Yadda muka magance matsalar ‘yan damfara – Hukumar NAHCON
Ba kamar yadda abin ke faruwa a wasu qasashe da yawa ba, Hukumar Kula Da Al’amuran Aikin Hajji Ta Najeriya (NAHCON) ya zuwa yanzu ba ta samu rahoton damfara daga kamfanonin aikin Hajji da Umrah masu zaman kansu , a yayin gudanar da aikin Hajjin bana ba. Hukumar, wacce ita ce jagorar kula da al’amuran […]
Ba kamar yadda abin ke faruwa a wasu qasashe da yawa ba, Hukumar Kula Da Al’amuran Aikin Hajji Ta Najeriya (NAHCON) ya zuwa yanzu ba ta samu rahoton damfara daga kamfanonin aikin Hajji da Umrah masu zaman kansu , a yayin gudanar da aikin Hajjin bana ba.
Hukumar, wacce ita ce jagorar kula da al’amuran aikin Hajji da Umrah a Najeriya, tana kula sosai da yadda al’amuran kamfanonin Hajji da Umrah masu zaman kansu da kuma Hukumomin Aikin Hajji na jihohi suke gudanar da al’amuransu a Najeriya, haka kuma tana aiki wurjanjan wajen fadakarwa da yaqi da bara-gurbin kamfanonin da ke damfarar maniyyata Hajji da Umrah, suna raba su da
dukiyoyinsu.
Hukumar NAHCON ta riqa yin hadin gwiwa da hukumomin tsaro, kamar EFCC da ICPC wajen gudanar da ayyukanta, wanda haka ya taimaka gaya wajen rage ko daqile ayyukan ’yan damfara.
Wadannan hukumomin tsaro biyu, sun yi nasarar gurfanarwa da hukunta wasu kamfanonin gudanar da aikin Hajji da Umrah na bogi, wadanda aka samu da halayen damfara, inda wasu ma aka yi nasarar kulle su a gidan yari.
Idan za a iya tunawa, hukumar ta samu nasarar samun umurnin kotu, inda ta rufe kamfanonin bogi guda 123 da suke gudanar da harkokin aikin Hajji da Umrah ba bisa qa’ida ba a wasu sassa na qasar nan.
A lokacin da yake bayani game da nasarorin da hukumar ta samu, Shugaban Sashin Kula Da Kamfanonin Zirga-Zirga, Alidu Shutti ya danganta nasarorin da hukumar ke samu bisa tsare-tsaren da ta dauka. Kamar yadda ya ce, bincike a kai-a kai da jami’an hukumar ke gudanarwa a kamfanonin domin tantance yadda suke gudanar da ayyukansu, da tabbatar da cewa suna bin tsarin doka, sun taimaka wajen samun nasarar hukumar. Ya qara da cewa yawan musharaqa da hukumar ke yi da qungiyar kamfanonin gudanar da zirga-zirgar aikin Hajji da Umrah (AHUON) ya ba hukumar tasu da su kansu kamfanoin damar tattaunawa da musayar dubaru dangane da al’amuran ayyukansu. Ya ce wallafa sunayen kamfanonin aikin Hajji da Umrah da hukuma ta amince da su a jaridun qasar nan da hukumarsu take yi, ya taimaka wajen wayar da kan al’umma, wajen rage ayyukan ‘yan damfara a fannin, a qasar nan.