Yadda muka kashe manyan yaran Bello Turji —Sojoji

Bello Turji ya yi garkuwa da mutane suna taka da sallar Isha a cikin masallaci a Jihar Zamfara

Yadda muka kashe manyan yaran Bello Turji —Sojoji

Bello Turji

Rundunar Sojin Sama ta Najeriya ta bayyana cewa hare-haren da jiragenta suka kai su halaka manya-manyan ’yan ta’adda a Jihar Zamfara.

Sanarwar tsa Daraktan Yaɗa Labarai na Rundunar, Iya Bais Mashal Olusola Alinboyewa, ya ce bayanan sirrin da suka samu sun tabbatar cewa an halaka gawurtattun yaran jagoran ’yan ta’adda, Bello Turji.

Iya Bais Mashal Olusola Alinboyewa ya ce an jikkata ’yan ta’adda masu yawan gaske a yayin hare-haren da jiragen suka kai da haɗin gwiwar dakarun sojin ƙasa.

Sai dai ta bayyana cewa ba su da masaniya a halin yanzu game da inda Turji yake ko halin da yake ciki ba, amma “an kashe ’yan bindiga da dama ciki har da jagororinsu, wasu da dama kuma sun sha da ƙyar da raunin harbi.

“Sakamakon ƙazamin harin da muka kai, yanzu babu labarin inda Bello Turji ya shige ko halin da yake ciki, wanda hakan ya ƙara rikita yara nasa.”

Ya ce jiragen sun tsinkayi ’yan ta’addan ne a yayin da suke tserewa ta kan wani tsauni, inda ba tare da ɓata lokaci ba sojoji suka fara ragargazar su da rokoki da sauran makamai, inda aka ayi nasarar kuɓutar da mutanen da suka yi garkuwa da su, wanda hakan ya haifar da farin ciki a zukatan al’umma,” in ji Iya Bais Akinboyewa.

Turji ya yi garkuwa da mutane a masallaci

Ƙasurgumin ɗan ta’dda, Bello Turji ya yi garkuwa da wasu mutane da ya sace a masallaci yankin Birnin Yero da ke Jihar Zamfara.

Ɗan ta’adda kuma ƙwararren a fannin yaki da ta’addanci, Zagazola Makama ya bayyana cewa Turji ya yi awon gaba da mutanen ne a yayin da suke tsaka da Sallar Isah’s wani masallacin ranar Juma’a a.

Zagazola ya bayyana cewa Turji ya yi aown gaba da mutanen zuwa cikin jeji, kuma wata majiya ta shaida masa cewa ɗan ta’addan na shirin amfani da mutanen a matsayin garkuwa a maɓoyarsa daga hare-haren sojoji.

Hakan na zuwa ne bayan wasu hare-haren jiragen soji sun halaka fararen hula 15 tare da jikkata wasu 16 a yayin da jiragen suke ragargazar ’yan ta’adda a ƙananan hukumomin Zurmi da na Jihar Zamfara.

’Yan sanda da gwamnatin Zamfara sun tabbatar cewa akasarin waɗanda aka kashen ’yan sa-kai ne da ke fatattakar ’yan bindiga. Sun nemi ɗauki daga jiragen soji, amma aka yi samu kuskure harin jiragen ya shafe su su ma.

Karo na biyu ke nan cikin kasa da wata guda da irin haka ta faru, bayan wanda ya faru a Ƙaramar Hukumar Island ta Jihar Sakkwato.

Aminiya ta ruwaito cewa fararen hula mutum 465 aka kashe a hare-haren kuskuren jiragen soji a shekara 11 da suka gabata a Najeriya.