‘Yadda muka shafe wata 2 a hannun ’yan bindiga muna cin garin rogo da gishiri’
Allah ne kaɗai Ya yi za mu fita da ransu amma har mun sadakar cewa ba za mu fito da rai ba.
Muhammad Haruna da Khalid, matasa ne biyu da suka baro garinsu ƙauyen Narabi da ke Ƙaramar Hukumar Toro a Jihar Bauchi zuwa garin Kachiya da ke Kudancin Jihar Kaduna don neman na rufin asiri saboda halin da ake ciki na matsin rayuwa a ƙasar nan.
Sai dai sun yi rashin sa’a inda suka faɗa a hannun ’yan bindiga masu garkuwa da mutane don karɓar kuɗin fansa kuma suka shafe kimanin wata biyu a hannunsu kafin su sako su.
- Satar allon kabari ya kai matsahi kurkuku a Kano
- Satar N660m: An tsare shugabannin ƙananan hukumomin Kano 3
Muhammad ya shaida wa wakilinmu a garin Kafanchan a kan hanyarsu ta komawa gida Bauchi bayan sun samu sun kuɓuta daga hannun ’yan bindigar sakamakon biyan kuɗin fansa na kusan Naira miliyan ɗaya, inda ya bayyana cewa sun sha wahalar gaske a hannun ’yan bindigar.
Sun bayyana irin wahalar da suka sha da irin mutanen da suka gani waɗanda suka ce suna da yawa.
“A tsawon kwanakin da muka shafe a hannunsu ba sa ba mu komai sai dai su yayyafa wa garin rogo ruwa su zuba gishiri su ba mu safe da yamma, a haka muka rayu,” in ji Muhammad.
Ya ce rana da iska da ruwan sama duk a kansu suke ƙarewa, “In da ruwan sama ya jiƙa mu a nan za mu ci gaba da zama hannuwa da ƙafafunmu a ɗaure har jikinmu ya bushe ba damar zuwa ko nan da can,” in ji shi.
Ya ce in aka ga an kwance musu mari da sarƙar da ake ɗaure su da su, to za su je ɗibo ruwa ne ko yi wa ’yan bindigar wankin sutura da wanke musu babura ko kuma za su jefar da gawar wanda aka kashe ko ya mutu a hannunsu.
Khalid da Muhammad sun bayyana cewa Allah ne kaɗai Ya yi za su fita da ransu amma su har sun sadakar cewa ba za su fito da rai ba.
“Sai dai duk da tsananin azabar da muke sha ga rashin barci amma suna kula da mutum idan ya samu rashin lafiya tunda har allura ma suna mana,” in ji Khalid.
Ya ce ’yan bindigar da suke kula da su waɗanda ba su ke nan ba, sun kai kimanin hamsin a dajin kuma suna ɗauke ne da sababbin bindigogi ƙirar AK-47.
Sannan sun ce babu irin mutanen da ba su gani ba a cikin waɗanda aka kama daga kan matasa da mata har zuwa kan tsofaffi.
“Ana gobe za mu fito daga dajin sai da suka kamo ’yan mata guda biyar daga yankin Kachiya suka kawo su inda suke tara mutane.
“Zuwanmu wajen mun tarar da mutanen da aka kama kusan 30,” in ji shi.
Kan yadda aka yi suka shiga hannun ’yan bindigar, ya ce “Wata rana muna kwance a ɗaki da daddare bayan mun dawo daga aiki a inda muke aikin ma’adani a yankin Kachiya sai muka ji ana ƙwanƙwasa mana ƙofa, bayan sun shigo sai suka fara haska mana tocila suka karɓe mana kuɗaɗe da wayoyinmu daga nan suka fito da mu suka tafi da mu cikin daji.”
Muhammad ya ce bayan an yi tafiya mai nisa da su zuwa wani daji sai suka ce musu duk wanda yake da wata lamba na wanda za a kira don kawo kuɗin fansa, to ya kira.
“Mun kasance mu uku ne a ɗakin da suka tafi da mu amma mu biyu muka dawo don bayan cikarmu kwana ashirin a hannunsu sun kashe abokinmu mai suna Hamza Ibrahim a kan idonmu a cikin dajin. Sun saba a wasu lokuta idan sun kamo dangin masu kuɗi suna so su karɓi kuɗi mai yawa a hannunsu sukan kashe wani da suke ganin ba za a samu wasu kuɗaɗe masu yawa a wurin danginsa ba, don su ba waɗancan tsoro,” in ji shi.
Ya ce, “Wata rana bayan sun yi wa wani babban mutum dukan kawo wuƙa wanda ya mutu a gabanmu sai suka umarce mu, mu shida mu kai gawar mu jefar a wani rami kusa da bakin rafi.
“Ni da ɗan uwanmu da aka kashe muka ɗauki gawar suka raka mu.
“Bayan mun jefa shi a rami mun fito sai suka ce ni in hauro shi kuma ɗan uwan nawa suka ce masa ya koma ramin ya tura gawar mutumin ciki da kyau.
“Bayan ya je ya tura yana ɗagowa sai wani daga cikinsu ya buɗe masa wuta ya zuba masa harsashi uku muna kallo, yadda suka kashe mana ɗan uwa ke nan,” in ji shi.
Sun ce ba su san ko nawa aka biya su ba don da farko an ba su Naira dubu 500 sai suka ce ta yi kaɗan, don ba a garkuwa da mutane a Naira dubu 500 a yanzu, inda suka buƙaci ƙari amma ba su bayyana nawa aka ƙara musu ba.
“Mun kwashe kusan wata biyu a hannunsu cikin uƙuba da wahala ga jikinmu duk ciwo kafin wata rana su fito da mu su nuna mana wata hanya wadda muka shafe kwana biyu muna tafiya a cikin daji babu gida gaba, ba gida baya kuma ba mu haɗu da kowa ba har muka fito wani gari da ke kan hanyar Kaduna zuwa Abuja da ake kira Akilbu kusa da garin Katari da ke Ƙaramar Hukumar Kagarko,” in ji Muhammad.
Ya ce daga nan ne suka fara neman taimako har suka zo Kafanchan suna ta waya da ’yan uwansu kafin wani ɗan uwansu ya shaida masa cewa yana da aboki a garin Kafanchan inda ya kira shi ya haɗa su da shi suka kwana kafin su wuce.
“Babban abin da ya fi ba mu tsoro shi ne yadda suke kiranmu gaba ɗaya su tara mu sai su zaɓi wani a cikinmu su kashe.
“Zuwanmu wajen sun kashe mutum uku a kan idonmu kuma mun tarar da gawarwakin mutum 11,” in ji shi.