisa ya rutsa da wani dan wasan kwaikwayo.
Matakan da al’ummar yankin suka dauka don magance matsalar ‘yan kungiyar asirin shi ne hadin gwiwar jami’an ‘yan sanda da kungiyar Yarbawa zalla ta OPC da kungiyoyin sa-kai na ‘yan kato da gora da shugabannin gargajiya, inda kwamishinonin ’yan sandan jihohin Legas da Ogun suka yi ta jagorantar zama na musanmman da shugabannin al’umma.
A Jihar Ogun kwamishinan ‘yan sandan jihar Ahmad Iliyasu ya yi irin wannan zama da shugabannin yankin, tare da manyan jami’an rundunar ’yan sandan yankin, lamarin da ya kai ga cimma gagarumar nasara domin yini guda da kammala taron a garin Mowe Sarkin Hausawan Ikere ya yi nasarar kame ‘yan kungiyar asiri ta badu su 30.
A zantawarsa da Aminiya, Sarkin Hausawan Ikere Alhaji Aminu Abubakar Gusau a fadarsa da ke garin Ikere a karamar Hukumar Obafemi Owode a Jihar Ogun, ya ce dare daya Allah ya ba shi sa’ar kame ’yan kungiyar asirin badu su 30, kuma abin da ya ba su kwarin gwiwa shi ne taron da kwamishinan ‘yan sandan jihar ya yi da su a fadar babban Basaraken Yarbawa na garin Mowe, wato abin da ya faru shi ne a ranar 7 ga watan 7 na shekarar nan ta 2017 ne muka samu bayanin cewa akwai wasu ‘yan kungiyar asiri na badu sun shigo garin Mowe, wanda ke kan babbar hanyar nan ta Legas daga Ibadan sun shiga garin suna ta harbe-harbe, har sun kashe wani mutum sun danddake kwanyar kansa sun shanye jininsa. Alamun ‘yan kungiyar asiri ta badu su ne kashe mutum su daddake kansa su sha jininsa. Da abin ya fara taba jama’armu ‘yan Arewa masu yin kasuwancin a yankin, domin sukan far musu su sassaresu su kwatar musu ‘yan kudin da suke kasuwancinsu da kuma wayoyyin salula. Sun raunata su da dama, wasu an yi musu magani a nan, wasunsu an mayar da su gida Arewa. Babu dai wanda aka kashe a jama’armu sai dai mutane sun tsorata kwarai. Wannan dalili ne ya sanya Sarkin Hausawan Mowe ya shigar da maganar zuwa gurin Sarkin Hausawan Abeokuta, inda aka yi sa’a a daidai wannan lokacin da ya je sai ya iske ana taron kungiyar bakin da ba Yarbawa ba mazauna jihar Ogun, inda nan take shugaban kungiyar ya kira kwamishinan ’yan sandan jihar, wanda shi ma ya yi magana da manyan jami’ansa na yankin, nan take a ka yi aiki a hukumance jami’an ’yan sandan suka ɗauki matakan tsaron da ya dace.
Sarkin Yarbawan Mowe ya shiga gaba ya nuna gidajen da ’yan kungiyar asirin, inda aka yi aiki tukuru domin sai da aka kai karfe uku na dare a na binciko gidajensu ana kame na kamawa, masu gudu kuma suna gudu suna barin garin. Sai dai kash a tunanin mu wadanda suka gudu sun tafi da nisa ne a she guduwa suka yi yankin da nake mulki, wato garin Ileke, wanda shi ma yake a nan kan babbar hanyar Legas daga Ibadan. An tabbatar mana da cewa yaran da aka koro daga garin Mowe sun shigo mana.
A wannan gari namu akwai mashaya, wacce dandali ne da ta zama mahada, inda jama’a da dama ke gudanar da kasuwancinsu ba dare ba rana, a nan ne suka samu mafaka. Sai muka yi nazari cewa, idan ba mu dauki mataki ba yadda suka yi wa mutanen garin Mowe mu ma haka za su yi mana, muna tsaka da tattauna yadda za mu bullo wa lamarin sai kwamishinan ’yan sanda Ahmad Iliyasu da Sarkin Yarbawan yankin Olu na Ebanyi suka kira taron sarakuna na yankin baki dayansu da shugabanin PCRC da sauran jami’an tsaro, muka tattauna yadda za mu bullo wa lamarin.
“Wannan zama shi ne ya ba mu kwarin gwiwar magance abin da yake kokarin addabarmu na ’yan kungiyoyin asiri, nan fa muka samu karfin yin aiki domin mun ga cewar shi kwamishinan ’yan sanda da gaske yake da sauran shugabannin yanki muka amince wa juna kowa ya ba da tasa gudunmawar wajen kame bata gari ko a ina yake” inji Sarkin Hausawan Ileke.
Alhaji Aminu Abubakar Gusau Sarkin Hausawan Ileken ya ce bayan sun kammala taron sai ya komo gida ya shawarci matasan garin kan yadda za su fuskanci halin da ake ciki.
A cewarsa: “ Kun san irin masifar da ta addabi makwaftanmu a baya don haka wadannan ‘yan kungiyar asirin yanzu haka sun shigo mana, don haka ya kamata mu ɗauki matakin fidda su daga cikin mu, nan take matasan mu suka ce sun gane su, suna haduwa ne daga 12 zuwa karfe 1 na dare daga nan har zuwa wayewar gari, sai a neme su a rasa. Nan take muka yi shiri, na ce idan dare ya yi a tanadi daga barci, na fada wa matasan za su samu wuri su labe ni kuma zan je inda ’yan kungiyar asirin suke idan na je kusa gare su, sai su fito su kewaye mu. To a haka muka shirya Allah ya ba mu nasara cikin ikonSa muka kame su gaba dayansu. Na sa aka daure su mutum bibbiyu kowane a jikin rigar dan uwansa, muka fito da su, su 30 mata uku maza 27, nan muka mika su ga hukuma. Hukuma ta gano tabbas su ne ‘yan kungiyar asirin da suka gudo yankinmu neman mafaka, daga nan mazauna gari muka bullo da hanyar tantance kawunan mu, ta yin katin shaidar zama gari, kowa da bayanansa da na sana’arsa. Hakan shi ne zai hana batagari kutsowa cikinmu.”
Ya ce, kawo karshen aikace-aikacen ‘yan kungiyar asirin ya yi alfanu kwarai, domin sun samu bayanan cewa a baya ‘yan kungiyoyin asirin sun fara tallata wa wasu matasan Arewa mazauna yankin kungiyar, inda ya ce babban kalubalensu da suke fuskanta shi ne yadda lauyoyi ke tsaya.
“ Mu da Allah muka dogara da zuciya daya muke aiki, ba ma tsoron cewa in an saki mai laifin da muka kama zai iya zame mana barazana, kodayake a baya ma irin hakan ta faru da mu. Ana samun lauyoyin da suke tsaya wa batagari a kotu, wadanda suke shiga su fita su tabbatar an sake su, ko a baya akwai barayin babura da ke addabar al’umma a kan babbar hanyan Legas daga Ibadan, inda a wancan lokacin a kan yawaita ganin gawa a gefen hanya, sai in ’yan uwanta sun zo dauka sai su ce an kashe mamacin ne aka sace babur dinsa, da muka tashi haikan a kan masu satar baburan muka kame su, bayan an kai su kotu lauyoyi sun tsaya masu aka sako su. Nan suka dawo suka zame mana alakakai, sai daga bisani ne muka gane shugabansu yana nan tare da mu a garin nan, nan muka sake kai kukanmu ga ‘yan sanda, inda aka sake kame su. Shi ma yanzu yana can a tsare, wato babban nasu, tun daga wannan lokaci kuma ba mu sake jin an kashe wani an kwace babur dinsa a wannan gari ba. Babban kalubalenmu shi ne yadda lauyoyi ke tsaya wa batagari suna fito da su suna dawo wa cikin jama’a suna tada masu hankula,” inji shi. An takaita hawan babur da daddare da hada-hada a kulob-kulob da mashaya a birnin Abeokuta.