Yadda muka tsallake rijiya da baya a harin bam din Nyanya na biyu
Da yawa daga cikin wadanda tashin bam din Nyanya a Abuja ya rutsa da su kuma suka tsallake rijiya da baya, musamman ta fuskar rasa wasu daga cikin sassan jikinsu, sai da suka suma kafin su san abin da ya same su bayan sun farfado. Aminiya ta zaga wasu daga cikin asibitocin da aka kai […]
Da yawa daga cikin wadanda tashin bam din Nyanya a Abuja ya rutsa da su kuma suka tsallake rijiya da baya, musamman ta fuskar rasa wasu daga cikin sassan jikinsu, sai da suka suma kafin su san abin da ya same su bayan sun farfado. Aminiya ta zaga wasu daga cikin asibitocin da aka kai wadanda suka raunata kuma ta ji ta bakin wasunsu, kamar haka:
Abdurrahman Adamu
A asibitin Maitama, wakilinmu ya tattauna da wani mai suna Abdurrahman Adamu, wanda dan asalin karamar Hukumar Doguwa ne da ke Jihar Kano, amma yake sana’ar achaba a unguwar Sabon Gari da ke Mararraba, inda ya bayyana yadda tashi ta same shi.
Ya ce yana daf da hawa kan gadar sama da ke kusa da inda nakiyar ta tashi, wani ya tsaida shi don ya dauke shi zuwa wani waje. “Mutumin ya mika min kayansa, sannan yana shirin hawa babur, sai kawai na ji karar fashewar bam. Ana cikin haka, sai kawai na ji wani abu ya sare ni a jiki, na saki mashin na fadi a kasa somamme. Bayan na farfado na nemi taimakon wani da na gani kusa da ni, amma ganin yadda na ji rauni sai ya guje ni, amma daga baya wasu suka tallafa min aka kai ni asibitin Asokoro. Kasancewar gadajen asibitin sun cika da jama’a, sai aka kawo ni nan”.
Theresa Sabo
Ita kuwa Theresa Sabo, wadda ’yar asalin Jihar Nassarawa ce da ke makaranta a Kuje, Abuja, ta ce ta je wajen ne tare da wasu ’yan mata biyu da nufin shiga mota don zuwa Area One, sai dai motar da suka so shiga da farko ba za ta dauke su gaba dayansu ba. “Hakan ta sa muka yi gaba don shiga wata motar, ana cikin haka ne, sai kawai muka ji kara, nan na rabu da ganin abokan tafiyata, daga baya na rarrafa ina neman dauki. Da farko jama’a ba wanda ya kula da ni, sai bayan jimawa na samu aka dauke ni zuwa Asibitin Asokoro, kafin maido ni wannan asibitin na Maitama.
Mahaifinta Malam Sabo Galadima, wanda ke tare da mahaifiyarta, ya bayyana godiyarsu ne ga ministan Abuja da kuma uwargidansa, “Saboda ziyartarmu da suka yi a asibitin Asokoro, kuma suka tallafa mana, kafin a maido mu nan”
Salisu Yakubu
Shi ko Salisu Yakubu, wanda dan asalin kofar Durmi ne a garin Bauchi, amma yake aikin yaron mota a Nyanya zuwa garuruwan Auchi da Enugu da kuma Fatakwal, ya ce rashin fasinja ya sa suka yanke shawarar lodi daga Nyanya zuwa Area One don magance zama haka nan, “Muna cikin neman fasinja da misalin karfe 7.30 na dare a lokacin da lamarin ya faru, abin da ya afku, ya kasance, aka kawo ni nan asibitin Asokoro. Ina rokon Allah Ya kare, abun ya tsaya haka nan”.
Mista Joseph Ogbeche, wanda aka kai shi a babban asibitin Nyanya, ya shaida wa wakilinmu cewa, “A lokacin da bam din ya tashi, na yi sayayya wajen wani da muke kira Malam, na ba shi kudi yana kokarin miko min canji. Ban san lokacin da na yi tsalle na fada kusa da magudanar ruwa ba. Bayan na komo hayyacina ne sai na gan shi kwance cikin jini, matacce, kuma ga kudin a kasa, kusa da shi.
“Na ji ciwo a kaina, wanda hakan ya sanya na garzaya asibiti, jini na zuba daga kaina, aka yi mini aiki. Yanzu na samu sauki, kuma ina yi wa Allah godiya”.
Malama Hadiza Adam kuwa ta bayyana cewa ita da abokiyarta sun yi shirin shiga motar da za ta kai su Area 1 ne bam din ya tashi.
“Motar da muka gani ta farko a cike take, sai abokiyata ta ce mu matsa gaba kadan don samun wata. Mun yi gaba din ne sai ga wata farar bas babu kowa a ciki. Da ma a gabana take, kafin in karasa wurinta, sai bam din ya tashi. Rabuwarmu ke nan, don ita ta mutu nan take. Ni kuwa ashe faduwa na yi kuma na fita hayyacina na wadansu mintoci, bayan na farfado, sai na kasa tashi, daga bisani ta lura ashe ba kafata ta dama, ta gutsure”.
An bayyana cewa kafin su kai ta babban asibiti da ke Maitama, sai da ’yan sanda suka ciccire wasu karafa da gilasai daga jikinta.
Shi kuwa wani mai kwashe shara mai suna Yusuf Muhammad, wanda yake zaune a Kubwa kuma yake sana’arsa a kasuwar lemu da ke Maraba, lokacin da wakilinmu ya ziyarce shi a babban asibitin Nyanya, saboda tsananin zafin raunin da ke kafarsa ta hagu, ya zaci ko likita ne ya zo gadonsa, sai ya ce, “Wallahi wannan kafar ba ta da lafiya kuma tana min azaba sosai”. Inji shi.
Mista Joseph Ogbeche harin ya rutsa da shi ne a lokacin da yake kan hanyarsa ta zuwa wajen dan uwansa, ya fada wa wakilinmu, a babban asibitin Nyanya cewa yana jiran mota ne zuwa Wuse a lokacin da bom din ya tashi.
Bayan kwana biyu da aukuwar harin, saboda abin da ya auku, sai Joseph ba ya iya ji da kunnensa na hagu sanadiyyar fashewar bam din, kodayake likita ya ba shi tabbacin zai warware cikin dan wani lokaci.
Samamen soja ya sa Hausawa kaura daga Nyanya
A wani lamari kuma, daruruwan Hausawa, wadanda mafi yawansu ’yan cirani ne da ke kwana ko gudanar da sana’a a yankin kauyen Nyanya, sun bar Abuja babu shiri zuwa garuruwansu don gudun abin da ka iya biyo baya daga bangaren jami’an tsaro.
Mutane da dama da wakilinmu ya zanta da su sun bayyana cewa hakan ya biyo bayan wani samame da jami’an tsaro na soja suka gudanar, a ranar Asabar, jim kadan bayan sallar Asuba, inda suka rika tara mutane a waje guda, daga bisani suka shiga cikin gidaje don binciken kwakwaf.