Yadda muka rabu da ‘yan uwanmu da suka rasu a Makka – Dangin Mamatan

Biyo bayan hadarin da aka samu a Masallacin Harami na Makka da ya yi sanadiyar rasa rayukan mutane fiye da dari ciki har da ‘yan asalin jihar Gombe guda hudu, Aminiya ta bi diddigon kauyukan wadanda lamarin ya shafa don ganawa da ‘yan uwansu kan yadda suka samu labarin rasuwar dangin nasuA kauyen Kombi da […]

Yadda muka rabu da ‘yan uwanmu da suka rasu a Makka – Dangin Mamatan

Biyo bayan hadarin da aka samu a Masallacin Harami na Makka da ya yi sanadiyar rasa rayukan mutane fiye da dari ciki har da ‘yan asalin jihar Gombe guda hudu, Aminiya ta bi diddigon kauyukan wadanda lamarin ya shafa don ganawa da ‘yan uwansu kan yadda suka samu labarin rasuwar dangin nasu
A kauyen Kombi da ke karamar hukumar Dukku Aminiya ta zanta da Sarkin Kombi Muhammad Magaji Sambo, wanda matarsa Ladi Mai Bille, tana daga cikin wadanda suka rasu, inda ya bayyana cewa, kafin ta tafi Makka sai da ta tara ‘ya’yanta guda 11 ta raba musu duk abun da ta mallaka, sannan kuma ta zagaya ta samu dukkan makwabta ta yi musu bankwana ta ce su yafe mata. ‘’Matata Ladidi Mai Bille, a shekarar da ta gabata ne na biya mata kujera amma Allah bai kira ta ba sai bana, amma kafin ta tafi ta raba wa ‘ya’yanta abun da ta mallaka, ni kuma na rubuta na ajiye mu ga lokacin dawowarta, ko za ta dawo ko ba za ta dawo ba, sai kuwa ga ta Allah ta kasance a kanta.’’
Ya ce dalilin rubutawa ya ajiye shi ,ne idan Allah Ya dauki ranta a can sai ya tuntubi Malamai ya ji ko wannan rabon da ta yi ya yi daidai ko za’a sake.
A cewar Sarkin Kombi, Ladidi ita ce uwargida a cikin matansa, kuma shekaranta 40 ‘ya’yanta 11, jikoki 4, manya daga cikin ‘ya’yanta 7 sun yi kuka sosai da suka samu labarin rasuwarta.
Ya kara da cewa, a lokacin da take kasa mai tsarki ta bugo masa waya lokacin shi kuma yana Abuja ta ce a hada ta da kishiryarta su gaisa haka kuma ya sa wani yaro ya je ya kai mata suka gaisa din, amma bai san me suka tattauna ba, sai dai ya san akwai kyakyawan zaman lafiya a tsakninsu, don ko sau daya ba su taba fada ba.
A kauyen Garin Malam Manzo kuma da ke karamar hukumar Akko, Aminiya ta samu jin ta bakin Alhaji Abubakar Abba, wanda shi ma matarsa Aishatu Alhaji Buba (Adda)  lamarin ya rutsa da ita, inda ya ce shi kam yana ganin gidansa zai tarwatse ke nan domin ita ke kula da rabin gidan.
Alhaji Abubakar Abba, ya ce a ranar wata Juma’a da matar tasa za ta fita daga gida ta tafi aikin Hajji ta shiga dakinsa sun yi bankwana, inda ta fara ba shi tarihin rayuwar aurensu na shekaru 25 da suka haifi ‘ya’ya biyar, ya ce mata haka ne. Sai nan take Aishatu (Adda) ta ce maigidan na yafe maka duk abun da na san ya shiga tsakaninmu, da wanda ban sani ba, haka shi ma sai ya ce Adda na yafe miki. Tana fita ya ce sai ya fara ganin gidan yana masa baki-baki.
Ya ce a cikin matansa uku ita Adda ce ta uku, amma ita ta fi kulawa da gidansa, duk garin kowa ya san hakan, sai ga shi yanzu ta mutu, don haka yake ganin gidansa zai waste, don babu mai kula masa da gida.
Alhaji Abubakar Abba, ya ce yana samun labarin rasuwarta kwanansa uku ba ci ba sha, barci ma ya gagare sh,i har jama’a suna ce masa ya aka yi ya rame.     
Ya ce ita ta biya wa kanta wannan kudin aikin Hajji ba shi ne ya biya mata ba, domin tana da tattali, shanunta ta sayar da wadansu kadarori. Allah Ya jikan Adda. Amma ya ce da ya tuna a kasa mai tsaki ta rasu a dakin Ka’abah, sai dadi kuma ya cika shi, domin yana yi mata  tsammanin samun rahama.
A garin Birin Bolawa kuwa ta karamar hukumar Nafada, Adamu Malam Hamma shi ne mijin marigayiya Innawuro Amadu Biri, ‘yar shekara 60, ya yi bayani ne cikin  jimami da bakin ciki da magagin tsufa, inda dakyar maganarsa take fita, ya ce hankalinsu ya tashi kwarai da gaske da suka samun labarin rasuwar   mai dakin nasa.
Ya ce Innawuro ita kadai ce matarsa kuma shekarunta 60, tana da ‘ya daya da jikoki 7, ‘’jin mutuwarta ya kara daga mun hankali. Na ji zafi sosai na mutawar mai dakina Innawuro, sai dai ina yi mata fatan alheri da saduwa da rahamar Ubangiji, kasancewar ta rasu ne a wurin aikin Hajji a kasa mai tsarki.
A jihar Kaduna kuma, Wakilimu ya ziyarci Unguwar Doka da ke Kargi a karamar hukumar Kubau da ke jihar Kaduna domin ganawa da iyalan marigayi Alhaji Shu’aibu Adamu Kargi wanda shi ma ya rasu a hadarin na Saudiyya. Inda ya fara da yayansa wanda ya yi bayani kamar haka; ’’ Sunana Alhaji Zubairu Adamu, ni yayan marigayi ne, uwanmu daya ubanmu daya.
Mun samu labarin rasuwar dan uwanmu ne ta hanyar labarai cewa an yi hadari a Makka, sai muka buga lambarsa domin mu ji halin da yake ciki, kasancewar ya sanar da mu cewa yana Makka. mun buga lambar amma idan ta shiga ba a dauka, sai hankalinmu ya fara tashi, muka fara shiga damuwa. Da gari ya waye sai muka tafi wani kauye kusa da mu don samun lambar abokan tafiyarsa, domin mu ji halin da suke ciki, sai daya daga cikinsu ya sanar da mu cewa tare suka tafi harami domin yin dawafi, bayan sun gama sai ya ce shi zai tsaya domin ya cigaba da ibada, kawai sai suka ji wannan abin ya faru, kuma daman dakin  kwanansu daya da shi tunda suka ga bai dawo ba sai suka kaddara cewa wani abu ya faru, to daga baya sai aka sanar da su rasuwarsa, haka dan uwan tafiyarsa ya sanar da mu. Bayan kwana uku da faruwar lamarin sai aka turo wani wakili daga Hukumar alhazai ta jihar Kaduna dauke da wata takarda da take sanar da mu a hukumance cewa dan uwanmu Allah Ya yi masa rasuwa. To ka ji yadda aka yi muka samu labarin.
A bara marigayi Alhaji Shu’aibu ya biya kudin tafiya Makka Naira dubu dari bakwai da hudu, amma bisa hukuncin Allah bai kaddara ya tafi ba, sai a wannan karon Allah Ya kaddara da yake kwanansa ya kare.
Marigayi manomi ne kuma malamin addini ne kuma direban mota ne, mutum ne mai son jama’a, ya rasu ya bar mata biyu tare da yara goma, kuma shekarun marigayi arba’in da haihuwa.
Aminiya ta ji ta bakin matansa biyu, inda uwargidansa mai suna Zainab ta ce,’’ Shekarunmu goma tare kuma muna da yara hudu da shi, mun yi zaman jin dadi tare kuma mun rabu cikin annashuwa, kwatsam sai muka samu labarin rasuwarsa, gaba daya rayuwa ta zama babu dadi, muna fatan Allah Ya gafarta masa.
Ita ma amaryarsa mai suna Hajara, cikin kuka ta yi wa wakilinmu bayanin yadda suka rabu da maigidanta, ’ kafin ya tafi duk sai da ya tara mu ya yi mana huduba, muka yafe wa juna, kwatsam sai muka ji labari mara dadi, amma daga baya sai muka fauwala wa Allah, domin muna masa kyakkyawan fata, mu ma muna neman Allah Ya hada mu da irin wannan rasuwar. shekaranmu biyar da aurenmu kuma muna da yara biyu tare da shi.’
Shugaban riko na karamar hukumar Kubau Ahmad Haruna Anchau ya ziyarci iyalan marigayin inda ya jajanta musu kuma ya ba su buhunan shinkafa biyu da na masara biyu da kudi Naira dubu goma. Ya ce ba su je da wuri ba ne saboda ba a sanar da su a rubuce ba, sai dai ya karanta ne a jarida.
Daga jihar Katsina kuma Ibrahim Bello dandume na daya daga cikin wadanda suka rasa rayukansu a sanadiyyar hadarin, sai dai kuma duk kokarin da Aminiya ta yi domin gano wadansu daga cikin ‘yan-uwansa a garin na dandume ko a Hukumar ta alhazai ta jihar Katsina ya ci tura, saboda jami’an Hukumar alhazan da za su ba da wani bayani suna kasar ta Saudiya.
An tuntubi shugaban kwamitin  alhazai na jihar Katsina Alhaji Salisu Ado Shinkafi(Bunun Katsina) inda ya tabbatar da mutuwar wannan mutum, amma ya ce su ma suna nan suna cigaba da bincike don samun karin bayani a kan shi Ibrahim Bello dandume din.
Alhaji Salisu ya ci gaba da cewa, baya ga marigayi Ibrahim,akwai wadansu mutane biyu mace da namiji da ke kwance a asibiti sanadiyar karaya da suka samu ta hanyar wannan hadari. Ya kara da cewa, akwai wadansu mata biyu da suka samu ‘yan kananan raunuka wadada nan take aka sallame su bayan an yi masu magani. Kamar yadda shugaban kwamitin ya tabbar,Ibrahim Bello dandume ne daga karamar hukumar ta dandume da ke jihar ta Katsina kadai ya rasa ransa sanadiyar wannan hadari na ranar jumma’ar da ta gabata da ya faru a Harami a kasar ta Saudiya.