Yadda muka kwashe da masu bukatar sake fasalin kasa – Tafida Mafindi
A yayin da yekuwar neman a sake fasalta tsarin kasar nan ke kara zafafa musamman daga manyan mutanen Kudu, Aminiya ta zanta da Alhaji Isa Tafida Mafindi wanda ya halarci Taron kasa na bayan nan, inda ya bayyana kiraye-kirayen a matsayin munafunci tare da yin bayani a kan hakikanin manufar masu bukatar a yanzu: Aminiya: […]
A yayin da yekuwar neman a sake fasalta tsarin kasar nan ke kara zafafa musamman daga manyan mutanen Kudu, Aminiya ta zanta da Alhaji Isa Tafida Mafindi wanda ya halarci Taron kasa na bayan nan, inda ya bayyana kiraye-kirayen a matsayin munafunci tare da yin bayani a kan hakikanin manufar masu bukatar a yanzu:
Aminiya: Magabatan wasu sasan kasar nan suna yekuwar a sake fasalta kasar nan, me kake ji ya sa suke kiraye-kirayen?
Bukatar a sake fasalta tsarin kasa wani shiryayyen munafunci ne da Turawa suke cewa “democracy is hypocrisy” ma’ana dimokuradiyya ta gaji munafunci. In ba haka ba ga abin da mutum ke bukata a yi masa, amma maimakon ya fito fili ya bayyana bukatar sai ya rika kewaye-kewaye. Shi wannan tsarin mulki da muke kai wadanda suke ta korafin sai a rage karfin Gwamnatin Tarayya ta fuskar doka da iko a kan arzikin kasa tare da kara shi ga jihohi, ba su ne musabbabinsa ba. Ai daga baya ne aka rika sauya masa fasali kafin ya ragu daga yadda suka tsara shi a farko. A lokacin Shugaban kasa Janar Ironsi ne aka dauko daya daga cikin masu korafin a sauya tsarin mulkin nan a yanzu wato Farfesa Nwabuze ya jagorancin kwamitin tsara wannan fasali saboda wanccan gwamnatin tana ganin nata ne. A wancan tsarin sun ba da karfin iko fiye da kima ga Shugaban kasa shi kadai ba wai Gwamnatin Tarayya a dunkule ba, sannan suka karbe ikon arzikin kasa daga hannun gwamnatocin yankuna zuwa ga tarayya wanda suka kira “Unitification.” A lokacin gudunmawar da yankin Arewa ke bayarwa ya dara na kowane yanki. To daga baya ne bayan Shugaban kasa Janar Gowon ya karbi mulki ya fara sauya shi har zuwa matakin da yake a yanzu.
daga baya-bayan nan a lokacin Shugaban kasa Goodluck Jonathan an yi yunkurin sauya fasalin tsarin mulkin, wanda ni kaina mamba ne a ciki. An yi tsare-tsare da dama amma a karshe sai ta bayyana cewa ikon sake fasalta tsarin kasar nan dole sai ya bi wani tsari kamar yadda kundin tsarin mulki ya tanada. Shi ne kuma ta hanyar mika duk wata bukata ga wakilan Majalisar dokoki ta kasa don yin muhawara a kai, idan bukatar ta samu amincewar kashi biyu a cikin uku shi ke nan sai a mika shi ga majalisun dokoki na jhohi, a can ma idan aka samu amincewar kashi biyu a cikin uku, sai a mika shi ga Shugaban kasa don ya rattaba wa kudurin hannu, shi ke nan ya zama doka. Idan kuwa ya ki sai majalisa ta sake gabatar da lamarin a gabanta idan aka samu kashi biyu a cikin uku shi ke nan sai a yi amfani da dokar koda Shugaban kasa bai amince ba.
Yaya kuka tafiyar da kungiyoyin jama’a da suka kawo irin wannan bukata a Taron kasa?
Ba shakka kungiyoyi daban-daban sun kawo mana wadannan bukatu amma duk mun samu hanyoyi da muka magance su. daga cikinsu akwai wata kungiya daga Kudu maso Gabas da suka bukaci a kara masu jiha daya a yankinsu. Sun yi korafin cewa yankuna 6 na kasar nan kowannensu na da jihohi 6 sannan na bangaren Arewa ta Yamma na da 7 a yayin da yankinsu kadai ne ke da jihohi 5. Gaba dayanmu sai muka amince musu da bukatarsu tare da neman su bi tsarin da ake bi na neman jiha a tsarin dimokuradiyya da ake kai wanda shi ne ta hannun Majalisar dokoki ta kasa ko kuma ta Majalisar kasa wadda gwamnoninsu ke matsayin wakilai. Sai kuma wata kungiiyarsu ta MASSOB da ta ce ita so take a bai wa yankinsu damar cin gashin kanta tare da kafa kasa. Muka ce musu babu matsala, sai dai kafin nan sai da wani mai hikima a kwamitin ya jefa musu wata tambaya inda ya kalubalance su da su aiwatar da kidayar gidaje da kadarorin wasu kabiilu da ke yankunansu, kuma su kidaya na kabilarsu a sauran yankunan kasar nan, su kawo mana rahoto. In ya so bayan nan sai su wuce yankunansu, ba mai hana su ware kasarsu shawara ta rage gare su. To a nan ne suka tashi suka ba mu waje ba mu sake jinsu ba. Mun yi muhawurori iri-iri masu zafi, wasu muhawarorin idan za a yi sai an fitar da ’yan jarida daga wajen taron tukuna saboda zafinsu.
To ba ka ganin rashin amfani da kudirorin wancan kwamitin ne ya sa ake ta kiraye-kirayen a yanzu?
Kai dai munafuncin dodo ne da aka ce yakan ci mai shi. Ai wanda ke gaba-gaba a wajen kiraye-kirayen a rage karfin ikon Gwamnatin Tarayyar a yanzu shi ne ya jagoranci zaman sauya tsarin da ya ba da karfin iko ga Gwamnatin Tarayya a baya, wato Farfesan Shari’a Nwabuze a lokacin Shugaban kasa Ironsi kamar yadda na yi bayani a baya. Bari in yi msali da abu guda da mutanen nan ke neman a yi. Ni da kai daga jihohin Arewa maso Gabas muka fito, shin yaya lamura za su kasance idan aka soke daukacin jihohin yankin sannan aka koma jiha guda daya kacal da ke da hedikwata a Maiduguri, kana ganin hakan zai yiwu? A duba jama’ar da suka rasa rayukansu a lokacin neman karin jihohin nan bayan kai-komo da wadanda suka mutu a yayin bukukuwan samun jhohin, sannan yaya za a yi da tarin cibiyoyin gwamnati da aka kakkafa a jihohin? Ka ga wannan abu ne da ba zai yiwu ba gaba daya ya kasance sun tafi a banza, a koma tsarin baya alhali kullum ci gaba ake nema tare da kara kusantar da gwamnati ga jama’a ba kara nisantar da su ba.
Kana ganin za su samu nasarar cimma burinsu idan suka bi ta hanyar Majalisar kasa da suka ce ’yan Arewa sun yi babakere?
Me zai hana, sai dai idan ba su bi ka’ida ba. Gwamnoninsu suna halartar tarurrukan Majalisar kasa, sannan a bangaren Majalisar dokoki ta kasa suna da wakilai, su mika korafin mana a daya daga cikin kafofin nan biyu. Kai dai al’amari ne irin na zamantakewar mutanen Kudu, inda yara suke shiga gaba, su kuma manya da suka san tsarin al’amura sai su sa musu ido ba dama su tsawatar musu. Sannan wani abu da suka gaza gani ko kin magana a kai, shi ne wannan tsari da ake bi a yanzu Arewa ce ake dannewa. Saboda idan ka dubi girman jihohin Kudu maso Gabas din nan gaba dayansu ba su wuce jihohin Borno da Yobe ba idan aka hade su. Amma idan aka zo batun yawan ma’aikata a ma’akatun gwamnati sai ka ga su ne suka mamaye ko’ina duk da tsarin raba- daidai da ake da shi.