‘Yadda muka katange jihar Kogi daga COVID-19’

Jihohin Kogi da Kuros Riba ne kadai jihohi biyu a fadin Najeriya da ba a samu wanda ya harbu da cutar coronavirus ba. Kwararru da dama, wadanda suka hada da Kungiyar Likitoci ta Najeriya (NMA), sun bayyana shakku a kan rashin samun wanda yake dauke da COVID-19 a jihar Kogi, ganin cewa dukkanin makwabtanta sun […]

‘Yadda muka katange jihar Kogi daga COVID-19’

Yahaya Bello, Gwamnan Jihar Kogi

Jihohin Kogi da Kuros Riba ne kadai jihohi biyu a fadin Najeriya da ba a samu wanda ya harbu da cutar coronavirus ba.

Kwararru da dama, wadanda suka hada da Kungiyar Likitoci ta Najeriya (NMA), sun bayyana shakku a kan rashin samun wanda yake dauke da COVID-19 a jihar Kogi, ganin cewa dukkanin makwabtanta sun samu masu dauke da cutar.

Lamarin ya janyo takaddama tsakanin jihar da Hukumar Yaki da Cututtuka Masu Yaduwa ta Najeriya (NCDC) wadda ke da alhakin dakile yaduwar cututtuka a kasar.

Hukumar da ma wasu masu sa ido a kan lamarin sun yi nuni da cewa rashin gano wanda ya harbu da cutar a jihar ta Kogi yana da nasaba da sakacin da ake zargin gwamnatin jihar da yi wurin kafa cibiyoyin gwaje-gwaje da kuma bin ka’idojin da aka shimfida. Sun bayyana cewa hakan yana iya jawo yaduwar cutar ba tare da masaniya ba.

Gwamnatin jihar ta Kogi dai ta yi watsi da irin wadannan bayanan tana zargin cewa tana fuskantar matsin lamba saboda ta bayyana alkaluman bogi da kuma siyasantar da lamarin.

‘Ba sabon abu ba ne…’

Ta kuma kara da cewa sabanin zarge-zargen da ake yi cewa ta yi wa lamarin rikon sakainar kashi, gwamnatin ba sabon shiga ba ce wurin yakar cututtuka masu yaduwa.

“Mu ba sabbin yankan rake ba ne wajen tunkarar matsalar kare lafiyar al’umma, duk da cewa babu tantama COVID-19 babbar annoba ce da duniya ba ta taba ganin irinta ba.

“Duk shekara sai mun yaki zazzabin Lassa saboda jiharmu tana yankin da cutar tafi kamari, kuma mun samu wadanda suka harbu har ma da wadanda suka rasa rayukansu.

“Mu ne jiha ta farko da ta kafa dakin binciken cutar Lassa a duk fadin Najeriya”, inji Kwamishinan lafiya na jihar ta Kogi, Dokta Saka Haruna.

Ya yi nuni da cewa jihar ta samu kwarewa da kuma karin basira wajen dakile cututtuka masu yaduwa tun kafin bayyanar coronavirus.

Kowa ya iya allonsa…

Shi ma da yake jawabi ga jami’an hukumar NCDC da suka ziyarci jihar ranar Alhamis, Gwamna Yahaya Bello ya ce duk da raunin da ake danganta jihar da shi wanda ya sa duk shekara take samun cututtuka masu yaduwa da dama musamman zazzabin Lassa, jihar ta yi kokari sosai wurin warkar da kashi 100 cikin 100 tun shekarar 2017.

“Haka kuma, shekara da shekaru kafin bullar wannan cuta ta COVID-19, muna da kwamitin kar-ta-kwana na yaki da cututtuka masu yaduwa wanda ya kunshi kwararru daga dukkan bangarori.

“Don haka a daidai lokacin da NCDC ke bai wa jihohi darasi a kan yadda za su kafa kwamitocin kula da cutar, na jihar Kogi ya yi nisa da aiki”, inji gwamnan.

Gwamna Bello ya ce hakan ya bai wa jihar damar girke matakai tun kafin a ayyana cutar a mastayin annoba.

Za a iya tunawa gwamnatin jihar ta kaddamar da wani kwamitin cika-aiki da zai hana bullar cutar coronavirus yayain da yake kokarin kawar da zazzabin Lassa, wanda ya riga ya yi sanadin rasa rayuka a jihar bana.

Kwamitin cika-aiki

Kwamitin ya kuma samar da wata manhaja da ke iya taimakawa wajen tantance hadarin da ake fuskanta na kamuwa da COVID-19.

Gwamna Bello ya ce manhajar ta samu karbuwa kuma ta yi tasiri wajen “kawar da fargaba game da wata bakuwar cuta mai saurin kisa a tsakanin al’ummar jihar”.

“Sama da mutane 200,000 ne suka yi amfani da wannan manhajar a fadin jihar, sama da 14,000 kuma suka tantance kansu, inda aka samu kadan daga ciki wadanda suke da wasu alamomi da ke bukatar karin bincike”, inji shi.

Ya kuma ce kwamishinan lafiya, wanda shi ne babban masani a kan cututtuka masu yaduwa a jihar, da sauran manyan jami’an lafiya da kansu suke bibiyar wasu daga cikin wadannan mutane don tabbatar da ko alamomin da suka nuna na cutae ne.

Ya ce hakan ya taimaka wa jihar tabbatar da cewa babu wanda yake dauke da cutar har zuwa yanzu.

Tsarin wayar da kai

Bayan wadannan matakan, gwamnan ya ce gwamnatin jihar ta samar da wani tsari na wayar da kai a kan ba da tazara tsakanin jama’a, wanke hannu da kuma sauran matakan da akan gindaya don kauwce wa harbuwa da cutar.

“Ma’aikatar Lafiya ta jihar Kogi ta tura ma’aikatan lafiya zuwa yankunan mazabu 239 na jihar, mutum biyu kowace mazaba, wadanda suke wayar wa al’umma kai a kan hadarin cutar.

“Suna kuma kai bayanai da labaran wadanda ake zargin sun harbu zuwa kwamitin dakile cutar don a gudanar da bincike.

“Mun samar da cibiyoyi uku na zamani saboda killace wadanda ka iya harbuwa da cutar, wadanda ke da jimillar gado 130.

“Har yanzu cibiyoyin ba su fara aiki ba. Muna fatan kuma mun kuduri aniyar cewa wadannan cibiyoyin za su ci gaba da kasancewa a rufe ba tare an kai kowa ba har annobar ta wuce.

“Mun samar da lambobin waya na ko ta kwana wadanda ake kira kyauta saboda al’umma su kira su ba da rahoto idan an samu wanda ake zargi ya kamu da cutar COVID-19.

“Mun karbi kira daga mutane da yawa ta layin. Dukkan kiran da muka samu mun bincika kuma mun gano cika sharuddan yin gwaji na NCDC ba.

“Saboda haka, ba za mu iya kirkiro alkaluma mu gabatar ba saboda kawai muna so mu shiga cikin jerin jihohin da aka samu cutar.

“A matsayina na gwamna, na ji cewa akwai wasu fa’idoji da ake samu idan aka samu wanda ya harbu da cutar a jiha, amma ni ba ni da bukata”, inji Gwamna Yahaya Bello.

Sa-in-sa

Tuni dai takaddama ta barke game da ziyarar ta jami’an na NCDC zuwa Kogi, wadanda aka ce sun tafi ba tare da sun aiwatar da abin da ya kai su ba, wato tantance halin da ake ciki game da yaduwar coronavirus a jihar.

Sai dai kuma babu tabbas a kan dalilin barin su jihar – saboda Gwamna Yahaya Bello ya umarci a killace su na tsawon mako biyu ko ayi musu gwaji ko su bar jihar ne ko kuwa?

Abin jira a gani dai shi ne gwamnatin jihar Kogi ke da gaskiya a kan wannan lamari ko kuma masu nuna shakku, musamman hukumomin lafiya na tarayya.