Yadda muka samar da aiki ga matasa dubu 10 – Shugaban gonar Labana

Aminiya: A matsayinka na fitaccen manomin shinkafa da kuma sarrafa ta da sauran kayan amfanin gona. Ya ya ka dauki wannan harka ta noma? Aleiro: Babu shakka ina matukar yin godiya ga Allah da Ya ba ni damar bude wannan katafaren gona mai suna Gonar Labana, (Labana Farms) sannan ina mai sanar da cewar noma […]

Yadda muka samar da aiki ga matasa dubu 10 – Shugaban gonar Labana

Aminiya: A matsayinka na fitaccen manomin shinkafa da kuma sarrafa ta da sauran kayan amfanin gona. Ya ya ka dauki wannan harka ta noma?

Aleiro: Babu shakka ina matukar yin godiya ga Allah da Ya ba ni damar bude wannan katafaren gona mai suna Gonar Labana, (Labana Farms) sannan ina mai sanar da cewar noma ya na bude hanyoyi ma su yawa na dogoro da kai ga al’uma ma su yawan gaske. 

Aminiya: Jihar Kebbi ta na takama da noma, musamman noman shinkafa da alkama da albasa ta fuskar tatalin arziki, wace hanya ka ke ganin za a bi wajen kara inganta harkar noma a jihar?

Aliero: Ya kamata mu kalli ayyukan da gwamnan Jihar Kebbi ke yi tukun, babu abin da ya sa gaba sai harkar noma, kowa ya sani a kasar nan Kebbi ce jagorar noman shinkafar rani, wanda mai girma shugaban kasa ya zo ya kaddamar, ya kuma kaddamar da bude kamfanin sarrafa shinkafa na Labana wanda ake kira (Labana Rice Mills) wadda Ministan Gona, Cif Audu Obeh ya wakilce shi.

Bayan ya kaddamar da noman ranin anan Jihar Kebbi daga bisani wadansu jihohi suka biyo bayanta. Shi kansa shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya kaddamar da shirin ya san cewa al’umar Kebbi da gwamnatin Kebbi ba za su ba shi kunya akan noman rani ta kowace fanni ba, baya ga wadannan manya-manya injinan dake jawo ruwan, mun jawo su ne daga kogin Neja watau (Riber Niger) zuwa nan cikin gona, kuma daga nan zuwa kogin Neja ya kai tsawon kilomita 45 ko 50, amma ka ga yadda ruwa ke zuwa da karfi. Muna kuma da kananan injinan bada ruwa har guda 200. Amfanin kananan injinan shi ne, inda ruwa baya kaiwa saboda tudu, sai mu jona da karami ya tura ruwan zuwa sama ta yadda ko’ina zai samu. 

Aminiya: Baya ga wannan gona ta Labana, ko akwai wata gonar da kake da ita?

Aliero: Kafin wannan babbar gona, dama mu na da wata gona mai suna (Lanaba Global Farms) ita wannan gona, karama ce ba ta kai girman wannan ba. Gidan gonar muna kiwon kifi da kaji da kuma ruwan roba, watau (Labana Water) kuma da yardar Allah kwanan nan zamu bude wurin yin fulawa. Wannan mu na yi ne domin matasanmu su sami aikin yi dan dogaro da kansu. 

Aminiya: Rashin ayyukan yi ke tilasta wa matasa fantsama birane don yin rani, shin kana ganin idan aka koma wa noma za a iya magance haka? 

Aliero: kwarai da gaske, domin ka ga tafiye-tafiyen nan da yaran nan ke yi, banda wahala babu abin da suke jawowa kansu da kuma yankunanmu. Su na zuwa su yi ta wahala, su ne haya da babur, yankan akaifa, leburanci, tura baro, wasu ma wanke-wanken kwanonin masu sayar da abinci. Domin muna da hekta dubu 500 na noman rani, wanda ya tashi daga karamar hukumar Argungu zuwa karamar hukumar Ngaski, kimanin kilo-mita 350, domin nan ne Mai Girma Shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya kaddamar da aikin noman rani, inda Gwamnatin Jihar Kebbi ta fito da tsari, komai zai tafi daidai. Yanzu noma ya wuce ka duka da kanka da fartanya, akwai fannonin noma daban-daban. Ka ga akwai noman kamar yadda masana aikin gona suke fada, idan aka yi wa matasanmu tsari mai kyau, na san za su yi noma kuma za a ga alheri sosai, ganin cewa babu abin da hannu ke yi a cikin wannan gona sai dai na’urorin dubarun noma.

Musamman kamar yadda gwamanan Jihar Kebbi, Sanata Abubakar Atiku Bagudu ya ke ta kira akan aikin noman rani na cewa za a tallafa wa manoma da iri da taki da maganin feshi da injinan bada ruwa da kuma kudi da kasuwar abin da suke noma da sauransu.

Aminiya: Wane kira za ka yi ga gwamnati domin kara himma kan noma kamar yadda ta kudarta? 

Aliero: Lallai idan aka dauki fannin noma za a iya farfado da tatalin arzikin kasa, a samar da aikin yi ga matasa, kasa ta zauna lafiya, saboda zaman lafiya kasar shi ne ace kowa yana da abin yi. Kuma yana da abin da zai ci, ga mu da yawan al’umma, ga kasar noma amma an bar matasa maza da mata da yawa babu sana’a babu aikin yi, idan har gwamnati ta rungumi noman nan, kamar yadda ta taso a harkar noma yanzu, Allah Ya taimake mu abin ya dore, to mutanenmu za su samu kwanciyar hankali, da ci gaba, misali, yanzu ka dubi fuskokin ma’akatan dake aiki a gonar nan ta Labana kowa yana cikin farin ciki kamar ba aiki suke yi ba saboda sun sami abin yi. 

Aminiya: A karshe mutane nawa ke aiki a gonar Labana da gidan gonar Labana da kamfanin sarrafa shinkafa na Labana?

Aliero: A wuraren nan guda uku da ka lissafa a kalla sama da mutane dubu 10 daga cikinsu za a sami sama da mutane dubu shida (6,000) wadanda muke biyan albashi duk wata, sauran muna biyansu a kullum iya aikin da mutun ya yi na yini.