Yadda muka rasa amarya da ’yan rakiyarta bakwai
Al’ummar Unguwar Tudun Nasara da ke garin Madalla ta karamar hukumar Suleja da ke Jihar Neja sun yini cikin farin ciki saboda bikin auren daya daga cikin ‘yan matan unguwar mai suna Aisha Adamu a ranar Asabar, amma sun kwana cikin bakin ciki da juyayi saboda a yayin kai amaryar gidan mijinta a garin Jama’are […]

Al’ummar Unguwar Tudun Nasara da ke garin Madalla ta karamar hukumar Suleja da ke Jihar Neja sun yini cikin farin ciki saboda bikin auren daya daga cikin ‘yan matan unguwar mai suna Aisha Adamu a ranar Asabar, amma sun kwana cikin bakin ciki da juyayi saboda a yayin kai amaryar gidan mijinta a garin Jama’are da ke jihar Bauchi, ta rasa ranta tare da ’yan mata hudu ‘yan unguwar da kuma wadansu mutanen uku, ciki har da direban motar kirar Honda da ke dauke da su, a sakamakon taho-mu-gama da motar ta yi da wata tankar mai a kusa da garin Gaya na jihar Kano.
Lokacin da wakilinmu ya ziyarci unguwar Tudun Nasara a ranar Litinin da ta gabata, ya tarar da mahaifin amaryar mai suna Alhaji Adamu Bajoga, tare da sauran iyayen ’yan matan cike da alhinin rashin da suka yi, inda jama’a daga wurare daban-daban suke ta zuwa gidan domin jajanta musu.
Alhaji Adamu Bajoga, wanda dan asalin Jihar Gombe ne, ya bayyana wa Aminiya cewa, ya shekara kamar 30 a garin na Madalla. Ya ce, angon ’yar tasa, wanda dan asalin garin Jama’are ne da ke jihar Bauchi, yana cikin wata mota bas mai daukar mutane 18, sai kuma wata motar kirar Golf da ke dauke da manyan mata daga bangaren amarya, a yayin da motar da ta yi hadarin kuma ke biye da motocin biyu. Ya ce kusan shekara biyu ke nan ’yar tasa ta hadu da angon nata wanda ke kasuwanci a garin Suleja ta jihar Neja, amma sai a ranar Asabar Allah Ya yi auren, a sakamakon dage bikin da aka rika yi a baya, inda suka bar garin jim kadan bayan an daura auren da misalin karfe 10 na safe.
Mahaifin amaryar ya ci gaba da cewa, ya yi ta yin waya da su a yayin tafiyar tasu, “bayan mun idar da sallar isha’i ne da daddare, sai aka yi min waya inda aka tambaye ni, ko na san mai lambar, na amsa da cewa, kwarai, sai aka ce to sun yi hadarin mota a bayan garin Gaya kusa da cibiyar NYSC, amma dai suna raye. “nan da nan na kira lambar kanwata, amma sai wani ne ya dauki wayar, inda ya shaida min cewa, shi dan sanda ne. Na hada shi da Allah da ya gaya min hakikanin halin da su ke ciki, to shi ne ya sanar da ni cewa lallai motar da su ke ciki ta yi hadari kuma daukacin mutanen da ke cikinta sun rasu.
Mahaifiyar amaryar mai suna Jummai, wadda ’yar asalin garin Jama’are ce, ta jima da rabuwa da mahaifin amaryar, sai dai daya daga cikin matan uban mai suna Rabi’atu Adamu, wadda kuma a wajenta ne amaryar ta girma, tana cikin manyan matan da ke cikin tawagar raka amaryar zuwa dakin mijinta tare da wata matar mahaifin amaryar, a yayin da ta ukunsu kuma ta kasance a gida tare da dangi da sauran yara.
Rabi’atu, wadda ke cike da jimami tare da sauran mata da ke kewaye da ita, ta shaida wa Aminiya cewa, kasancewar motarsu na gaba, ba su tashi sanin aukuwar hadarin ba sai bayan da aka yi musu waya daga gida Madalla, “a nan ne motarmu ta juyo, inda muka garzaya asibitin da aka kai su, kuma a daren ne aka dauki gawarwakinsu zuwa garin Jama’are, sai dai an jira zuwa wayewar asubahi sannan aka yi musu jana’iza, muka dawo gida Madalla da maraice tare da wadansu tawaga ta mazaje da ta je wajen bayan samun labarin abin da ya faru.
Da Aminya ta je wurin da aka yi hadarin motar ta gano cewa hadarin ya yi muni kwarai, domin wadansu daga cikin ‘yan rakiyar da hadarin ya rutsa da su, kansu daban gangar jikinsu daban, wadansu kuma sun rabe gida uku, yayin da wadansu kuma suka rabe gida biyu, fatar gadon bayansu kawai ta rike sauran jikin.
Masu karamin rauni sune wadanda kansu ya yi raga-raga, wuyansu ya karye, ko kuma suka samu karaya, asali ma dai, gaba dayan wadanda suka mutun kafin a yi musu wanka sai da likitoci suka yi musu wata dabara ta dinke su kafin a samu damar yi musu wanka a sanya su a cikin likkafani, kana aka yi musu sallah aka binne gawarwakinsu a makabarta.
Lokacin da wakillinmu ya ziyarci garin Jama’are ya lura cewa mutane da dama a cikin garin suna cikin juyayi da damuwa, mutuwar amaren ba mazauna garin Jama’are da kewaye kawai ta girgiza ba, za a iya cewa daukacin mutanen jahohin Jigawa da Kano sun girgiza, kasancewar hadarin ya auku ne a kan hanyar da mutanen jihohin Kano da Jigawa da Borno da Yobe suke zirga-zirga. Duk ya ga motocin a gefen hanya sai ya tambayi yadda al’amarin ya kasance, idan kuma ya ji yadda lamarin ya faru sai ya dimauce.
Alhaji Ibrahim Kawule kanin mahaifiyar amarya Aisha Adamu ne, ya ce mahaifiyar Aisha mutumiyar jama’are ce, mahaifinta kuma Alhaji Adamu mutumin Madalla ne da ke kusa da birnin tarayya Abuja, kuma auren shamsudeen da Aisha aure na hadin zumunci.
Alhaji Ibrahim Kawule ya kara da cewa, a lokacin da ya samu waya daga ‘yan sanda da ke Gaya hankalinsu ya tashi matuka, ya ce da kafin a tabbatar musu da mutuwar amaryar sai da ya sha tambayoyi a wajen ‘yansanda, daga bisani ne suka tabbatar masa da cewa duk wadanda suke cikin motar sun rasu
Ya ce, direban motar da ya dauko amaryar mai suna Musa Almajiri abokinsa ne, shi ma ya rasu tare da amaren.
Alhaji Kawule ya ce ‘yan sandan Gaya sun yi matukar burge shi, domin duk abin da yake cikin motar, tun daga kudin wadanda ke cikin motar zuwa sakon kudi da aka bai wa direban da kudin da yake jikin amarya da wayoyinsu da kayansu, babu abin da ya salwanta, ya ce hatta kudi da suka bai wa ‘yan sandan domin su zuba mai a motarsu lokacin da suka kawo gawarwakin Jama’are kin karba suka yi.
Kawun amaryar marigayiya Aisha Adamu ya ce a iyakar rayuwarsa bai taba ganin hadarin mota da ya tada masa da hankali ba kamar wanda ya rutsa da ‘yarsa Aisha ba, inda za ka ga mutum mota ta yi masa gunduwa-gunduwa, tamkar an yaka dabba, abin babu kyan gani, mata kuwa duk wadda ta kalla sau daya ba ta iya sake kallo, saboda lamarin babu dadin gani .
Ya yaba wa hukumar gudanarwa ta asibitin Jama’are saboda irin gudunmawar da ta bayar wajen yi wa gawarwakin dinkin ta hada su suka koma matsayinsu na hadaddiyar gawa kafin a yi musu wanka a adana su zuwa safiyar asabar, inda da gari ya waye aka yi musu sallah a babban asibitin na Jama’are. Sai dai shi direban ne aka yi masa sallah shi kadai a gida.
Shi ma da yake tofa albarkacin bakinsa, uban angon Malam Shehu Mai unguwar Agayari da ke garin na Jama’are ya ce samun labarin rasuwar amaryar da kawayanta ba karamin tada musu hankali ya yi ba.
Ya ce da suka taso daga Abuja motoci uku ne, motar amarya da ta ango daban, sai kuma motar abokan ango. Motar ango da ta abokansa ita ce a kan gaba, sai motar amaryar tana biye a bayansu, amma kowace tsakaninsu akwai rata, saboda ratar da ke tsakaninsu ne ma ya sa su angwayen ba su samu labarin hadarin ba sai da suka iso Kiyawa aka yi waya aka sanar da su cewa amarya da ‘yan rakiyarsu sun yi hadari gaba dayansu sun rasu, kuma ‘yansanda ne suka yi amfani da daya daga cikin wayoyin masu yi wa amarya rakiyar suka sanar da iyayen amaryar halin da ake ciki.
Ya ce, mutuwar amaren ya tada musu hankali, domin gaba daya dangin amarya na ango da ma sauran mutanen garin Jama’are ba su yi barci ba saboda halin damuwa da suka samu kansu a ciki. Ya ci gaba da cewa, marigayi Aisha mutumiyar kirki ce, mai ganin darajar mutane, tana girmamaJama’a, yaro da babba kowa tana ba shi girmansa gwargwadan hali.
Shi ma angon amaryar, wanda shi Allah Ya barshi da ransa, domin hadarin bai rutsa da shi ba, kasancewar motarsa daban, watau Malam Shamsudeen, mai kimanin shekaru 26, ya ce shi kam bai taba ganin tashin hankali irin wannan ba, duk dacewar shi yaro ne karami, yanzu ne ya fara rayuwa ta zama mutun cikakke.
Ya ce, marigayiya Aisha wadda shekarunta ba su wuce 25 ba, mace ce mai tarbiyya, wadda saninsa da ita a kallah ya kai shekaru 3, kuma bai taba jin wani ya fadi wani abu marar kyau a kanta ba balantana a yi wata magana ta baci a kanta, ‘’Aisha ta samu shaida mai kyau, sai dai Allah Ya yi mata rahama.’’
Shamsun ya ce, ya hadu da Aisha ce a lokacin yana bakin aikinsa a wani babban kanti na alfarma (Super market) da ke Garki a Abuja, ita kuma tana zaune ne a Madallah da ke kusa da birnin Abuja, saboda mahaifiyar Aisha ‘yar Jama’are ce kuma dama sun san juna, daga nan ne soyayya ta shiga tsakaninsu.
Shi ma da yake tofa nasa albarkacin bakin, Auwalu Sa’adu, wanda yayan angon ne, ya nuna damuwarsa matuka game da faruwar lamarin, duk da cewa haka Allah Ya riga Ya tsara cewa mota ita ce za ta zama sanadin mutuwar amaren, amma abu ne da wanda duk ya taso a yankin na Jama’are bai taba ganin irinsa ba, domin mutuwa ce da ta girgiza zukatan mutane.
Ya ce, musamman ma su da suke cikin tawagar dauko amaryar daga Abuja zuwa Jama’are, kasancewarsa dan uwa kuma babban yaya, a lokacin da suka dauko amaryar ma har sai da aka yi doguwar muhawara na cewa sai an sauya wa amaryar mota, amma dai daga bisani aka amince a bar amaren su hau motar dan almajiri, ‘’ashe kwanansu ne ya kare al okaci guda, bakin iyakar rayuwarsu ke nan, da fatan Allah Ya jikansu.’’
Wadanda hadarin ya rutsa da su sune: ita kanta amarya Aisha Adamu, sai kanwarta Zainab Adamu dakuma kanwar mahaifiyarta Fatima Umar da kuma wata karamar kanwarta Fatima Adamu, sai kuma babbar kawarta Sa’adiya Adamu da Safiya Adamu da kuma Munubiya, sai kuma direban da yake tare da amaren Malam Musa Almajiri.