Yadda muka kasance a hannun Boko Haram – ’Yan matan Dapchi
Yadda aka sake su Murna a Dapchi tamkar Sallah Gwamnati ta kitsa sace su – PDP Daliban Kwalejin Kimiyya da kere-kere da mayakan Boko Haram suka sako bayan wata daya da sace su, sun iso Abuja a cikin dare shekaranjiya Laraba, inda ake sa ran za su gana da Shugaban kasa Muhammadu Buhari a jiya […]

Yadda aka sake su
Murna a Dapchi tamkar Sallah
Gwamnati ta kitsa sace su – PDP
Daliban Kwalejin Kimiyya da kere-kere da mayakan Boko Haram suka sako bayan wata daya da sace su, sun iso Abuja a cikin dare shekaranjiya Laraba, inda ake sa ran za su gana da Shugaban kasa Muhammadu Buhari a jiya Alhamis, sai dai har zuwa hada wannan rahoto ba su gana ba.
’Yan matan sun bar Dapchi ne bayan sun gana da iyayensu, inda suka isa sansanin sojin sama na Maiaduguri da misalin karfe 5 na yamma, suka ci abinci kafin a dauko su a jirgin sama zuwa Abuja.
Kafin barin daliban garin Dapchi daya daga cikinsu mai suna Khadija Grema ta shaida wa Aminiya cewa lokacin da ’yan Boko Haram din suka sace su, sun yi ta shiga daji da su, “Kuma sun tambayi wadanda suka yi azumi daga cikinmu inda suka ba mu abinci da abin sha, sannan daga baya muka yi sallolinmu,” inji ta.
Khadija Grema ta ce ’yan Boko Haram din sun ba su duk kulawar da ta kamata, “Mun yi tafiyar kwana da kwanaki a cikin daji da koramu da gulabe kafin mu isa wani gida da suka ajiye mu. A gidan suna ba mu abinci kuma babu wanda ya kasance mu da lalata ko cin zarafi. Haka suka sa muka cire kayan makarantarmu suka ba mu wadanda muke sanye da su a yanzu. Haka muka yi ta zama a wurinsu har tsawon kwanaki ashirin da bakwai kafin su mai do mu,” inji ta.
Khadija ta bayyana wa Aminiya cewa yara biyar daga cikinsu sun rasu kuma an yi musu sutura irin ta addinnin Musulunci amma yarinya daya daga cikinsu wacce Kirista ce tana hannunsu, saboda kin karbar Musulunci da ta yi.
“Sun ce ta yi Kalmar Shahada amma ba ta yi ba sai suka ce za ta ci gaba da zama a wurinsu har lokacin da ta karbi addinin Musulunci,” inji Khadija
Daga aka tambaye ta game da fasalin ’yan ta’addan Khadija Grema ta ce, suna sanye da kayan sojoji kuma suna magana da harshen Kanuri da Larabci kawai.
Ita kuwa Fatima Abdullahi a wani faifain bidiyo ta shaida wa wani mai suna Modu Geidam cewa ita ’yar aji daya ce a Babbar Sakandaren Makarantar Dapchi. Ta ce da safiyar nan (shekaranjiya Laraba) aka dawo da su. Ta ce yanzu za ta je asibiti ne a duba ta. Da ya tambaye ta ko wani abu ya same ta, sai ta ce “Wallahi babu a bin da suka yi mana. Suna ba mu abinci mu ma muke dafawa da kanmmu. Sun ajiye mu ne a wani wuri a rufe da ko jirgi ba zai iya ganinmu ba. Amma dai alhamdulillahi. Mutum biyar ne suka rasu, amma biyu na sani a cikinsu, kuma matsatsi a cikin mota ce ya sa suka rasu lokacin da ake dabe mu saboda a kansu aka zauna. Wadanda na sani akwai A’isha akwai Maimuna, amma da za mu dawo a cikin natsuwa aka shiga mota.”
Murna a Dapchi tamkar Sallah
Iyaye da mutanen garin Dapchi sun samu kansu cikin yanayin murna da farin ciki sakamakon dawowar da ’yan mata ’yan makarantar Dapchi da kungiyar Boko Haram ta dawo da su a shekaranjiya Laraba.
An mika musu ’yan matan ne da aka dauko su a manyan motoci takwas zuwa cikin garin da misalin karfe 8:18 na safe, bayan sun shafe awa daya da rabi suna yi musu wa’azi.
Abba Musa da aka fi sani da Shago daya daga cikin mutanen da suka gane wa idanunsu yadda abin ya kasance, ya bayyana wa Aminiya cewa yana zaune a bakin tashar garin sai ya ga ayarin motocin ’yan Boko Haram guda takwas sun tunkaro garin.
“Dama mun ji labarin suna kan hanya saboda sun sauke daya daga cikin ’yan matan a garin Bumsa. Da farko mutane sun fara guduwa amma da yaran suka fara saukowa daga mota sai garin ya rude, jama’a suka rika ihu suna godiya ga Ubangiji.
’Yan Boko Haram din sun ce kada mu gudu, ba za su taba kowa ba. Sun kawo yaran ne a kashin kansu saboda ’yan uwansu ne Musulmi kuma gwamnati ba ta ba su kudi ba,” inji shi.
Ya ce “Sun tambayi mutanen garin ko ba su murna da dawowar ’yan matan, sai muka amsa da cewa: “Dukanmu muna murna.” Kuma sun roke mu kan mu gyara musu tayarsu da ta yi faci, inda muka gyara musu cikin farin ciki kafin su tafi.”
“Sun kalle ni suka ce, “gashin kanka haram ne. Kuma a matsayinka na Musulmi ya kamata ka ajiye gemu kamar namu ba ka rika aski irin na Balotelli ba. Kuma sun ce duk wanda yake son ya shiga aikin Allah Ya bi su, amma babu wanda ya bi su,” inji shi.
Ya ce an ajiye yaran ne kusa da wurin da ’yan sanda ke duba motoci kuma sojoji da ’yan sanda da sauran jami’an tsaro duk sun janye daga garin a lokacin da ’yan Boko Haram din suka shigo garin.
Ya ce sun shigo garin a natse kuma suka shafe fiye da rabin awa suna yi wa mutane wa’azi kafin su ce a yi musu rakiya.
“A can bayan gari suka ce ko akwai wanda zai bi su aikin Allah, amma ba mu yi wannan kasadar ba,” inji shi.
Shi kuwa Shugaban kungiyar Iyayen ’Yan Matan Dapchi da aka sace, Bshir Manzo wanda ya ce ya ga ’yarsa ya ce yana godiya ga gwamnatin Shugaba Buhari kan hakan.
“Ya yi mana alkawarin za a dawo mana da ’ya’yanmu cikin gaggawa da koshin lafiya. Yau duk mun gaskata cewa shi mutum ne mai fada-da-cikawa. Kuma muna godiya ga dukan wadanda suka ba mu goyon baya a wannan lokacin mai wuya. Kuma muna rokonsa da ya taimaka a sako mana ’yarmu daya da ke hannun ’yan Boko Haram din,” inji shi.
Iyayen yara biyar da suka rasu da mahaifiyar yarinya daya Kirista da ta ki canja addininta kuwa suna cikin bakin ciki da damuwa.
daya daga cikin iyayen yaran da suka rasu mai suna Adamu Jumbam ya shaida wa wakilinmu cewa rasuwar ’yarsa babban rashi ne, amma haka Allah Ya kaddara. “Babban abin takaici shi ne yaran nan sun dauki ’ya’yanmu a raye suka kashe su a kan hanya amma suka mayar da sauran ba tare da wani hukunci ba. Wannan da me ya yi kama? Kamar Badawi ne ya shiga gidanka ya yi sata, ya kashe danka kuma ya dawo ya ijiye abin da ya sata ba tare da an yi masa komai ba? Gwamnati ta yi kokari amma ba a kyauta mana ba,” inji shi.
Mahaifiyar yarinyar da ta ki canja addininta, Misis Rabecca Shurabu wadda ta some lokacin da ta samu labarin ba a sako ’yarta ba, ta roki Shugaba Buhari ya taimaka a sako ’yarta domin ita ce kawai abin da ta mallaka.
“Kowa yana da ’yancin ya yi addinisa, kuma ko Annabin Musulunci ya zauna da wadanda ba Musulmi ba ba tare da tsangwama ba. Su yi hakuri su bar mini ’yata,” inji ta.
Mu ma ku sako mana ’ya’yanmu – Mutanen Chibok
Iyayen ’yan matan Chibok da Boko Haram ke ci gaba da rike su sun yi kiran da su tausaya musu su sako musu ’ya’yansu su ma.
Shugaban kungiyar Iyayen ’Yan matan Chibok, Mista Nkeki ne ya yi kiran yayin ziyarar tausayawa da ya kai Dapchi.
Ziyarar ta zo ne dab da lokacin da aka sauke ’yan matan Dapchi a kan idon mutanen Chibok din. “Muna murna da dawowar wadannan ’yan matan kuma muna rokon masu fada-a-ji su mayar da hankali wajen ganin an kwato mana sauran ’ya’yanmu,” inji shi.
Yadda aka sako su
Bayanai sun ce aikin da Hukumar Tsaron kasa (DSS) da sauran hukumomin tsaro suka gudanar ne ya haifar da sako ’yan matan na Dapchi, kamar yadda Aminiya ta samu labari.
Kafin sako su an samu gagarumar hadin gwiwa a tsakanin hukumomin tsaro inda suka hanzarta tuntubar ’yan ta’addan tare da tattauna yadda za a sako su.
Kuma duk da Gwamnatin Tarayya ta ce ba ta biya ko kwabo ba ga mayakan Boko Haram kafin sako ’yan matan na Dapchi, akwai bayanan da suka ce an kulla yarjejeniya da ta gamsar da ’yan Boko Haram din kafin sako su, yarjejeniyar da ba lallai b ace ta shafi biyan kudi, sai dai wasu abubuwa na daban, da ake jin akwai yiwuwar musayar fursunoni ko ba su damar samun magunguna ko sauran kayayyakin da za a iya musayarsu da ’yan matan.
Ministan Watsa Labarai, Alhaji Lai Muhammed dai ya ce gwamnati ba ta biya ko kwabo ba kan sako su, inda ya ce sako ’yan matan da Boko Haram ta yi ya faru ne sakamakon kyakyawar yarjejeniya da aka yi da mayakan a bayan fage.
Ministan ya kuma ce: “Domin ceto ’yan matan, gwamnati ta gano cewa rikici da tashin hankali a tsakani gwamnati da mayakan ba mataki da ya kamata ba ne, domin yin haka zai yi wa rayuwar yaran barazana, don haka muka dauki matakin sasanci da mayakan.”
Lai Muhammed ya ce lokacin da mayakan ke kokarin mayar da ’yan mata sai da aka dakatar da ayyuka a garin domin ganin an mayar da su lami lafiya ba tare da wata tarzoma ko lahani ba.
Gwamnati ta kitsa sace su – PDP
A yayin da jama’a ke yabo kan sako ’yan matan na Dapchi, babbar jam’iyyar adawa, Jam’iyyar PDP ta yi zargin cewa Jam’iyyar APC da fadar Shugaban kasa ne suka kitsa sace matan Dapchi 110 a watan jiya.
Wata sanarwa da Kakakin PDP, Cif Kola Ologbondinyan ya aike wa manema labarai, ta ce APC da wadansu jami’an Fadar Shugaban kasar ne suka shirya sace ’yan matan “domin cimma wani buri na siyasa.” Sai dai babu wata kafa da ta tabbatar da wannan zargi na Jam’iyyar PDP, sannan har zuwa hada wannan rahota gwamnati da Jam’iyyar APC ba su mayar mata da martani kan zargin ba.
Buhari ya cancanci yabo – Dokta Tilde
Dokta Aliyu Tilde ya yi yabo da jinjina ga Shugaba Buhari kan ceto ’yan matan. Ya rubuta a shafinsa na Facebook cewa: “Wannan lamari ne mai dadi ga iyayen yaran sannan abin a jinjina wa Shugaba Buhari ne, wanda ya yi barazanar gurfanar da kwamandojin sojin a gaban kotun sojoji.”
A ganin Dokta Tilde ko da fansa aka biya aka karbo yaran, to hakan ya fi domin su dawo gida da wuri maimakon a tsaya jiran shekaru.
Ya ce a ganinsa ko da fansar aka biya, iyayen yaran za su zabi haka fiye da zama cikin zullumi.
A karshe ya bai wa gwamnati shawarar cewa ya kamata ta kara tsaurara matakan tsaro a yankin Arewa maso Gabas ta yadda mayakan Boko Haram ba za su iya amfani da injin fitar da kudi na ATM ba.