‘Yadda muka rayu da Shekau a dajin Sambisa’
Fatima Muhammad Mai’alewa, budurwa ce ’yar shekara 18 da ’yan Boko Haram suka kama a wata kasuwar da ke cikin garin Maiduguri suka tafi da ita dajin Sambisa. A tattaunawarta da Aminiya, bayan ta kubuta ta bayyana yadda suka rayu da Shugaban Boko Haram Abubakar Shekau. Kuma ta ce ‘yan matan Chibok suna nan raye […]

Fatima Muhammad Mai’alewa, budurwa ce ’yar shekara 18 da ’yan Boko Haram suka kama a wata kasuwar da ke cikin garin Maiduguri suka tafi da ita dajin Sambisa. A tattaunawarta da Aminiya, bayan ta kubuta ta bayyana yadda suka rayu da Shugaban Boko Haram Abubakar Shekau. Kuma ta ce ‘yan matan Chibok suna nan raye a dajin:
Yaya aka yi kika zo garin Buni Yadi?
Allah Ya kubutar da ni daga hannun ’yan Boko Haram ne. Ina zaune a cikin dajin Sambisa sai wani Kwamandan Boko Haram dan Damaturu da ya dauko ni daga Sambisa ya ce zan zauna wurinsa, bayan kwanaki kadan sai na ce bari in kwatanta guduwa. Allah da ikonSa tunda na fara tafiya ban ga kowa ba har na iso Yadi. Kwanana hudu ina tafiya cikin daji kafin in iso.
Ke ’yar asalin ina ne?
Ni ’yar asalin Jihar Yobe ce, amma in zaune a Unguwar Hausari, cikin birnin Maiduguri ne.
Yaya aka yi kika shiga hannun ’yan Boko Haram?
Wata rana ne mun je kasuwa, sai ’yan Boko Haram suka shigo cikin kasuwar suna ta harbe- harbe, suka tattara mata wuri guda suka tafi da mu, sai da muka yi tafiyar fiye da awa biyu kafin muka shiga Sambisa, daga nan kuma muka ci gaba da tafiya cikin daji har muka je cikin Farisu.
Ina ne Farisu?
Farisu wani babban wuri ne kamar gari a tsakiyar dajin Sambisa, inda Imam Shekau yake zaune. A nan suka ajiye mu kusa da Imam Shekau.
A lokacin kuna ganinsa?
kwarai kuwa, wata rana ma har ya tara mu ya yi mana wa’azi da nasiha.
To wane irin wa’azi ko nasiha yake yi muku?
Yana gaya mana cewa mu kwantar da hankalinmu, babu abin da zai same mu. Mu kuma manta da iyayenmu saboda arna ne su, sun zabi rayuwar arnanci a cikin gari. Yana cewa duk wanda ya nuna cewa iyayensa ba arna ba ne to shi ma ya kafirta. Haka yake gaya mana kullum.
To yaya kuke yi da matsalar abinci a cikin dajin?
Babu wata matsala, muna samun abinci sosai, kullum ana ba mu abinci muna ci mu koshi, kuma babu wata fargaba.
Wani irin abinci ake ba ku?
Shinkafa da taliya da nama da sauransu. Babu ranar da muka taba zama da yunwa.
To a ina suke samun abincin da ake dafa muku?
Akwai kasuwa babba a cikin Sambisa, kuma babu abin da za ka nema ba ka samu ba. Abin da ya fi ba ni mamaki shi ne, yawancin masu sayar da abubuwa a kasuwar Larabawa ne, ba bakar fata ba. Kuma tare da su muke kasuwancin saboda su suke sayo kayan su sayar.
To, da wane irin yare kuke yin cinikkayya?
Ba sa jin Hausa, Larabci kawai suke yi. Sai dai idan mutum ba ya ji a fassara masa.
A lokacin da suka kama ku ku ’yan mata nawa ne a ciki?
Muna da yawa, amma da muka je sun yi mana aure. Bayan kamar misalin wata biyar sai mijina ya fita yaki aka kashe shi a can, daga nan ban sake yin aure ba.
A lokacin da kuke can sojoji sun taba kai farmaki?
Tabbas sun kai, amma idan jirgin sama ne, to ba mu cika jin tsoro ba. Amma da an ce sojin kasa ne, to kowa a tsorace yake. Za ka ga ana yin hijira daga wannan wuri zuwa wancan. Kullum kayanmu a daure suke. Idan abin ya lafa sai mu koma cikin Farisu.
To a lokacin guje-gujen ina Shekau yake?
Shekau, yana Farisu, sai dai wani lokaci su fita cikin motoci kirar Hilud da yawa amma su dawo.
Ana cewa Shekau ya mutu ko da gaske ne?
Wallahi bai mutu ba, yana nan da ransa, lafiyarsa kalau kuma muna ganinsa. Sai dai in bayan da na fito ne a kashe shi. Na fito ne lokacin Sallar Layya da ta wuce.
To yaya labarin ’yan matan Chibok?
’Yan matan Chibok suna nan.
Kin san inda aka ajiye su?
Suna cikin Farisu, akwai manyan gidaje da aka ajiye su a ciki, ina ganinsu wasu lokuta.
Amma a cikin wane yanayi suke?
Suna cikin koshin lafiya, ba su rasa ci ko sha ba. Irin kayan da muke sawa su suke sakawa. Sai dai daga cikinsu akwai wadanda Shekau ya yi wa da’awa ba su karba ba, sai ya mayar da su bayi ya sayar da su. Daga cikinsu kuma akwai wadanda suka karbi da’awa amma suka yi kunar bakin wake, wadansu kuma sun yi aure. Akwai masu ’ya’ya a cikinsu yanzu. Akwai wani Kwamadan Boko Haram dan asalin Buni Yadi da ake kira Usaini Afuwa ya sayi ’yan matan Chibok uku a matsayin kwarkwara.
Akwai wani hari da jirgin sama ya kai Sambisa, kina can?
Zahiri ina can jirgin sama ya zo ya jefa bama-bamai a cikin masallaci, wajen mutum 400 aka ce sun rasa rayukansu sakamakon harin, amma bai shafi inda ’yan matan Chibok suke ba.
Kina da tabbacin bai shafi ’yan matan Chibok ba?
Ni dai a sanina bai shafe su ba, saboda a masallaci aka jefa bam din. Har na baro Sambisa ’yan matan suna nan babu abin da ya same su.
Akwai maganar fada a tsakanin magoya bayan Shekau da na Mamman Nur, ko kin gane wa idonki wannan arangama?
Gaskiya har na baro Sambisa ba a fara yakin ba, amma dai akwai kishin- kishin cewa rashin jituwarsu ya yi kamari, bayan na zo dajin Talala ne suka fara fada. Wanda hakan ya sa mutane da dama sun tarwatse saboda Shekau ya rika kashe mutane ba gaira ba dalili. Daga baya an ce Shekau ya rika yanka malamai da suka yi wa Mamman Nur mubaya’a. Abin da ya fi ba ni tsoro shi ne, yanka mutane da a ka rika yi a kan idonmu, wani lokaci kwai sai su kama mutum su yanka a gaban mutane. Su dauki kansa su dora a gadon bayansa, sa’annan su ci gaba da yin kabbara. Har yanzu idan na rufe idanuna wata sa’a nakan firgita.
Me mutanen ke yi a yanka su?
Ba su fadin laifi, sai dai kawai mu ga an jera su ana ta yankawa.
Sai kuma me ya kara ba ki tsoro?
Suna jefe duk wanda aka kama da laifin yin zina. Idan mutum ya yi sata a yanke masa hannu. Wanda kuma bai taba aure ba a yi masa bulala.
To wane abu ya burge ki lokacin da kike tare da su?
Babu abin da ya burge ni sai fargaba da tashin hankali.