Yadda muka shiga tasku a Afirka ta Kudu – ’Yan Najeriya
A daren Larabar makon jiya ne jirgin Air Peace ya fara jigilar ’yan Najeriya 187 da suka zabi komowa gida daga kasar Afirka ta Kudu. Mutum 187 din sun hada da maza da mata da yara sun samu kyakkyawan tarba daga Mai Taimaka wa Shugaban Kasa kan Al’amuran ’yan Najeriya da ke Kasashen Waje Misis Abike […]
A daren Larabar makon jiya ne jirgin Air Peace ya fara jigilar ’yan Najeriya 187 da suka zabi komowa gida daga kasar Afirka ta Kudu.
Mutum 187 din sun hada da maza da mata da yara sun samu kyakkyawan tarba daga Mai Taimaka wa Shugaban Kasa kan Al’amuran ’yan Najeriya da ke Kasashen Waje Misis Abike Dabiri-Erewa da jami’an Hukumar Agajin Gaggawa ta Kasa (NEMA) da jami’an Hukumar Shigi da Fici ta Kasa.
’Yan Najeriyar sun iso filin jiragen sama na Murtala Mohammed da ke Legas cike da farin ciki da annashuwa inda suka yi ta rera takenNajeriya tare da bayyana takaicinsu kan halin kuncin da suka samu kansu a kasar Afrika ta Kudu.
Aminiya ta zanta da wadansu daga cikinsu inda wadansunsu suka bayyana yadda suka bar tarin dukiyoyi da kadarorinsu a Afirka ta Kudu yayin da wadansu suka ce, sun bar iyalansu a can. Mista Codobasi dan asalin Jihar Abiya daya ne daga cikin wadanda suka dawo ya shaida wa Aminiya cewa, ya yi matukar farin ciki ganinsa a Najeriya. Ya ce, zuwa yanzu akwai dimbin ’yan Najeriya da suka makale a Afirka ta Kudu, kuma akwai wadanda ba sa so su dawo ko ta halin kaka bisa dalilan da su kadai suka sani.
“Ni karatu ya kai ni Afirka ta Kudu inda na shafe sama da shekara bakwai, kuma ni malamin coci ne. Na yi farin cikin dawowa ta domin na shiga garari, na je kasar Afirka ta Kudu ne domin in wuce kasashen Turai daga can, amma sai na fada tarkon ’yan damfara baya ga masifar nuna wa baki bakaken fata kiyayya. Allah Ya saka wa wadanda suka yi ruwa-da-tsaki wajen dawowarmu,” in ji shi.
Ita kuwa Temilabi, wacce ta dawo dauke da ’yarta, ta shaida wa Aminiya cewa, ta tafi Afirka ta Kudu ce bidar aiki lokacin da ta kammala karatunta a Jami’ar Jihar Legas. Ta ce idan gwamnati ta sama wa matasa ayyukan yi za a samu saukin fitar ’yan kasar nan zuwa kasashen ketare neman aiki.
Haka zalika wata budurwa da ta dawo daga Afirka ta Kudu a cikin mutum 187 ta shaida wa Aminiya cewa, a halin da suka bar kasar ’yan Najeriya ba su da matsuguni ko maboya, ta ce tun daga abin da ya shafi babban birnin kasar Johanisburg da sauran sassan kasar, ana bin ’yan Najeriya ana kashe su tamkar tumaki ana kuma wawason dukiyarsu, ta ce su ma sun tsallake rijiya da baya ne.
Wani dan asalin Jihar Ondo mai suna Segun Salau da ya kai shekara biyar a Afirka ta Kudu, ya bayyana wa Aminiya cewa a lokacin zamansa a Afirka ta Kudu ya kasance cikin fargaba saboda harin da ake kai wa baki a kasar. Ya ce a wani harin da aka kai wa ’yan Najeriya an shiga shagon ’yar uwarsa inda aka yi mata asarar dimbin dukiya. Ya ce ba ya da dalilin komawa Afirka ta Kudu nan gaba saboda sau uku yana ganin abin da ake yi wa baki a kasar.
’Yan Najeriyar sun shaida wa ’yan jarida cewa da yawansu sun sauka Najeriya babu komai tare da su, inda suka ce akwai da dama daga cikinsu da suka bar dimbin dukiyoyinsu a can suka komo ba ko kwabo. Kuma ya ce akwai ’yan Najeriyar da ba za su dawo ba saboda ba za su iya barin abubuwan da suka mallaka ba.
Shi ma Ali Sa’id Samuel, cewa ya yi da kyar ya sha a Afirka ta Kudu ya ce kiris ya rage da an kashe shi. “Ana tauye hakkin ’yan Najeriya, a baya-bayan nan wata shida na yi ina aiki aka hana ni kudin aikina, haka suke yi mana, suna tauye hakkinmu,” inji shi.
A daya bangaren Gwamnatin Tarayya ta sha alwashin kyautata rayuwar ’yan Najeriya da suka komo daga Afirka ta Kudu.
Idris Abubakar Muhammad babban jami’i a Hukumar NEMA wanda ya jagoranci jami’an hukumar wajen karbar mutum 187 din ya shaida wa Aminiya cewa, hukumar ta shirya tsaf domin ba su kulawa. Ya ce sun tanadi kayayyakin abinci, magunguna da sauransu.
“Bayan jami’an shigi da fici ta kasa sun tantance su kamar yadda kake gani ana yi yanzu za mu ba su wannan tallafi mu sanya su a motocin da za su karasa da su jihohinsu sannan mu ba su dan abin hasafi kafin mu mika su ga mahukunta na jihohinsu su dora a kan tallafin da Gwamnatin Tarayya ta yi musu,” inji shi.
A bangaren Malama Abike Dabiri-Erewa ta ba da tabbacin ba su kulawa ta musamman, ta ce ko wannensu za a ba shi katin waya na Naira dubu 40 da za su yi amfani da su cikin wata biyu.
“Mun ba ku wannan ne domin in kun je gidajenku kun huta ku samu hasafin kiran ’yan uwa da abokan arziki ku yi zumunci, kana akwai kamfanonin da muka gayyato wadanda za su tallafa muku ku kama sana’a ko kasuwanci,” inji ta.
Ta ce, Gwamnatin Tarayya za ta ba su dan abin hasafi domin su tada komada.
Shugaban Kamfanin Jiragen sama na Air Peace, Mista Allen Onyema ya ce, sun yi jigilar mutum 188 daga Afirka ta Kudu zuwa Najeriya a jirginsu ba tare da karbar ko kwabo ba. Ya ce sun ga ya dace su taimaka musu kuma su bada irin tasu gudunmawar a matsayinsu na ’yan kasa masu son ci gaban kasa da al’ummarta. Ya ce abin da ya burge shi shi ne yadda mutanen ke ta rera taken kasar nan lokacin da suka sauka Najeriya.
“Wannan shi zai tabbatar muku cewa, mutane ne masu son kasarmu Najeriya ba ’yan tawatse ba ne, a shirya nake mu ci gaba da kwaso su, duk wanda yake bukatar komowa mun shirya dauko su, koda mutum guda ne ya rage a shirye muke mu dauki jirgi mu je mu dauko shi, jira kawai muke mu samu izini daga Gwamnatin Tarayya,” inji shi.
Dubban ’yan uwa da abokan arziki ne suka hallara a filin jirgin domin tarbar mutanen wadanda yawancinsu suka yi zaman dirshan tun daga safiyar Laraba zuwa dare a lokacin da ’yan uwansu suka sauka a birnin Legas daga Afirka ta Kudu.
Ana sa ran jirgi na biyu ya dawo da wadansu daga Afirka ta Kudu daga yanzu zuwa kowane lokaci bayan da hukumomin Afirka ta Kudu suka amince a dauko su. A baya dai hukumomin sun hana kwaso wadansu bisa zargin suna zaune a kasar ce ba da takardun izini ba.