‘Yadda muka sha da kyar daga gobarar iskar gas a Lafiya’
Wata mummunar gobarar iskar gas da ta auku a gidan mai na Monaco Oil and Gas da ke Lafiya a Jihar Nasarawa a ranar Litinin da ta gabata ta hallaka mutum tara yayin da mutum 37 suka samu munanan raunuka. Kwamandan Hukumar Kashe Gobara ta Jihar, Alhaji dalhatu Mohammed ya ce da misalin karfe 8 […]

Wata mummunar gobarar iskar gas da ta auku a gidan mai na Monaco Oil and Gas da ke Lafiya a Jihar Nasarawa a ranar Litinin da ta gabata ta hallaka mutum tara yayin da mutum 37 suka samu munanan raunuka.
Kwamandan Hukumar Kashe Gobara ta Jihar, Alhaji dalhatu Mohammed ya ce da misalin karfe 8 na safiyar Litinin ce aka buga wa hukumarsa waya kan tashin gobarar inda nan take ya turo jam’ansa da motocin kashe gobara. Ya ce sai dai kafin su isa wurin gobarar ta riga ta yi mummunan barna saboda gobarar ta iskar gas ce. Ya ce jami’ansa sun yi kokari tare da hadin kan sauran hukumomin agaji suka kashe gobarar da kuma agaza wa wadanda lamarin ya rutsa da su.
Kwamandan ya ce hukumar ta kwashe wadanda suka rasu da wadanda suka samu raunuka zuwa Asibitin kwararru na dalhatu Araf da ke Lafiya.
Ya ce gobarar ita ce mafi muni da ta auku a jihar a bana, inda ya ce bayan aukuwar gobarar hukumar ta gudanar da bincike kan musabbabin aukuwar gobarar inda ta gano cewa gobarar ta tashi ne lokacin da ake sauke tukwanen gas daga wata tirela, kuma daya daga cikin tukwanen ta rika yoyo.
Kwamandan ya ce daga bisani wuta ta tashi ta bi ta iska tana ta kone motoci da baburan da ke wucewa ta kan babbar hanyar Abuja zuwa Makurdi da gidan man ke kanta.
John Anthony, daya daga cikin wadanda suka tsira da kyar daga gobarar ya shaida wa Aminiya cewa: “Ina daya daga cikin wadanda suka tsira suka kuma yi babbar asarar dukiyoyi na miliyoyin Naira a wannan bala’in gobara da ya auku. Abin da ya faru shi ne a lokacin da ma’aikatan gidan man suke sauke tukwanen gas din daga wata tirela da ta zo da su ne sai daya daga cikin tukwanen ta fashe inda gas din ya rika tsiyaya. Kasancewar ma’aikatan sun san illar haka sai suka yi ta gudu suna sanar da jama’a musamman mu da ke kusa da wadanda suke bin babbar hanyar da ta bi ta gaban gidan man cewa mu gudu. Bayan mun gudu sai kawai muka ga wani hayaki ya tashi daga wajen ya mamaye wurin baki daya. Ana wannan hali ne muka ga jami’an kashe gobara sun iso suna korar jama’a suna kokarin kashe gobarar.”
Ya kara da cewa: “Ana cikin haka ne kawai sai muka ga wuta ta tashi. Daga gidan man ta rika bin ta iska tana kama shagunanmu da motoci da babura da Keke-NAPEP da suke bin hanyar. Muna ji muna gani dukiyoyinmu suka kone kurmus babu abin da muka iya. Na yi asarar motocin da nake sayarwa sababbi kirar Sharon guda 3 da Golf guda 3 da injin facin taya na zamani da sababbin tayu da nake sayarwa da na mutane da suka kawo faci wurina da sauransu. Mun gode Allah da Ya taimaka mana muka tsira daga gobarar, amma gaskiya kusan na rasa komai na rayuwa.”
Sai ya roki gwamnatin jihar da ta tarayya da sauran jama’a su taimaka musu don ba su damar farfadowa daga asarar da suka yi.
Ita Esther Sule Attah, wadda ke sayar da takalma da kayan sawa da takardu a kusa da gidan man, ta ce ta fito shagonta da safe kamar yadda ta saba sai kawai ta ga daya daga cikin ma’aikatan gidan man a guje yana ce mata maza ta tattara abin da za ta iya ta bar kwantenanta ta gudu. “Rufe bakinsa ke da wuya sai kawai na ga hayaki mai duhu da ban taba ga irinsa ba ya mamaye sararin sama. Daga nan na fito a guje don tsira da raina. Bayan na yi nisa da wurin ba sai na ji karar fashewar wani abu kamar bam inda daga nan wuta ta kone kayayyakinmu,” inji ta.
Ta ce, ta yi asarar daukacin kayayyakin da ke cikin shagonta da suka kai kimanin Naira miliyan daya da rabi, sai ta roki gwamnati da masu hali su taimaka musu da jari don su ci gaba da harkokinsu. “Kuma ina so gwamnati ta dauki matakan kare sake aukuwar irin wannan gobara a nan gaba,” inji ta.
Shi kuwa Musa Nasiru cewa ya yi “Na yi asara sosai amma ina godiya ga Allah da Ya kiyaye ni Ya sa ban rasu ko na samu rauni a gobarar ba. Ina sayar da man fetur ne a kasuwar bayan fage a kusa da gidan man sai na ga wani ma’aikacin gidan man a guje ya gaya cewa in yi maza in bar inda nake akwai matsala. Kafin in dauki jarkar man fetur dina da ta rage, sai na ga wani makwabcina ya riga ni daukar jarkar, sai na bi shi. Muna cikin gudu ne sai na ji karar fashewar gas din inda wuta ta biyo karar. Nan take na ga ko’ina ya kama da wuta, wadanda ba su san abin da ke faruwa ba suna tafiya a babbar hanyar da ta bi ta gidan mai sai wutar ta kama su suna cikin motoci da masu tafiya a kasa. Ni dai a safiyar wadanda na ga sun fadi wutar na cin su suna ihu, kuma suka mutu daga bisani sun kai mutum 7. Kuma jama’a da dama sun kuna kafin jami’an kashe gobara da na kare haddura da sauransu su kwashe su zuwa asibiti.”
Gwamnan Jihar Umaru Tanko Al-Makura ya ziyarci wadanda lamarin ya shafa a Asibitin dalhatu Araf da ke Lafiya, inda ya jajanta musu. Gwamnan ya bukaci su dauki lamarin a matsayin kaddara daga Ubangiji. Ya yi fatar Allah Ya bai wa iyalan wadanda suka rasu karfin halin jure babban rashin da suka yi, inda ya ce gwamnatinsa za ta yi duk mai yiwuwa wajen tabbatar da wadanda ke kwance a asibitin sun samu kyakkyawar kula.
Gwamna Al-Makura ya ce tuni gwamnatinsa ta tura wadanda rauninsu ya yi muni zuwa Asibitin kasa da ke Abuja don su samu kyakkyawar kula. Ya ce gwamnatinsa ta kafa kwamitin da zai rika sa ido ga harkokin gidajen man da ake ginawa ba bisa ka’ida ba a tsakiyar al’umma.
Gwamnan ya bukaci al’ummar jihar su yi watsi da karin gishiri da wasu gidajen rediyo da jaridu ke yi kan adadin wadanda suka rasu, inda ya ce mutanen da aka tabbatar da rasuwarsu su ne mutum 9, yayin da mutum 26 suke kwance a asibiti a Lafiya, sai mutum 7 da gwamnatinsa ta tura Abuja.
Shugaban Majalisar Dattawa Sanata Bukola Saraki me ya ziyarci wadanda gobarar ta shafa bayan ya gana da magoya bayan Jam’iyyar PDP a Sakatariyar Jam’iyyar da ke Lafiya.
Da yake jawabi a asibitin Sanata Saraki ya bayyana lamarin da kaddara daga Ubangiji inda ya bukaci iyalan wadanda lamarin ya shafa su yi imani cewa Allah ne Ya kaddara aukuwar haka. Ya yi addu’ar Allah Ya jikan wadanda suka rasu tare da jinjina wa kokarin jami’an kashe gobara da ’yan agajin Red-Cross da sauransu da suka isa inda lamarin ya auku cikin lokaci suka kashe gobarar suka kuma kai wa wadanda lamarin ya shafa dauki.