‘Yadda muka kubuta daga kisan Abuja’

A makon da ya gabata ne jami’an tsaro suka kai wa wani gida a Apo kusa da gidajen ‘yan majalisun tarayya da ke Abuja farmaki inda suka kashe wadansu matasa tare da raunata wadansu da dama da sunan wai ‘yan Boko Haram ne. Aminiya ta bi diddigin lamarin, inda ta zanta da wadanda ke kwance […]

‘Yadda muka kubuta daga kisan Abuja’

Wasu daga cikin majinyatan a Asibitin AsokoroA makon da ya gabata ne jami’an tsaro suka kai wa wani gida a Apo kusa da gidajen ‘yan majalisun tarayya da ke Abuja farmaki inda suka kashe wadansu matasa tare da raunata wadansu da dama da sunan wai ‘yan Boko Haram ne. Aminiya ta bi diddigin lamarin, inda ta zanta da wadanda ke kwance a Asibiti da kuma lauyansu.
Ibrahim Muhammad,  mai shekara 25, wanda dan asalin garin Moriki ne a karamar Hukumar Zurmi ta jihar Zamfara, da ke sana’ar sayar da takalma, ya ce, ya share kamar shekara uku yana kwana a gidan, inda ya ke biyan maigadin gidan Joseph, wani dan asalin kudancin Kaduna, Naira 200 a kowane mako. Ya bayyana cewa al’amarin ya faro ne bayan wadansu ’yan bola sun yi wa gidan kutse a ranar Larabar  makon jiya, inda suka yanki wayar jikin ginin gidan tare da daukar kwanukan abinci guda uku na wata mai sayar da abinci:“Daga bisani maigadin gidan ya kama  ya gabatar da su wajen wani mai shayi da ke kusa da wajen, a lokacin ne kuma mai gidan ya garzayo wajen, bayan ya sanar da shi al’amarn ta waya, ya bukaci da a sake su, kuma ya bada umarnin cewa kowa ya bar gidan cikin mako guda. Amma kashegari, watau ranar Alhamis da tsakar dare a lokacin da muke barci, sai kawai mu ka ji harbi ta ko’ina, nan kowa ya ruga, wadansu suka mutu, wadansu suka jikkata, wadansu kuma har yanzu ba’a san halin da suke ciki ba.’’
Sani Usman kuwa mai shekara 18, shi ma dan asalin garin Moriki ne, daga Jihar Zamfara, da ke sana’ar sayar da kayan salad, wanda shi kadai ne a cikin majinyata 11 da aka kai Asibitin Wuse, kasancewar gado ya kare a asibitin Asokoro, ya ce watansa guda ke nan a gidan bayan ya zo Abuja, kuma an harbe shi ne a duwawunsa a lokacin da ya tashi a kidime bayan ya ji harbe-harbe.
Shi kuma Sani Abdurrahman mai shekara 24 da ke sayar da kayan miya a kasuwar Garki, wanda dan asalin karamar Hukumar Safana ne ta jihar Katsina, da lamarin ya rutsa da shi mako guda bayan dawowarsa daga gida, ya ce bayan an harbe shi, ya rarrafa ya kwanta a karkashin wani Keke Napep har zuwa wayewar gari lokacin da ’yansanda suka zo su ka dauke shi zuwa asibiti.
Daya daga cikin majinyatan a Asibitin Asokoro da ke AbujaAbubakar Auwal kuma, mai shekara 18 da haihuwa da ke sana’ar tura baro, wanda dan asalin garin Bichi ne da ke jihar Kano, ya ce ya share kamar wata bakwai a gidan. Kuma an harbe shi ne a lokacin da ya fito don gudun kada a zo a kama shi, sai kawai ya ji harbi a sawunsa; “a nan na yi ta ja da kafa har dai karfina ya kare, na fadi.’’
‘….Mu ba ’yan Boko Haram ba ne, kazafi akai mana’
Wadannan matasan da su ka tsira daga farmakin da jami’an tsaro na farin kaya (SSS) da kuma sojoji su ka kai a makwancinsu da ke kusa da Unguwar ’yan majalisar tarayya da ke Apo Abuja, sun bayyana cewa bayanin da wadansu matasa guda biyu da jami’an tsaro na farin kaya (SSS) su ka gabatar  suna cewa su ’yan Boko Haram ne a matsayin kazafi.
Haka nan sun ce ’yan uwansu  7 da aka kashe a yayin farmakin da tsakar dare ranar Alhamis da ya gabata, da ma wanda ya rasu a asibiti daga baya, matasa ne da ke gudanar da sana’o’i daban-daban a Birnin Tarayya. Sun ce ba su mallaki makami ba bare su yi musayar wuta a lokacin da a ka kawo harin, kamar yadda  jami’an tsaron su ka bayyana a lokacin da suka gabatr da matasa biyun,a matsayin dalilinsu na bude wuta.
Matasan, wadanda yawancinsu harbin bindigar ya same su ne a duwawu ko a kafa , su goma sha  daya ne (11)  har zuwa ranar Litinin da ta gabata lokacin da Wakilinmu ya koma Asibitin Asokoro inda aka kwantar da mutum goma a wajen, a yayin da guda dayansu kuma aka kai shi Asibitin Wuse. Cikon na 12 mai suna Nasiru Adamu  daga Jihar Zamfara, wanda aka harba a ciki ya cika a cikin daren ranar Lahadin da ya gabata, bayan an yi masa aiki tare da kwantar da shi a bangaren kulawa na musamman da ke Asibitin na Asokoro.
A yayin zantawarsu da wakilinmu, majinyatan, wadanda har zuwa daren ranar  Litinin da ya gabata sun ce ba a cire musu harsasan da ke jikinsu ba, illa banda bandeji da aka sa a wuraren raunukan tare da ledar karin ruwa da aka sa musu,
sun ce su da sauran wadanda aka kashen wadanda ke kwana a gidan sun haura dari, wadanda suka hada Musulmai da Kirista masu sana’o’i daban daban, inda a kowane mako su ke bai wa mai gadin wajen, wani mai suna Joseph, dan asalin kudancin Kaduna, Naira 200, sun ce wasunsu da su aka yi aikin leburancin gina gidan.
. Sun bayyana cewa, bayan wayewar gari ’yan sandan da ke cikin tawagar wadansu ma’aikata daga ofishin Ma’aikatar Kula da yankin Birnin Tarayya Abuja  sun kawo musu dauki inda suka dauke su zuwa Asibiti  tare da wadanda suka samu munanan raunuka saboda harbi su 7 da suka rasu, wadanda su ma aka dauki gawarwakinsu zuwa Asibitin a lokaci guda.
Barista Sanusi Musa a yayin da ya ke zantawa da wakilinmu Majinyatan sun kuma bayyana cewa,  wani dan uwansu ya zo musu da wata jarida a ranar Asabar da ta gabata mai dauke da hoton wadansu matasa guda biyu cikin ankwa, wadanda aka bayyana ma su cewa, jami’an tsaron sun gurfanar da su a gaban gidan da abun ya faru ga ’yan jarida da suka yi ikirarin cewa su ‘yan Boko Haram ne da ke zaune a wajen. Sun ce wadannan mutanen biyun ba sa cikin wadanda ke kwana a gidan kuma bas u da wata alaka da wajen a iya saninsu, kuma bayanin da suka yi kazafi ne, ba gaskiya ba ne.
Shi ma jagorar kare hakkin dan Adam Shehu Sani ya ce yaki da jami’an tsaro suka ce suna yi da ‘yan ta’adda ba hujja ba ne da za su rika amfani da ita wajen halaka bayin Allah a kasar nan kamar abin da ya faru a Apo.
Ya ce, ‘’mun gansu cewa wadannan matasan da aka kashe ba ‘yan ta’adda ba ne kamar yadda jami’an tsaro suke yadawa, illa bayin Allah ne da suke zaune a gidan aka je aka halaka su. Matsalar ta’addancin da muke fama da shi a Arewa ai ya samu asali ne a shekarar 2009 lokacin da jami’an tsaro suka aikata irin wannan kisan gilla. Ga alama dai har yanzu kasar nan ba ta daddara ba.’’
‘’Saboda haka mun ziyarci wajen mun kuma ga abin da muka gani da kuma abin da muka ji. Saboda haka abin da muke so a yanzu shi ne gwamnatin tarayya ta kafa kwamitin bincike  domin binciko ainihin abin da ya faru a wannan gidan domin a samu damar kamo wadanda suka aikata wannan aika-aika don a hukunta su.’’
A zantawarsa da Wakilinmu, daya daga cikin lauyoyin matasan mai suna Barisata Sanusi Musa, ya ce da zarar sun kammala bincikensu  za su shigar da kara a gaban koto don neman hakki ga mamatan da kuma majinyatan. Ya ce zancen danganta al’amarin da Boko Haram bayan kisa da kuma raunata wadansu, abu ne wanda hankali ba zai dauka ba, kuma ya saba wa shari’a. Ya ce idan ’yan Boko Haram na zama a gidan a wadansu lokuta, al’amari ne da ya kamata ya je ga mai gadin gidan da kuma shi kansa mai gidan, ba wadanda ke kwana a ciki ba.
Kuma bayanin da ya samu shi ne a cikin daren da aka kai harin mai gadin bai kwana a gidan  ba, haka nan wadansu mutane na kusa da shi. Ya ce kuma akwai ayar tambaya a game da rashin rusa gidan kamar yadda ake yi ga duk gidan da aka gano yana da alaka da Boko Haram. Sannan kuma jami’an tsaron ba su nuna wa duniya makaman da suka gano ko kuma inda suka ce an binnesu ba.
Shi ma a nasa tsokacin da ya yi, wani jami’in Hukumar Kare Hakkin bil’Adama ta kasa  (N.H.R.C), mai suna Barista Salihu Bobbo, ya ce hukumarsu ta kammala na wuccin-gadi a ranar Litinin da ta gabata inda take jiran sanya hannun babban jami’in zantarwa na hukumar, “daga nan ne ne kuma matakin gaggawa zai fara don samar da adalci ga wadanda al’amarin ya rutsa da su.’’
Kwamared Shehu Sani (na farko daga hagu) yana addu’a ga wadanda aka kashe a Apo, AbujaWakilimu ya samu labarin cewa, tuni aka dauki daukacin gawarwakin mamatan daga asibitin, inda aka binne wasunsu a  Abuja, yayin da wadansu kuma aka wuce da su jihohinsu, bayan hukumomi a Ma’aikatar kula da Birnin Tarayya, sun samar da motocin da suka dauke su zuwa yankunansu.
Wani dan majalisar dattawa daga jihar Zamfara Sanata Sahabi Ya’u da kuma dan majalisar wakilai Honorabul Bilyaminu Shinkafi sun ziyarce majinyatan tare da alkawarin bi musu hakki, domin yawancinsu ’yan cirani ne daga jihar Zamfara, a yayin da wadanda aka kashe  kuma yawancinsu ’yan Katsina ne.
A halin yanzu majalisar dattawa ta umarci kwamitocin kula da tsaron kasa da binciken sirri da kuma na shari’a da doka su  binciko mata yadda yi wannan al’amarin ya faru har mutane suka rasa rayukansu, wadansu kuma jikkata, inda aka bas u mako guda su mika rahotonsu.
Ta yanke wannan shawarar ce a sakamakon kudurin da Sanata Sahabi Alhaji Ya’u (PDP Zamfara) ya gabatar, inda ya nuna cewa ya damu kwarai da mabambantan bayanan da ake bayarwa game da kisan mutanen guda takwas, mafi yawansu masu tuka babura masu taya uku kuma mafi yawansu sun fito ne daga jihohin Zamfara da Katsina da kuma Kano.

Sunayen mamata zuwa ranar  Litinin
1.  Mamman Abdullahi (Katsina)
2.  Nura Abdullahi (Katsina)
3.  Ashiru Musa (Katsina)
4.  Sulaiman Imran (Katsina)
5.  Musa Damaturu (Yobe)
6.  Buhari Ibrahim (Kano)
7.  Ahmad Musa (Zamfara)
8.  Nasiru Adamu (Zamfara)

Majinyata da shekarunsu da sana’a da kuma ’yankunansu na asali.
1.    Ibrahim Aliyu, 25 Mesin,Qaura Zamfara
2.     Nuhu Ibrahim, 23, kayan miya, Zamfara.
3.    Ibrahim Muhammad, 25, Takalma, Zurmi Zamfara.
4.    Murtala Salihu 20, Markaxe, Zamfara.
5.    Murtala Abubakar, 21, Markaxe Zamfara.
6.     Sani Usman, 18, Salad, Moriki Zamfara.
7.    Yusuf Abubakar, 22, Barrow, Moriki Zamfara.
8.    Abubakar Auwal, 18, wankin mota, Bichi Kano.
9.    Ibrahim Bala, 20, Ruwan leda, Bichi Kano.
10.    Sani Abdullahi, 24, Waifan mota, Safana Katsina.
11.    Yahaya Bello, 20, Waifan Mota, Safana Katsina.

Waxanda ba a san halin da suke ciki ba
Sani Haruna.
Ado Isa.
Abdullahi Sa’adu.
Yasinu Gado.